Chapter 18

59 8 0
                                        

Tun daga ranar da Dr Abdullahi ya tafi kullum Khadija acikin zuba idon jiran ganin dawowarsa take amma shiru har yanzu babushi babu alamarsa, kullum sai ta fito kofar gidansu ta zauna tana kallon hanya har sai magriba tayi sannan zata tashi ta shiga gida kuma gobema haka zata kuma zuwa ta zauna, su jaru basusan da tafiyar da Dr yayiba dan haka suma kullum cikin zuba idon ganinsa suke suna tsoron yin wani abun kar suje suyi daidai da ranar da zai dawo.

Watannin Dr Abdullahi shida kenan da tafiya har yau Khadija bata daina saka ran dawowarsaba sai dai zuwa yanzu yan gidansu sun ware sun fahimci ba fa zai dawoba dan haka duka da zagi ya dawo sabo, ga aiki kamar jaka itace shara wanke wanke daukan ruwa da yan kananan shekarunta amma idan kaga abinda take daukan ruwan dashi sai kayi mamaki.

Yanzu Khadija ta koma kazama dan babu wanka ba wanki dan bata da lokacin yinsu gaba daya lokacinta na bautane sai dai wani lokacin adi matar Habu kan kirata da niyyar kamar zata aiketa sai su tafi rafin garin ta sakata tayi wanki sannan tayi wanka nan bayan yan bishiyu dan ko daukar ruwan tayi ta tafi dashi gida to fa ba za'a barta tayiba, ko abincine wani lokacin ma sai dai adi ta kirawota dakin ta suci nata abincin dan ita khadija bata da kwano sai dai idan an gama ci abinda yayi saura ko kanzo idan ya kama ta kankara taci.

Wata rana Khadija na sharar tsakar gidan dan duk girmansa yanzu ita take shareshi idan kuma bai fitaba ta sake, adi ta leko daga dakinta tace "ke Khadija zo nan" Khadija tace "shara nake" adi tace "ni kuma nace ki ajiye sharar kizo nan ko zan zauna jiranki sai kin gama zakiyimin abinda zakiyimin?" Khadija ta ajiye tsintsiyar hannunta tana kallon jaru dake zaune tana sakar kaba ko zatayi mata magana amma sai kawai ta dauke kai ta cigaba da abinda take yi, Khadija ta shiga dakin adi tace "adi gani" adi ta jawo wani kwano daga karkashin gado ta bude tana cewa "kin wani makale a bakin kofa ki shigo kiyi sauri kici dankaline Yayana ya kawomun nace nasan tun safe bakici komaiba bari na kirawoki kici maza zo ki zauna kafin yanzunnan a kuma kwada miki wani kiran" Khadija tayi sauri ta zauna suka faracin dankalin sai dai ko loma uku kwarara batayiba jaru ta daga labulen dakin ta shigo gaba daya, ta kare musu kallo su da kwanan dake gabansu sannan tace "ehh lallai sannunku fitsararu lallai adi kin cika munafuka wato sai kizo kina wani fiffika kina masifa kiyi kiran yarinya ashe abinda kikeyi kenanko? Ke ga mai tausayi salon yarinyar ta rainani tace ina zalintarta ko? To wallahi yau sai kun gane kuranku dagake har ita dama na fara zargin wani abun kukeyi ashe kuwa" adi ta mike tsaye tana cewa "kiyi hakuri innar bintu wallahi..." Jaru ta katseta cikin tsawa "ke dalla rufemin baki munafuka yau zanga wanda ya tsaya miki a gidannan da har zaki hade kai da makiyana" adi ta danyi murmushi tace "innar bintu banajin zakiji dadin ganin wanda ya tsaya min dan banajin hakan zai miki dadi makiya kuma da kike magana tsakani da Allah me yarinya yar shekaru biyar tayi miki da har ta zama makiyiyarki? 'Da fa na kowane bakasan wanda zaiji kankaba sannan idan ke Khadija makiyiyarkice ni batayimin komaiba dan haka bazan taba azabtarda itaba wai dan in faranta miki" jaru tace "ehh lallai adi wuyanki yayi kauri ni kike gayawa magana? Ni jaru kike maidawa da magana?" Tana daga hannu ta sauke shi a kuncin adi, Khadija ta mike a tsorace jiki na karkarwa a daidai lokacin Habu ya shigo dakin, yana shigowa adi ta rike kunci ta dinga zabga ihu shi kuma ya gigice kira yake "me ya sameki adi uban waye ya tabaki kaf gidannan gayaminshi" cikin gunjin kuka tace "innace kawai daga na kira Khadija na sakata shara shine ta biyota wai itama shara take mata ina bata hakuri dan ni bansan shara take mata ba shine kawai ta zabgamin mari yanzu ni ko gani sosai banayi na shiga uku haka kawai za'a maidani makauniya ni wallahi ba zan iya wannan zamanba" da sauri Habu yace "me kike nufi ba zaki iya zamaba? Ni na ajiyeki ba waniba dan haka wallahi idan mutum nason zaman lafiya a gidannan kar ya kuma tabamin mata dan ba zaman wani takeyiba ehe" cikin tsananin mamaki jaru tace "Habu ni kake gayawa wannan maganar" yace "me yasa kika tabamin mata? Babu zaman wanda takeyi a gidannan wallahi babu mai takura mata idan ana son zaman lafiya kenan" ya matso kusa da matarsa yana cewa "share hawayenki kinji babu mai tabaki a gidannan na kyaleshi kiyi yadda kikeso kinji?" Adi ta daga kai tana share hawaye shi kuma ya dauki rigarsa ya kalli uwar sannan ya daga labule ya fice yana cewa "wallahi gatanan a kuma tabata aga tashin hankali a gidannan danni yanzu a kanta ba wanda bazan iya rabuwa dashiba".

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Stories to obsess over. Discover now