Ranar gaba daya haka suka kwana kowa rai babu dadi, washe gari da safe abdulrahim ya fice suka nemeshi suka rasa sai can wajen hantsi sai gashi da kashu cikin wata katuwar leda yana shigo tun daga waje yake kwada mata kira “inna inna” da sauri ta fito daga dakinta tana tambayar abinda ya faru da kuma tambayar daga inda yake dan tun safe take nemansa, yana zuwa ya daga ledar ya juye kashu din a kasa yana nuna mata “inna kinga abinda na samo miki, da yawa duk sun nuna wannan kuma da basu gama nuna ba zaki iya nukasu daga baya sai kisha ko?” ya fada yana ware wadanda suka nuna da wadanda basu gama nunaba, rai ta hade tace "a ina ka samo wannan kashu din? Nace maka ina so ne?" Jikinsa a sanyaye ya dago yana kallon innar yasa yace "inna.." Bata bari ya karasaba tace "ba na hanaka shiga gonar mutane ka ciro musu abuba?" Da Sauri yace "wallahi inna sai da na tambayi mai gonar Allah kuwan" ganin yadda jikinsa yayi sanyi itama kuma sai jikinta yayi sanyi ta tsaya kawai tana kallonsa, a hankali ya matso kusa da kafarta yace "inna dan Allah dan annabi kiyi hakuri wallahi ba zan sakeba insha Allah zan daina duk abinda bakyaso na daina dan Allah ki daina bata rai a kaina dan Allah kinji?" Ya fada yana goge hawayen da ya zubo masa a idonsa, a hankali inna ta matso kusa da abdulrahim tace "ya isa share hawayenka na hakura Allah ya shirya min kai" da sauri yace "ameen inna na daina ma insha Allah" tace "Allah yasa" wannan ya kawo karshen wannan takaddama sai ci gaba da biyan kudin magani da kubra tayi har yaron ya warke.
Cikin jikin Inna yanzu watanninsa goma kenan, hankalinta ya fara tashi ammasu Abdul da yake yarane basuma San abinda ke faruwaba harkarsu kawai suke sai dai Abdul Rahman ya fahimci akwai abinda ke damunta, haka zai zauna yayi ta tambayarta Amma sai ta nuna masa ba komai. Wata rana yaran na sharar tsakar gida ita kuma tana tankade garin da ta daka yanzu, yau tun safe take jinta wani iri daurewa kawai take tanaso ta kammala tuwonnan tukunna sannan tajeta kwanta dan tasan ko nakuda takeyi jaru ba zata karbar mata girkin da takeyiba, watakil ma baccin da bata samu bane yau yasa dan haka da sauri sauri ta gama duk abinda zatayi Allah ya taimaketa ta kammala tuwon ta kwashe su Abdul suka kaiwa kowa nasa wanda za'a dumama kuma gobe da safe ta sakashi cikin tukunyar ta rufe, ai kuwa ciwo tamkar jira yake ta rufe wannan tukunya ya taso mata gadan gadan, sai a lokacin ta fahimci naqudace takeyi tun safe, da kyar ta Kai kanta daki Abdul Rahman da yake mai kulane tun tuni ya fahimci bata da lafiya Dan haka ya bita daki Yana mata sannu, hannu kawai ta daga masa sai da ciwon ya lafa sannan tace "Abdul maza jeka kirawomin Yaya" tana nufin jaru kenan.
Da gudu yaro ya tafi ya gaya mata Amma sai cewa tayi "raguwar banza da wofi nakudar takewa wannan rakin daga farawa zatace a wani kirani? To jeka cene mata Ina zuwa ni yanzu tuwo nakeci" haka jiki a sanyaye yaron ya koma ya fadawa innarsa "tace tana zuwa" tun ana kiyaye kirayen sallar magriba kenan akai wannan abu Amma jaru ba ta leka dakin kubraba sai wajen 9 na dare shima da taje ta tarar yaran sun sakata a gaba suna mata sannu suna share hawaye sai ta kama bala'i "Kai jama'a nikam na gaji da kallon wannan abin kunya Wai wadannan din yayan farine kuma maza kika saka a gaba kina nakuda saboda rashin kunya ko? To ai shikenan su da kika tasa a gaba su tayaki" tana gama fadin haka kuwa ta juya zuwa dakinta, da gudu Abdul Rahman ya bita Yana bata hakuri "Dan Allah innar habu kiyi hakuri wallahi zamu fita kizo ki taimakawa innarmu Dan Allah kar ta mutu Inna kinji" ta hankadeshi ta shige daki tana fadin "Kai tafi can ni dama bacci nakeji ba iyawa zanyiba banda bala'i wake taya kishiya nakuda da zaku addabi rayuwata? Wato ga marar gata ko? To nima bazan iyaba ai dama duk abinda kukeyi kyaleku nayi" Haka yaran suka garzaya da gudu zuwa gidan wata ungozoma dake nan kusa dasu suna kuka suka gaya mata halin da innarsu ke ciki ba shiri kuwa ta biyosu har lokacin kuma babansu bai dawoba, bashi ya dawoba Sai can dare ya tarar har a lokacin bata saukaba shima sai kawai yayi shigewarsa dakinsa ya kwanta.
Baiwar Allah haka ta kwana biyu tana abu daya da ungozoman taga abin yafi karfinta sai ta samu mal musa Yana zaune a runfar dakinsa Yana cin masara gashashshiya da yake lokacintane, ta zauna suka gaisa sannan tace "mal musa dama akan yarinyarnan ne abinnan yayi yawa kwana biyu muna fama Amma haihuwar tayi gaddama wallahi ta galabaita da yawa ni dai Ina ganin mezai hana a kaita kaura can asibiti ko Allah zai taimaka sai kaga ta haihu ko ya kace?" Sai da ya gama cinye masarar da ya banbaro sannan yace "ba akwai kuma yan dabarun da kuke dasuba? Ayi amfani da wata dabarar mana" ungozoma ta juya Kai cike da tausayin kubra tace "wallahi mal musa Babu dabarar da na sani da banyi amfani da ita akan yarinyarnan ba, har barkono na tukaka mata Amma sai dai kaga numfashinta na neman daukewa Amma Babu wani ci gaba" yanzuma shiru yayi Yana faman taunar masararsa har sai da tayi tsammanin bazai bata amsaba ta yunkura zata tashi sannan yace "nifa asarar kudine banaso yanzu kana zuwa asibiti sai suce sai ka kashe wasu kudade ni kuma bani dasu ehe" shiru sukayi duk su biyun zuwa can ta kuma cewa "yauwa to indan hakane akwai yaronnan Dan gidan mari yayi karatun likitanci ko shi zaka kirawo bashi da tsada Dan ko naira dari ka bashi karba zaiyi kuma Yana karbar haihuwa sosai" jin ance naira dari kawai yasa mal musa mikewa yace "yauwa bari na kirawoshin" Nan ya kada babbar riga ya fice ita kuma ta koma dakin kubra sukabar su Abdul nan Abdul Rahman na kuka yayinda Abdul Rahim ke jin tamkar yaje ya shake baban nasu saboda a gaban idonsa aka kawo masa dubu goma yanzunnan Amma yace wai bashi da kudin da zai Kai mahaifiyarsu asibiti.
Zuwa tsahon awa guda mal musa ya shigo tare da yaron da akace yayi karatun likitanci, kallo daya Abdul Rahim yayi masa ya dauke Kai tare da Jan uban tsaki, da sauri Abdul Rahman ya kalleshi da alamar tambaya yace "kaikuma Kai da wa?" A kule Abdul Rahim yace "yanzu wannan ne likitan? To ai ko malamin makarantarmu yafi wannan tsafta daga alama kuwa yafishi ilimi" da sauri Abdul Rahman ya toshe masa baki yace "shsh karka bari yaji indai zai taimaki Inna mudai Ina ruwanmu da tsaftarsa?" A cikin dakin kuwa suna shiga suka tarar kubra har ta fara fita a hayyacinta saboda wahala batasan Wanda ke kantaba, suna zuwa likita ya zira hannu a aljihu ya zaro bakar leda ya nada a hannunsa wai da ita zaiyi amfani a matsayin handglove, ita kanta ungozoman baki ta saki cike da mamaki tace "da wannan zakayi amfani?" Kai kawai ya kada mata ya fara abinda ya kawoshi, sai da ya shafe sama da awa biyu sannan ya iya ciro babyn, ya cirota mace kyakykywa da ita katuwa tubarkallah sai dai tana fitowa tamkar an bude bakin fanfo jini ya tsinke mata, shi kansa likitan sai da ya tsorata saboda yadda jinin ke zuba, har wani bulbul yakeyi kamar da bakin jarka, Nan da Nan yace da mal musa "Mal Ina ganin fa asibiti ya kamata a kaita wannan jinin yayi yawa" yamutsa fuska kawai yayi yace "ku wai Kuna ta maganar asibiti asibiti Ina naga kudin kaita asibitin? Kawai kayi abinda kaga ya dace" Yana gama fadar hakan yayi ficewarsa.
Kallon kallo aka tsaya yi tsakanin ungozoma da likita tace "yanzu likita ya zamuyi?" Shima hankali a tashe yace "wallahi iya ban saniba kuma wallahi mutuwa zatayi idan aka barta a haka" a hankali kubra ta dago hannu ta kama hannun likitan ya kalleta da sauri sannan tace masa "Dan Allah zan iya ganin yarana?" Da sauri yace "me zai hana bari na kirawo miki su" Nan ya leka runfar dake wajen dakin inda su Abdul suka hada Kai da gwiwa sunci kuka sun koshi yace su zo, da gudu suka shigo dakin suka durkusa a gaban mahaifiyarsu, ta sakar musu wani wahalallen murmushi ta na kallonsu tace "menene kuke kuka? Babu abinda zai sameni kuma ma koda wani abu ya samenin ai nasan zaku kula da kanku ko?" Da sauri suka daga Kai sannan ta cigaba "Abdul Rahman karka canja hali ko wanne irin tsanani zaka shiga ka cigaba da hakurin da na sanka dashi ka kula da dan uwanka karka bari wani abu ya sameshi kaji?" Kai ya kuma kadawa yana kuka, shidai jikinsa ya bashi wani mugun abu na shirin faruwa da mahaifiyarsu yasan kuma bashi da ikon hanawa, ta kalli Abdulrahim tace "Abdul Rahim Dan Allah ka rage zuciya kaji? Ka daina fada da mutane duk abinda hakuri bai bayarba rashinsa ba zai taba bayarwaba duniya Yar karamace kuma a yadda ka dauketa a haka take zuwar maka idan ka dauketa da zafi da zafi zatazo maka idan ka dauketa da sanyi sai tazo maka da sanyi Dan haka Dan Allah Abdul Rahim ka sakawa zuciyarka salama kaji? Kaima ka kula da Dan uwanka kuyiwa mahaifinku biyayya kunji ni kuma ku rinka yimin addu'a Ina Nan tare daku aduk juyin da rayuwa zatayi daku Allah yayi muku albarka" daganan tayi shiru tana ci gaba da numfarfashi su kuma suka kwantar da kansu a jikinta suna ci gaba da kukansu.
A can tsakar gida kuwa sai ga mal musa da makara mutane na biye dashi ana masa sannu Yana sabe babbar riga, suna shigowa jaru ta fito daga ban daki kawai taga mutane na shigowa da makara da sauri tace "subhanallahi malam lafiya? Wannan makarar fa?" Ya kalli yaran da suka dauki makarar yace "yauwa sannunku ku jingine ta anan" ya fada Yana nuna jikin dakinsa sannan ya waigo ga jaru yace "yauwa an shiryata?" Da mamaki tace "Wai malam wa?" A zuciye yace "kubra mana" da sauri tace "au Wai ta sheka?" Kawai sai mutanen dake tare da malam musa suka tsaya suna kallonsu cike da mamaki ganin an zubo masa ido yasa ya hauri takalma ya wuce dakin kubran Yana fadin "banason shashanci ana Miki magana kina rainawa mutane wayau" Yana faman fada ya bankada labulen dakin, su Abdul Rahim suka dago Kai suna kallonsa kawai, banza yayi da kallon tsanar da suke jifansa dashi ya karasa kan kubra Yana cewa "au Ashe bata karasa ba tukunna sannu" murmushi takaici tayi tace "idan kayi hakuri zan karasa dinne idan kuma ba zaka iya jira na shaki sauran numfashin da yayimin ragowaba zaka iya karasani sai dai ka sani inda zan tafin kaima dole wataran ko badade ko bajima zakaje dolece, mutuwa rigace ba kuma ka isa ka ciretaba" ungozoma dake gefe tana sharar hawayen bakin ciki tace "kubra ga yarinyar fa baki gantaba" ta kawo mata ita zuwa kirjinta, ta kalleta tana murmushi hawaye na zubowa daga idonta tace "tubarkallah ubangiji ya rayaki yasa mai zamace yayiwa rayuwarku albarka gaba dayanku" tsayawa tayi tana maida numfashi sannan ta cigaba zuwa yanzu jikinta yayi fari tas ya kuma kunbura kana ganinta kasan Babu jini ko kadan a jikinta "Abdul Rahman". Da sauri ya dago Kai Yana goge hawayen idonsa idanunsa sunyi jajir jijiyoyin kansa sun fito rada rada, numfashin ta kuma ja da alama ya fara yi mata wahalar shaka tace "ga khadija nan inaso kayi mata Kiran sallah a kunnenta ka iya ko?" Kai ya gyada ta cigaba "kayi mata Kiran sallah sannan ka rada mata Khadija duk da nasan ba lallaine tayi tsahon kwanakiba Amma ga amanarta nan Abdul Rahim ku kula da ita kunji? Ku zame mata uwa ku zame mata uba ku Zama gatanta na barwa Allah na bar muku ku kula da kanku ku zamo wadanda manzon Allah zaiyi alfahari daku a matsayin alummarsa ranar gobe kiyama ku guji abin tir Allah ya iya muku yayi muku albarka" daganan ta fara shakuwa da sauri yan biyun suka Mike neman ruwa sai dai kafin su samo ruwan sai gawa suka dawo suka tarar rai yayi halinsa kubra ta tafi gidan gaskiya tabar su mal musa suci abinda akeci a duniyar idan akwai.
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
