Chapter 20

56 9 0
                                        

Suna dawowa gida Abdulrahman ya kira Abdulrahim yana dauka yace "Dan uwa ya hanya?" Abdulrahim yayi murmushi mai dan sauti yace "alhmdlh ko daga kano bamu fitaba" Abdulrahman yace "OK Allah ya kiyaye hanya ka ku..." "...kula da kanka zan kula OK? Ka daina damun kanka I promise I will be fine zakuzo ku tarar dani in one piece OK?" Abdulrahman ya dan shafa kansa yace "shikenan bye Allah ya kiyaye hanya" Abdulrahim yace "ameen dan uwa bye".

Kafin dare sai da Abdulrahim da Abdulrahman sukayi waya yafi sau a kirga sunajin yadda juna suke, haka ragowar sati biyun suka kasance saboda training din da Abdulrahim yakeyi yasa sai dai shi idan ya sami time ya kira dan uwansa, dukkaninsu ji sukeyi tamkar gangar jikinsuce kawai ke tafiya amma babu ruhi wani irin feeling irin wannan feeling din da kakeji idan ka manta bakayi wani abu mai muhimmanci ba kullum haka sukeji har ranar da sukayi zasubi Abdul tazo.

Abdulrahman ya gama hada 'yan kudinsa dan yasan dole zai bukacesu kuma shi kansa Abdulrahim din zai bukaci kudi tunda yasan zuwa yanzu kudin da Abdul din ya tafi dashi a hannunsa ya kare, yana zuwa gidan dady ana e gobe zasu tafi dan yaji karfe nawa zasu tafi ga mamakinsa kawai sai dady ya dauko kudi da yawa ya bashi yace "ga wannan ka rike a hannunka ka kaiwa Abdul din dan nasan shima yana bukata sannan ni bazan sami damar binku yanzuba Saboda akwai wani meeting da zamuyi amma insha Allah kafin ayi final indai na sami dama zaku ganni, akwai gidan abokina a Abuja Alh Dahiru nayi masa waya na gaya masa zakuje sai ku sauka a gidansa ku hudu zakuje kai, Bello, Umar da Aliyu dan haka ku kula sosai Abuja ba kano bace ku kula Allah ya bada sa'a" duk suka hada bakin cewa Ameen ya Allah sannan Abdulrahman ya dora da godiya akan kudin da aka basu yayi godiya sosai, washe gari karfe takwas na safe a tasha tayi musu suka dau hanya sai babban birnin Abuja.

Karfe biyu na rana a cikin gidan Alh Dahiru tayi musu da yake dady ya basu number dinsa suna zuwa suka kirawoshi ya aiko dansa Sajidullah sa'an su Abdulrahim ne ya daukesu a tashar da aka saukesu, suna zuwa sukayi sallah sannan aka kawo musu abinci sukaci, sai da suka huta bayan la'asar sannan suka tafi inda aka sauki su Abdulrahim a wani kyakykyawan hotel kusada stadium din da zasuyi wasan, tunda suka shiga harabar wajen Abdulrahman ke baza idon ganin dan uwansa saboda sunyi masa waya sunce gasunan sun shigo wajen, zuwa can suka hangoshi ya taho da gudu wajensu da JC yellow a jikinsa yana zuwa ya rungume Abdulrahman shima ya rungumeshi su bello kuma suka kama yi musu dariya.

Bayan sun gama gaggaisawa su Bello suka tafi zagaya wajen sukabar su Abdul, bayan tafiyar su Bello Abdulrahman yace "so how are doing?" Abdulrahim na murmushi yace "good" Abdulrahman ya hade rai "good kawai? Iya abinda zakace kenan?" Abdulrahim yayi dariya "wai me yasa yanzu ka fiya saurin daukan zafi?" Ya bashi amsa da "zama da madaukin kanwa kai ka koyamin" sukayi dariya a tare Abdulrahim yace "banda missing dinka da nakeyi zan iya cewa ban taba rayuwa mai dadin da ta kai wacce nayi a wannan sati biyunba, kullum sai nayi fatan inama dai tare mukazo? Abinci sai wanda nakeso ga training ga kwararren coach ga gym gaskiya ba karamin dadi najiba wallahi Abdul naso tare muke" zuwa yanzu bakin Abdulrahman kamar zai tsage saboda murmushin jin dadin da yakeyi yace "ni inacan ina ta tunanin halin da kake ciki ashe kai dadinka kakeji" Abdulrahim yace "dama ai na gaya maka bani da wata damuwa sai ta rashinka" Abdulrahman yace "to alhamdulillah gaskiya naji dadi sosai Allah ya bada sa'a" Abdulrahim ya amsa da "ameen ya Allah dan uwa ina Amira" Abdulrahman ya sake fadada murmushinsa yace "ba kananan ta koma school ba?" Abdulrahim yace "dama so nake kayi wannan murmushin" sai kuka suka saka dariya tare, Abdulrahim yace "taso muje na nuna maka dakina" daga nan Abdulrahim yayi ta zagawa da Abdulrahman waje waje har inda suke training sai da ya kaishi, suna cikin tafiya suna hira wayar Abdulrahim ta fara ringing yana dauka akace masa shi ake jira zasuyi training dan haka yayi sallama da Abdul yace sai gobe idan sun hadu a wajen wasan.

Washe gari sai 9:00pm sannan aka fara wasan, dama tun magriba su Abdulrahman suke cikin stadium din, an tsara wasan zai gudanane a cikin national stadium Abuja (currently known as Moshood Abiola National Stadium) sannan team kano state zasuyi wasane against Kaduna state, iya kacin northern states ne keyi a Abuja su kuma southern States suna Lagos sai final sannan zasu hadu duk anan Abujan.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Stories to obsess over. Discover now