Chapter 22

47 8 0
                                    

Babu wanda yasan Abdul yayi wannan abun babu wanda yasan yadda akai tsakanin Abdul da mai girma gwamna sai da result din su ya fito suka je suka kaiwa dady, dady yayi murna sosai da ganin result dinsu duk da daman ya saka ran samun hakan amma hakan bai hanashi murna sosai ba, yace “to yanzu sai tafiya makaranta kai ina kakeson tafiya duk da naji a interview dinka kace BUK har yanzu BUK dince?” ya fada yana kallon Abdulrahim, Abdulrahim ya dan sosa keya sannan yace “aa dady na canja” duk suka kalleshi da mamaki dady yace “to yanzu ina kakeso?” Abdulrahim yace “stanford university ta California" baki gaba daya sukayi suna kallonsa Abdulrahman yace “Abdul” Abdulrahim ya kalleshi kawai yana dan murmushi yace “dady na fasa na zauna nayi tunani idan har kudi nakeso muyi da gaske zaman Nigeria bai kamamuba yadda bamu da wani connection bamu da kowa sai Allah sai kai idan muka samu exposure ba karamin taimaka mana zaiyiba, dady idan ni nace ina da abinyi su Abdul fa? Beside ball ba sana’ar dazan dogara da ita bace zan iya jin ciwo wanda bazan iya cigaba da ball ba, sannan idan na manyanta dole na barta amma idan na sami sana’a kaga shikenan sannan idan ance Abdul medicine yakeso yayi su suna saurin samun aiki Bello fa? NNPC basu da mutunci idanba da connection ba ba aiki zaka samuba duk kyan takardarka kuwa amma idan sukaga daga waje muke kaga mun karawa kanmu daraja da probability na samun aikin mu shima ya karu” dady yayi ajiyar zuciya sannan yace “to yanzu Abdul kana tsammanin a ina za’a samu kudin da su Abdulrahman zasu tafi idan ance kai kanada scholarship su kuma fa? Abdulrahman scholarhip din BUK ne dashi ba Stanford ba” Abdulrahim ya kalli Abdulrahman da ya kura masa ido danjin abinda zaice sai kuma ya dauke kai da sauri sannan “nayi amfani da card dina wajen gwamna kuma ya amince tare zamu tafi”

Gaba daya wajen yayi shiru kowa yana kallonsa kuma kowa ya rasa me zaice, zuwa can dady yace “yaushe ka yanke wannan shawarar sannan yaushe kaje wajen gwamnan?” Abdul yace “tun ba’afi sati da dawowarmu daga Abuja ba” Abdulrahman yace “amma ka kasa gayamin? Ka kasa gayawa dady ko Bello?” Abdulrahim yayi shiru bai amsaba kawai sai Abdulrahman ya mike ya fice daga dakin ya barsu da binsa da kallo har ya fice sannan Abdul ya dawo da idonsa kan dady yace “dady kaga wai yayi fushi” dady yace “gaskiya kaima baka kyautaba Abdul shi al’amari irin wannan shawara akeyi yanzu kaje ka gayawa mai girma gwamna kanason Standford idan kuma su basason kasarfa? Idan kuma suna da wani plan din fa? Kamata yayi ka nemi shawararsu kafin ka yanke irin wannan hukunci amma baka je ka yanke kai kadai kuma har kaje ka sanar da gwamnaba ka daina irin haka” Abdul yace “dady nayi hakanne fa dan nayi suprising dinsa banyi dan na bata masa raiba" dady yace “to yanzu kam ai kayi suprising din nasa sai kaje kuyi Magana ai nidai fatana Allah ya baku sa’a koma ina kuka tafi be it BUK ko Stanford din” haka suka tashi sukabi bayan Abdulrahman jiki a sanyaye da dokakkiyar gwiwa.

An kai ruwa rana sosai tsakanin Abdulrahman da Abdulrahim kafin daga baya Abdulrahman ya yadda, daman a ganinsa ta yaya Abdulrahim zai yanke irin wannan decision din ba tare da ya tuntubesuba? Daga baya dai bayan Abdulrahim yayi ta faman bada hakuri ya hakura sannan kuma suka fara shawarwarin yadda tafiyar zata kasance, gwamnatice zata nema musu admission dan haka babu ruwansu da wannan su yanzu nasu jirane kawai a kirasu ace sun samu ko basu samuba idan sun samu sai tafiya idan basu samuba kuma BUK itace plan B.

Ana cikin haka su Amira suka dawo hutu ranar da zata dawo su Abdul ne sukaje suka daukota murna kam kamar zata zuba ruwa a kasa tasha finally gata ga Abdul dinta sannan ga wannan kyakykyawan labari da take samu na abubuwan alkhairin da ya samu yayyenta, kamar yadda sukayi tsammani kam kwalliya ta biya kudin sabulu dan sosai Amira ba karamin canjawa tayiba, lokacin da suka hangota daga nesa kaf cikinsu babu wanda baiyi zaton dannowa zatayi da gudu ta rungume Abdulrahman kamar yadda ta sababa sai ga mamakinsu ta daiyi dan sauri amma ko gudun batayiba sannan kuma da tazo babu wanda ta runguma a cikinsu sai da suna tsokanartane ma ta buya a bayan Aliyu ta kifa fuskarta a kafadarsa tana dariya.

Wannan canji na Amira yayiwa kowa dadi atlast dai Amira an fara girma, Abdulrahmanne ke tuki da yake gidan dady babu wanda bai iya driving ba sai Amiransa kusa dashi baya kuma Aliyune da Abdulrahim tunda suka taho take faman basu labaran makaranta har suka iso gida, suna shiga cikin get din gidan ta fito ta kwasa da gudu sai cikin gida tana shiga ta dane dady tana ihun murna, Abdulrahman ya fito daga mota bayan ya gyara parking ya kasheta bakinsa har kunne yana kada kai a zuciyarsa yace ‘da saura kenan Amira ba zata taba girmaba’.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Where stories live. Discover now