Chapter 14

53 7 0
                                    

Haka su Abdul suka fara rayuwar makarantar boko sabuwar rayuwar da basu saba da itaba, suna zaune a aji wannan malamin ya shigo ya fita wannan ya shigo ya fita kuma kowanne ya shigo sai yayi noticing dinsu saboda kasancewarsu sabuwar fuska da kuma girmansu, a haka har akayi break suma suka biyo yaran ajin suka fito suna fitowa suka tarar ana raba abinci irin wanda wasu shugabannin ke rabawa a makarantun gwamnati, basu taho da kwanoba tunda basu san ana rabawaba sai da suka jira wani yaro yagama ci sannan da kyar ya ara musu nasa da suka je wajen karbarma sai da sukayi fada da prefect din dake rabawa wai ba’a hadawa kowa nasa yake karba daban, bayan an zuba musu suka koma gefe sukaci abinsu sannan sukaje wajen fanfo suka wanke hannayensu suka sha ruwa, a hanyarsu ta dawowane suka hango wasu yara na ball a cikin filin game din makarantar, da sauri Abdulrahim ya tafi wajen saboda shi kam daman ba karamin sha’awar ball yakeyiba, yana gani kullum da yamma yan unguwarsu sunayi amma bai taba shigaba sai dai ya zauna yayi ta kallo saboda baya so ya shiga su raina masa hankali shi kuma ba kyalewa zaiyiba dan haka sai yaga da muguwar rawa gwara kin tashi.

Yana zuwa wajen ya zauna yana kallonsu suna ta wasansu har su Abdulrahman sukazo suma suka tsaya suna kallo, Abdulrahim kafin a koma break sai da ya tabbatar ya yi abokai da kusan mutum uku cikin kwarin game din dan ya dau aniyar shima fa sai ya shiga yayi ball din ana tashi headmaster ya aika aka kirawo masa su Abdulrahim ya karbi littafansu masu jan layi guda dai dai ya yi musu rubutu sannan yace suje suyi ta maimaita abinda ya rubuta musu gobe suna zuwa makaranta su kawo masa.

Direct gidan su Amira suka wuce ai kuwa baiwar Allah tunda ta taso daga tata makarantar take zaune a kofar gida tana jiransu, tana hangosu kuwa ta tafi da gudunta ta taroso tana ta murna tunda yanzu ta gansu da uniform ta yadda da gaske makarantar aka kaisu, ita ta koya musu homework din da headmaster  ya basu dama ABCD ne, sannan da dady ya dawo yayi assigning Abubakar kan lesson din su Abdulrahman tunda daman education yake, kullum daga makarantarsu suke wucewa makaranta boko idan suka dawo kuma zasu wuce gidan dady suyi homework din headmaster da kuma wanda wani malamin ya basu sannan idan Abubakar na gida shima yayi musu lesson sai kuma suci abinci sannan su rankaya har su Umar su tafi allo tare dan haka yanzu abincin dare kawai suke baratowa tunda sunacin na safe a makaranta na rana kuma a gidan Dady.

Rayuwa na tafiyar musu yadda ya kamata suna zuwa boko kuma ga allo sunayi wanda har sun tasamma izu talatin, kullum idan sukaje gidan dady sai sun san yadda sukayi wani ya koya musu wani abun Abubakar, Umar ko Aliyu wani lokacin ma har Amira bata rasa abinda zata koya musu su kuma basa girman kan kin tsayawa su koya dan haka sai kansu yake budewa abin kamar a novel, Abdulrahim ne ma sometimes ake dan shan wahala dashi amma shima da ya waye shikenan yake gane komai, ranar da basu da makaranta kuma kasuwa suke tafiya suna ci gaba da sana’arsu ta siyar da kayan yara, zuwa yanzu su biscuit, cheese da alawa har katan suke budewa kuma insha Allah baya kwana biyu zasu siyar su siyo wani, har makaranta suke zuwa dashi sai su ajiye a staff room sai an fito break sai su dauko su siyar abinsu idan kuma a allone sai su saka kayan a gabansu suna zaune da allunansu suna karatu kuma suna ciniki ganin da malam yayi hakan bai sa suna wasa da karatunsu yasa bai hanasuba.

Tunda akayi case din matar nan da ta sace musu kudi sai malam yace su dinga kawo masa shi zai cigaba da ajiye musu dan haka duk wani dan ribar da suka samu sai suje su kaiwa malam ya saka musu a banki sannan kuma da littafi ana lissafa yawan abinda suka ajiye.

Yanzu babban abinda ya ke dauke hankalin Abdulrahim bayan karatu shine ball, idan yana buga kwallo tamkar ranar wasan kwallo ta duniya aka haifeshi, ba zaka taba cewa bai dade da fara bugawaba, nan da nan yayi suna a kurmawa saboda kokarinsa abin a jininsa yake hatta malamin PE din makarantar yasan da zamansa, da yaga ya ware sai ya fara shiga cikin yan unguwar tasuma sunayi tare, da farko kin yadda sukayi sai da yayi suka gani sannan sai kuma ya zamana wani lokacinma har fada akeyi akan team din da zai shiga saboda duk wanda ya buga kwallo dashi to kuwa sai ya cinyeshi.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Où les histoires vivent. Découvrez maintenant