Chapter 24

54 9 0
                                    

Ranar asabar suka iso kano da karfe 9am, kamar lokacin da suka tafi yanzuma kowa trolley ce a hannunsa sai backpack a goye a bayansa, amma ba kamar yadda suka tafiba a yanzu wadannan cikakkun samarine da kana kallonsu zaka fahimci jin dadi da ilimi ya gama ratsa koina na jikinsu weather din California ba karamin karbar jikin kowannensu tayiba sun koma tamkar wasu black Americans, dukkansu blue jeans ne a jikinsu sai dai banbancin kalar riguna cikin izza da kasaita suke tafiya duk da su a wajensu normal tafiya sukeyi sai dai naturally yanayinsu ya riga ya koma hakan.

Suna fitowa kofar arrivals suka hango Amira sai baza ido takeyi kamar wadda tayiwa sarki karya, hankalinta a matukar tashe yake so kawai takeyi ta hango yayyenta idonta kamar zai fado kasa, itama kamarsu ta girma sosai shape din jikinta mai kyaune sosai komai nata daidai ita ba mai yawaba kuma ba kadanba, tana hangosu ta fara tsallen murna banda ba za’a barta ta shiga arrivals dinba kam da tuni ta shige ciki ta taroso, amma sai ta rike hannun Dady kam dan ta hana kanta zuwa ta taro wani daga cikinsu.

Suna fitowa sukayi wajen da suka hango su Dady, idon Abdulrahmanna kan kanwarsa sai washe mata baki yake, banda suna video call kam da sai ya kalleta ya kuma kafin ya ganeta dan girman da tayi, suna zuwa suka rungume Dady suna ta faman murna sai ga Prof shima suka gaisheshi haka sukayi ta bin sauran su Umar suna rungume juna cike da murna, bayan an gama gaggaisawa suka dunguma sai gida amma ga mamakinsu instead of suga anyi gidan Dady sai suka gansu a gidan Prof.

Suna shiga get din suka hango hajiya matar Prof a tsaye akan brander sai kara tsahon wuyanta takeyi kamar mai leken wani abu, bello na cikin mota yace “innalillahi wa inna ilaihir rajiun” duk suka juya suna kallonsa Amira tace “yaya bello lafiya? kai dawa?”  yace “me yasa mukazo nan gidan?” ta daga kafada alamar oho sai kawai tayi waje ta barshi yana mirgina kai, Abdulrahim ya dan daki kafadarsa yace “hey chill ba cinyeka zasuyiba” shima ya fice daga motar aka bar bello shi kadai.

Shi kam ya rasa wane daliline zaisa a kawosu gidannan? Dama yadda sukayi shine zasu sauka a gidan Dady tunda ba dadewa zasuyiba amma yanzu an kawosu nan, kafin ya gama tunanin me yasa kawai yaga ana fito da jakunkunansu daga boot din motar da sukazo a ciki da sauri yace “what! Ana nufin a gidannan zamu zauna ne ko me? Tab wallahi bazan zaunaba” da sauri ya fito daga motar ya nufi Abdulrahman dan jin wai sunsan da wannan zaman da yaga alamar ana shirin tilasta musu? Amma kafin ya kai ga Abdul din hajiya ta karaso da sauri ta rungumeshi tare da sakin kuka.

Ba karamin shock suka shigaba gaba dayansu me kenan? Me hakan yake nufi ina ruwanta da Bello da har zatazo ta wani rungumeshi tana kuka? Duk sai suka saki baki suna kallonsu shima sakin bakin kawai yayi yana kallon ikon Allah, da kyar Prof din yazo ya jata yana rarrashinta sukayi cikin gida su kuma su Abdul Umar ya jasu zuwa wani part a gidan inda aka shigar musu da kayansu.

Wani falone da dakuna guda uku kowanne da toilet a ciki, dakunan da kaya tamkar dama ana amfani dasu haka falonma da saitin kujeru da tv fridge da sauransu dakin yayi kyau sosai, suna shiga Umar ya nemi waje ya zauna yana cewa “welcome home” Bello yace “home? Home fa kace? Wallahi badai nan ne home ba” Abdulrahim yace “wai Umar tsaya nifa kaina ya kulle wai meke faruwane ban ganeba” Bello yace “tayani tambaya” Umar ya danyi murmushi ya mike sannan yace “ni kam ina da lectures by 2pm tafiya zanyi yanzu gashinan dakunane uku kowa ya zabi daya kuyi abinda zakuyi wanka, sallah, bacci whatever idan kun gama su zasu kirawoku su gaya muku abinda ke faruwa” ya juya yayi hanyar kofa har yakai ya juyo ya kallesu duk sun zubo masa ido yace “kundai san ba saceku za’ayi ba ko?” sai kuma yayi dariya ya fice.

Bayan fitarsa suka dawo da idanuwansu kan juna, Abdulrahim ya nemi waje ya zauna yana cewa “kai wannan abun fa ya fara yawa na kasa gane kan wannan abin kawai shikenan muna almajirai daga mutum ya ganmu sai ya fara nuna mana irin wannan kulawar? Sai dai idan da wani abun a kasa” Abdulrahman yace “amma kasan ko da wani abu bazai taba zama sharriba dan na yadda ko Dady zai rasa rayuwarsa ba zai taba sakamu cikin wani halinba kun sani, tunda kukaga Dady a ciki tabbas alkhairine ba sharriba” Bello yace “amma Abdul bana son muje muci bashin da bazamu iya biyaba, tun muna cikin tsummokaranmu Dady ya daukemu yayi mana suttura dan haka munsan shi dan Allah yake koma me yakeyi amma wannan fa? Sai da muka zama mutane kawai rana tsaka zai fara nuna mana irin wannan kulawar? Wannan fa har nema yake yafi Dady zakewa tunda gashinan munzo da murnarmu zamuje gidan Dady shi kuma ya daukomu ya kawo nan ya zube” Abdulrahman yace “nidai so nake mubi komai a hankali yanzu karmu yanke masa hukunci mu bari zuwa anjima sai mu tuntubi Dady na tabbatar shi zai fayyace mana komai” Abdulrahim yace “dan allah Abdul ka daina playing matured mana wai kai mai sanin ya kamata sai ka dingayin abu kamar wani ubanmu wannan abun a fayyace yake akwai wata a kasa” Bello yace “tayani gaya masa idan dai bada wani abu a kasanba me yasa kawai daga shigowarmu matarsa zata wani rungumeni tana kuka? Menene ma’anar hakan? meye hadina da ita?” Abdulrahim yace “nima dai abin ya matukar bani mamaki sai kace wata mai fama da wani ciwon?” Abdulrahman yace “nidai so nake ku iya bakinku kar kuzo kuna dana sani karku yanke musu hukunci ba tare da kunji daga bakinsuba kuyi shiru yanzu muyi abinda akace idan anjima sai muji abinda yake faruwar” Abdulrahim ya mike yace “ ahhh you are so boring” sannan ya dauki jakarsa yayi daki daya cikin ukun dake wajen ya barsu.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon