Chapter 04

52 12 0
                                    

Can kan wasu duwatsu cikin bishiyoyin kalgo sukaje suka zauna, har yanzu Abdul Rahman kuka yake shi kuwa wanda aka daka dinma kamar ba shi aka dakaba, ganin da gaske bazai dainaba Abdul Rahim ya Dan daki kafadarsa yace "Kai Abdul ya Isa haka ko Kai aka daka ai yaci ace yanzu ya daina maka zafi, ka daina kukan haka dan Allah kaga Khadija duk a tsorace take" harararsa Abdul Rahman yayi yace "ba dole ta tsorataba Wai Abdul Kaine da zagin baba, kasan kuwa irin fishin da Inna zatayi da zata dawo taji abinda kayi? Babanmune fa" kafada Abdul Rahim ya daga alamar hakan bai dakeshiba yace "babansu mudi dai ba mu ba, ko ka manta abubuwan da yayi Mana? Makarafa ya dauko ya tsaya a gaban Inna yace Yana jiran ta karasa mutuwa zai binneta, ka manta irin azabar da yake gana mana? Mu fa mukayi masa noma amma abinda zamuci ya saka kafa ya kifar, koda bamuyi masa nomaba indai mu 'yayan sane da gaske ai bazamu rasa abinda zamuci a cikin gidansaba balle kuma" share hawaye Abdul Rahman yayi ya juyo yana kallon dan uwansa sosai yace "duk da haka koma me yayi mana kai kasan babanmune kuma kasan abinda malamanmu suka gaya Mana akan yiwa manya rashin kunya sannan na tabbatar da ace Inna tana da rai yau sai ta dakeka itama saboda kasan ta hanaka rashin kunya amma kayi" durowa Abdul Rahim yayi daga kan dutsen da suke zaune yace "sai kuma gashi bata raye" Yana fadin haka ya juya yayi tafiyarsa ya barsu a wajen.

Haka ranar suka wuni su basu koma gidanba balle suyi bautar da suka saba ko a taimaka a sanmusu abinci, ba kuma susan inda zasuje suciba haka sukayi ta garari sai da yunwa ta ciwosu Khadija tayi ta kuka sannan sukaje wata gonar babansu da ya shuka dankalin hausa suka tono suka hada yan karare suka gasashi sukaci.

Basu koma gidanba sai dare suna zuwa suka shige daki suka kwanta sai dai basu saniba ashe jaru ta saka sale ya jire mata su kawai sai jin duka sukayi wai yau basuzo sunyi mata komaiba ko ice basuyo mataba sai mudi ta saka ya yi. Haka aka zanesu hatta Khadija bai bariba da yake shima ba karamin mugu bane, sai da ya tabbatar ya fitar musu da jini a jikin kowanne sannan ya juya ya fice yana cewa "gobe ma kuki yin abinda aka sakaku kuga yadda zanyi daku" haka yaran suka hada kai sukayi kukansu mai isarsu sukayi bacci suna ajiyar zuciya.

Washe gari tunda sassafe suka tashi kamar yadda suka saba sukayi sallah sannan suka fara diban ruwa, kafin rana tayi zafi sun gama sun share gidan tas Abdul Rahim Yana wanke wanke Abdul Rahman ya dumama sauran tuwon jiya sannan suka zauna jiran Azo aci a sanmusu ragowar kamar wasu almajirai.

Sai can bayan Rana ta fito sannan jaru da yaranta suka tashi, ba sallah ba salati ko wankin baki babu suka fara lodawa ciki tuwo kamar jakai, sai da suka tabbatar babu dauran wajen ajiyar abinci a cikinsu sannan ne jaru ta zubo wani da bai wuce mutum daya yaci ba ta miko musu tana cewa "'yayan jaraba sun zubawa mutane ido kamar zasu cinye gashinan dauki kuci karku cinye mu" Abdul Rahman ne ya iya tashi ya dauko musu suka zauna sukaci duk da khadija suka barwa ta kusan cinyewa dan ba isarsu zaiyiba idan suka ce zasu saki jiki suci.

Sun gama kenan suna wankin hannu sai ga baban ya shigo da sauri sai cewa yayi "naga tunda kunyi girman fara zagina nan gaba ice zaku saka ku dokene Dan haka Kai.." ya nuna Abdul Rahman "shiga ka hadomin kayanku almajiranci zaku tafi" gaba daya suka dauka a tare "almajiranci kuma?" Dariya jaru ta fara tace "malam almajiranci kuma? Wa ya baka wannan shawarar?" Mal musa ya nema can gindin bishiyar dake tsakar gidan ya jabe kamar kayan wanki har maida numfashi yake saboda saurin da yayi yace "wallahi in gaya kiki kwana nayi jiya ina tunanin yadda zanyi da yarannan saboda na gaji da ciyar dasu ke a takaicema na gaji da ganinsu Amma ban Sami amsaba da yake Allah na sona ina fita da safennan kamar ance nabi ta kofar hakimai kawai sai ganin wani malami nayi yazo daukan almajirai ai kuwa kamar anmin bishara nace masa tsaya nima Ina da kankararrun yara bari na kawo maka, Kinga idan suka tafi ai na rage wani abun ko?" Wata muguwar dariya jaru ta kwaso harda kifewa tace "ah lallai kam malam ka iya tuggu, ragi bama kadanba" 'yar karamar dariya Abdul Rahim yayi yace "ai ba'a zuwa almajiranci da mata" da mamaki suka kalleshi sannan sukace "Kai macene?" Ya girgiza Kai yace "aa Khadija nake nufi kasan dai ba'a zuwa almajiranci da Mata musamman ma kuma yara" dariyar mugunta uban yayi yace "ai da ni ce maka nayi da ita zaku tafi? Anan zaku barta kai wuce ka hado muku kayanku malam nacan na jira" kuka Abdul Rahman ya fara Yana cewa "baba dan Allah dan annabi kayi hakuri ta yaya zamu tafi mubar Khadija ita kadai? A wajen wa zamu barta? Baba bata da kowa sai mu dan Allah ka kyalemu" ganin bashi da niyyar tashi yasa mal Musa ya yunkura ya shiga dan dakin nasu ya fara hada tsummokaran kayansu yana cewa "naka wasane, Mal nacen da kyar na rokeshi ya tsaya bazan bari kayi silar da zai tafiba" yayinda shi kuma Abdul Rahman ke faman kuka a tsakar gida.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Where stories live. Discover now