Nine years back
Da iya kacin karfinta take ihu ita dai ba hankaline da ita da zata fahimci abinda ke faruwaba abinda ta sani kawai shine wani babban tashin hankaline yake tunkaro rayuwarta, Abdul da Abdul sun tafi sun barta batasan ina baba zai kaisuba me yasa ake riketa bayan duk inda zasuje tare suke zuwa? Dan Allah a cikata tabi su Abdul bataso su tafi su barta.
Haka Khadija tayi ta kuka tun safen da aka daukesu Abdul har azahar babu wanda ya rarrasheta sai ma bintu da ta mayar da ita ganga duk wucewar da zatayi sai ta tillika mata dundu wannan yake kara karfin kukan nata, babu wanda ya kalli Khadija ya miko mata abinci babu wanda ya rarrasheta haka har bacci ya dauketa a wajen cikin kasa kudaje na binta kamar danyen nama amma babu wanda ya tasheta daga wajen ko ya lullubeta har la'asar.
Wata wawuyar yunwace ta tasheta ta tashi tana mutstsika idanu ga uban fitsari da tayi jagaf da jikinta, a lokacin ma ta manta wai an dauke su Abdul, ta zata ko aikensu akayi yanzu sun dawo dan haka ta mike tayi dakinsu tana tafe tana diga, tana zuwa ta daga dan labulen dakin tana kira "Abul yunwa ji ni eh" haka tayi ta leke leke a dakin tana kiransu "abul yunwa ji ni eh abul yunwa ji ni eh" haka har ta gaji ta fito ta tafi soro nanma basanan ta dawo bandaki zuwa yanzu ta fara kuka sosai dan ta fahimci basanan, can cikin dutsunan bayan gidansu inda suke guduwa idan gidan yayi musu zafi can ta tafi nan ma basanan dan haka ta juyo ta dawo gida.
Tana shigowa idanta a rufe tana kuka sukayi karo da bintu da ta taho da sauri zata fita waje, Khadija ta fadi kasa amma maimakon bintu ta dagata sai kawai ta rufeta da duka "shegiya bakya ganine zakizo ki shafamin fitsari? Yar iska mai suffar aljanu sai na kasheki idan bakiyi wasaba dama yanzu babu Abdulrahim din da zai tare miki da wasu kwala kwalan idonki kamar na aljanu" kuka sosai Khadija takeyi tana kiran "Abul banta duka ni eh abul" marinta bintu ta kuma yi tace "dan ubanki ba sunana bantu ba bintu nake" haka ta fice tabar yarinyar tana kuka da tayi mai yinta ta mike tayi cikin gida tana cewa "ni gaya abul ramani eh" sai dai abinda Khadija bata saniba babu Abdul din da zata gayawa ya rama matan Abdul yayi mata nisa ba zata iya kamoshiba.
Babu irin neman da Khadija bata yiwa su Abdul ba amma babusu babu labarinsu ga yunwa na kwarzabarta dole ta tafi dakin jaru tana shiga jaru tace "ke! Menene haka zaki shigomin daki jiki duk fitsari? Uban me zan miki?" Khadija na hadiyar zuciya tace "inna yunwa ji ni eh" jaru ta yamutsa fuska tace "me? Nifa kinsan ba gane wannan yaran naki nakeba me kikace?" Khadija ta kuma cewa "yunwa ji ni eh" shiru jaru tayi sai can tace "yunwa kikeji?" Yarinyar ta daga kai jaru ta kwaso wata uwar shewa tace "ahayye dadi kasheni wuya tai kuka wa yaga bada bada?" Ta kuma kwashewa da wata dariyar sai da tayi mai isarta sannan tace "to sai dai kiyi hakuri su sale sun cinye sai an sauke tuwo tukunna" Khadija bata gama fahimtar abinda jaru tace ba sai ta cigaba da tsaiwa a kofar dakin, jaru da ta cigaba da harkarta ta juyo ta kalleta sannan ta doka mata tsawa "dallah malama ficemin daga daki nace bani da abinci ya kikeso nayi ficemin kinzo kina min digar fitsari" ba shiri Khadija tayo waje tana fitowa ta shiga dakinsu ta kwanta kan yar yaloluwar katifarsu tana kuka a haka har wani baccin ya kuma dauketa.
Magriba Khadija ta kuma farkawa sakamakon sauron da ya daka mata wawa da kuma azababbiyar yunwar da takeji, ta fito tana bin bango ga wani kashi ta takeji a hankali ta wuce su jaru suna cin abinci ta dauko foo dinta ta hau tayi kashin sauro na ta cizonta ta fara kiran "abul gama ni eh" haka tayi ta maimaitawa har jaru ta gaji tace "ke zabiya babu wani Abdul a gidannan ki tashi kiyi tsarki da kanki kije kuma ki zubar" yarinyar ta tashi taje ta dauko buta dan ruwan ciki ba yawa haka ta jagwalgwala tsarkinta duwawun bai fitaba sannan ta bata hannunta, wajensu ta dawo tana kallon jaru tace "to meye kuma kike kallona?" Khadija tace "yunwa ji ni eh" sale dake cin tuwo a gefe yayi dariya yace "tab inna kin hadu da aiki nifa yarinyarnan idan tana magana banda eh da aa babu abinda nake ganewa" jaru tace "na hadu da aiki ko ita ta hadu da aiki? Nima ba ganewar nakeba ba kuma zan takura kaina nace sai na gane din ba" ta jawo wani kwankwatsatstsen kwano can gefe ta turowa yarinyar tace "gashinan kar a cinyemu"
Duk irin dagwalon nanne a cikin kwanon amma rashin wayo da kuma yunwar da yarinyar keji yasa bata ko kulaba ta tasa abinta a gaba hannu baka hannu kwarya ta cinye tas ko koshima batayiba amma tunda daman can bata saba akaraba sai batayi gigin cewa a kara din ba.
VOCÊ ESTÁ LENDO
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Ficção AdolescenteLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
