Chapter 09

40 8 0
                                    

Bayan tafiyarsu Abdulrahman ya juya shima ya tafi neman ruwan alwala dan har an fara kiran sallar isha dan dai suna da abinci da yau haka zasu kwana tunda yanzun nan za'a shiga karatun dare, bayan yayi alwala yayi sallah ya tarar da su Abdulrahim suna jiransa har yanzu Abdulrahim fushi yakeyi shima sai ya shareshi ko bi ta kansa baiyiba dan yasan zai saukone, suna cikin cin abincin yaji kamar an taho da gudu an dafashi, da Sauri ya waiga Amira ya gani tana haki alamar gudu tayo da mamaki yake kallon ta sannan ya kalli bayanta ya kuma kallon ta yace "Amira me kikeyi anan ke da wa kuka taho?" Yana ci gaba da kallonta, tace "ni kadai na taho yanzu na gane hanya" sannan ta miko masa takalmin hannunta ta cigaba da cewa "ga takalmi na samo maka" takalmin ya kalla da gani sunyi masa yawa sannan sababbine kuma na yan gayu irin na fita unguwa dinnan dan haka yace "takalman waye wannan amira?" Tace "takalmin Yaya Abubakar ne dama ba yace zai baka takalmiba? Shine naje na zabo maka wannan yafi kyau ka saka ka gani zaiyi maka?"

Abdulrahman ya Juya ya kalli su Abdulrahim kallon neman shawara dan yasan wannan takalmin daukowa tayi watakil ma ba'a san ta daukoba, bello yace "shi Yaya Abubakar din yasan kin dauko masa?" Ta girgiza kai jikinta nayin sanyi saboda kallon da sukayi mata Bello ya maida kallonsa wajen Abdulrahman yace "mu karasa cin abinci muje mu maida musu basu san ta dauko ba sannan itama mu maida ita gida tun kafin a fara neman ta, ke kuma.." Ya fada yana nuna Amira da ta zaro manyan idanuwanta a tsorace ya cigaba "idan kika kuma fitowa ke kadai sai na zaneki yanzu da wani abin ya sameki kuma fa? Ko kin kasa gane hanya? Sannan idan kika kuma dauko abinda ba'a bakiba kika kawo mana shima zaneki zanyi kinjiko?" Ta daga kai idonta yana kawo ruwa.

Bayan sun gamacin abincin suka tashi suka sakata a gaba har gida, wannan karon ta gane har kofar gida ta rakasu, gidan katone sosai da katon get dan haka suka buga kofar sun dan dade suna bugawa sannan wani saurayi yazo ya bude kofar, da alama shima zai girmi su Abdulrahman amma kuma bai karasa Abubakar ba, yana budewa ya kare musu kallo sai kuma ya kalli Amira da itama ta kafa masa ido, bakin mamaki saurayin ya bude yace "Amira? Daga ina kike?" Sai kuma ya koma cikin gidan da gudunsa yana kwala kira "momy momy?" Wata mata  ta bude kofar da ta shiga gidan Tana cewa "haba umar wannan wane irin kirane kakemin haka kamar makaho kuma a kofar gida?" Sai kuma tabi su Abdulrahman wadanda suka shigo harabar gidan da kallo sannan ta sauke idonta kan Amira dake buya a bayan kafafuwan Abdulrahman sai zare ido takeyi, tace "Amira? Dama ficewa kikayi? Ba bacci kikacemin zakiyiba?" A zuciye tayo kanta ta fara dukanta yana cewa "ban hanaki wannan tsinannan yawonba? Ba dazunnan aka kawo ki daga batan da kikayiba? harda zuwa ki kwanta kice min zakiyi bacci shine kuma sai ki fice?"  Ihu Amira ta fara tana kiran "dady dady yaya Abubakar yaya Abdulrahman” babu yadda Abdulrahman baiyiba don ya kareta sai dai dole saida wani dukan ya sameta duk da most of dukan akan Abdulrahman din ya kare, ana cikin hakan dadyn ya fito da sauri ya janye momy yana cewa “haba mariya me kikeyi haka kike dukanta haka?” momy na maida numfashin duka da kuma hargagin da tayi tace “yanzu dady me Amira takeso idan ba dukaba? Dazu ta dage sai tabi su umar makarantar allo suna zuwa ta bata sai bayan sallar magriba fa sanna suka samota ban daketaba shine yanzu dan rainin hankali tace bacci zatayi ni dama abin ya bani mamaki ace amira da baccin wuri amma na kyaleta sai cewa tayi wai a dakin Abubakar zatayi akan idona ta shiga dakin bansan yadda akayi ta fitaba sai gashi yanzu an kawota da kuma wani abun ya sameta fa? Ya takeso nayi da raina a darennan da wani abun ya sameta ya zanyi?” ta karashe maganar kamar zatayi kuka, su Abdulrahim dady ya kalla yace “wadancan kuma fa?” Abubakar yace "sune suka tsinceta dazun ahannunsu muka karbota” umar ma yace “yanzuma su suka kawota” ciki dady ya juya yana cewa “ku shigo ciki har yaran”

Suna shiga ciki kowa ya samu waje kan kujeru suka zauna yayin dasu Abdulrahim suka makale can bakin kofa suna zare ido kamar an tsoma zakaru a ruwa, Amira dake jikin abubakar tun daya dauketa a waje ta dago kai suna hada ido da dady daya kura mata ido ta sake kwabe baki ta saka kuka shi kuma ya mika mata hannu ta taso daga kan cinyar Abubakar ta dawo wajen dady, saida tagama kukanta sannan dady ya goge mata hawayen yace “princess me yasa kika fita? Kinsan na gaya miki banason wannan wayon ko? momy ma bataso amma shine kika fita me yasa kika koma makarantar?” tana sheshshekar kuka tace “dady yaya Abubakarne yace zai bawa yaya Abdulrahman takalmi saboda shi almajirine bashi da takalmi kuma da naje kan gadonsa zanyi bacci sai naga ya manta bai kai masa ba shine na dauka naje na kai masa” dady yace “ina takalmin yanzu?” tace “yana wajen yaya Abdulrahman” kallonsa ya maida kan yaran dake zaune a gefe, takalman abdulraman ya dauko ya mikowa dady ai kuwa abubakar dake kwance yana game ya mike zaune yana cewa “princess?” umar ya saka dariya shi kuma ya dau fillow din kan kujerar ya jefa masa, dan murmushi dady yayi sannan yace “haba princess tunda yaya Abubakar yace zai bashi ai zai bashinne me yasa zaki dauka ki kai masa? Wannan ba kisan takalman yaya Abubakar dinne na sallaba? Ki bashi hakuri” ta kalli Abubakar din da kwababbiyar fuska tace “Allah ya baka hakuri” dan murmushi yayi mata sannan ya cigaba da game dinsa, amira ta kalli dady tace “dady yaushe zai bashi takalmin? Kaga nima dazu da yara suka daukemin takalmina shine ya goyani saboda inajin zafin rana ina kuka shima dady a dauko masa kaji?” dady na murmushin jin dady yarinyarsa tasan maida alkhairi ga wanda yayi maka alkhairi yace “shikenan momy zata samo masa wani” tace “momy ki tashi ki dauko masa yanzu kinji” ganin rigimar tata yawane da ita yasa momy ta mike ta shiga dakin yaran zuwa can sai gata da takalman a leda ai kuwa amira ta dire daga kan cinyar dady ta karbi ledar tana cewa momy kawo na gani” tana karba ta daga ledar ta zazzage takalman, takalmane guda uku masu kyau amma amira ta tsugunna ta fara dubawa sai dago wani tayi tace “momy banda wannan ya lalace” momy da ta zauna kusa da dady tace “kawo mu gani” ta karba ta duba dan tashi kawai ledar ta farayi tace “haba amira kinga fa bai tsinkeba” amma sai amira tace “momy ya tsufa ki sake masa wani” momy ta fara zuciya kuma dan haka tace ”amira zan mareki kuma” tanajin haka tayi baya ta bada distance din da tasan hannun momyn bazaiyi saurin samuntaba sannan ta fara bubbuga kafa a kasa tana cewa “dady kace momy ta canza banason wannan” hannu dady ya mika mata yace “zo zo nan kinji uwata zo kiji muyi wata Magana” dan hawayen daya fara zubowa ta gofe sannan ta kama hannun dady daya miko mata ta haye kan cinyarsa yace cikin muryar lallashi “kinsan yadda za’ayi yanzu kikai masa wannan gobe idan na fita sai na siyo masa sabo ko” ta daga kai sannan ya kuma goge mata hawayen idonta yace “maza jeki kai masa wannan” ta karba takaiwa su Abdulrahman dake zaune suna zare ido kamar marasa gaskiya suna sakawa a zuciyarsu lallai wasu dai sunyi dacen iyaye na gari yanzu da ce babansu yana musu koda kwatancen son da wadannan iyayen ke yiwa 'yayan sune aida basu da wata matsala a rayuwa shikenan sun gama dacewa, karba sukayi suna ta godiya sannan momy tace su kawo kwanansu ta zuba musu abinci dan haka suka koma makaranta suka dauko kwanan nasu suka kawo ta cika musu shi da abinci sukayi ta godiya sannan suka tafi  amira har waje ta rakosu tana daga musu hannu tace “byebye yaya Abdulrahman sai gobe zanzo makarantarku da yaya umar” shima ya daga mata hannu yana murmushi.

Washe gari da safe suna tashi suka tarar Abdulrahim ya samo musu abinci da yawa kuma da alama yanzu aka saukeshi danda zafinsa, sunyi mamakin inda ya samu sai yake ce musu tashi yayi da wuri yaji yanajin yunwa shine ya fita bara aka bashi, basuyi masa musu ba suka zauna suka kwashi girki suka koshi sannan Abdulrahman yace “ku tashi kafin muje kasuwa mu samo bokiti muyi wanka” da mamaki duk suka kalleshi bello yace “wanka kuma?” Abdulrahman yace “eh wanka” dariya Abdulrahim ya fara tare da sakalo wuyan bello yana cewa “wai kasan me yasa yakeso muyi wanka? Saboda wannan yarinyar ta jiya tace baya wanka, yanaso ya burgeta to yau babu makaranta ba haduwa zakuyiba” gaba daya suka kwashe masa da dariya, Abdulrahman ya hade rai yace "eh din naji dan Amira tace bana wanka zanyi amma ku dan Allah bakuji kunyaba da tace bamayin wanka? Amira yarinyace yar karama amma harta fahimci bama wanka sannan kai Abdulrahim ka tuna sanda inna tana raye sanda muke kauyema kullum sai munyi wanka da zafi ma sau biyu take sakamu muyi wankan shikenan dan ta mutu sai mu daina wanka mu daina wanki?” mikewa Abdulrahim yayi yana cire riga yace “shikenan mike muje muyi wanka idan yaso wannan yayan na amira idan ya ganka ya kalleka a matsayin d'a saboda kayi wanka” mikewa shima Abdulrahman din yayi yace “koda bai kalleni a matsayin d'a ba wasu zasu kalleni a matsayin d'a koda kuwa banyi wankaba” shima bellon da aka bari a zaune ya yunkura ya mike yana cewa “dalla malam karka yaudari kanka dan jiya ka shiga gidan yan gayu har an baka abinci da takalmi hakan baya nufin ka zama dan gayun da har mutane zasu kalleka a matsayin d'a kai almajirine ko me zaka zama koda zaka zama shugaban kasa dole kai almajirine” yana gama fadin haka yayi waje abdulrahim ma yayi masa wani kallo irin abin tausayi dinnan sannan shima yabi bayan bello, jiki a sanyaye Abdulrahman ma yabi bayansu.

Da kyar suka sami bokiti sukaje suka debo ruwa sun dawo a hanya sukaga wani mutum yana sadakar goma goma suma sukaje suka karba sai Abdulrahim yace “kun san yadda za’ayi kamata yayi mu sayi omo da wannan kudin sai muyi wankan dashi zaifi akan ace muyi wanka haka da ruwa kawai” suka kuwa yadda da shawarar tasa sukaje suka sayi omo sannan suka raba sukayi wanka dashi suka shirya suka tafi kasuwa kamar kullum.

Yanzu kullum Abdulrahim ne yake samo musu abinci yawanci kafin su tashi zasuganshi da abincin idan kuma ana karatun safe sai suna karatu sai su nemeshi su rasa sai dai su ganshi da abinci kuma yaki gaya musu a inda yake samowa, sannan yanzu kullum sai sunyi wanka koda kuwa da ruwane kawai sannan duk sati sai sunyi wanki dan haka yanzu idan ka kallesu zaka ga sunyi kyan gani sosai.

Sun damu da son sanin inda Abdulrahim ke samo abinci dan haka wata rana suka tsareshi da tambayar inda yake samowa sai ce musu yayi wata matace take bashi sadaka, Abdulrahman yace “kuma ita matar kai kadai take bawa da kullum kai kadai kake zuwa ka karbo? Inda da gaske kake muje tare ko kuje da bello mana” yana wasa da kasar wajen da suke zaune alamar bai damuba yace “bani kadai take bawaba muna da yawa kuma sadaka takeyi sai da nace mata zamu dinga zuwa tare sai tace ai tasanku shiyasa take zuba mana da yawa yadda zai ishemu basai kunzoba saboda batason almajirai da yawa susan tanayin sadakar dan idan aka yi yawa bazai dinga isarmuba” kallon tuhuma Abdulrahman ya tsaya yana yi masa ganin yaki kallonsa yace “Abdul karya kake” shi kuma ya wani zuciya irin yayi fushi dinnan yace yana mikewa tsaye “shikenan tunda baka yadda daniba kayi yadda kakeso idan zanje ka bini a baya kaga inda nake zuwa tunda baka yaddaba” Abdulrahman yace “da nasan sanda kake tafiya ai bazan tsaya tambayarkaba bin naka zanyi indai da gaske kake gobe idan zakaje ka yi min magana mu tafi tare” Abdulrahim ya bude baki kamar zaiyi magana sai kuma ya maidashi ya rufe ya juya yabar wajen.

................
Wash yau nayi dogon episode ko? Saboda ina yinkune ina kuma jin dadin comments dinku idan kuka kara nima sai naji dadi na kara.

Kuna ta tambaya akan Khadija almajiri ma da ne ba labarin Khadija bane dan haka ba yanzu zakuji labarintaba sai nan gaba.
Na gode

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora