Chapter 37

67 8 5
                                        

"do you know why i don't like you nigerians? It's because you underestimate the power of your intelligence you believe that only white people can make miracles only white men can do this only white men can solve that you never gave your students a chance, for instance now you left him in your country in your state.. Wait from which state are you?" eng bakura ya dan muskuta a cikin kujerarsa yace "kano state sir" mr john ya cigaba da fadansa "you see he is there in your country in your state unemployed and you are here looking for a white genius" eng bakura ya ce "we are really sorry mr john but how can i contact him like i said earlier this is urgent" mr john ya dauko yar paper yayi rubutu a jiki sannan ya miko masa yace "here this is his email address we communicate only through email you can send him a message his name is Bello Mukhtar find him he is more than capable" eng bakura ya mike tsaye shima mr john ya mike sannan sukayi hannu eng bakura yace "thank you so much mr John" mr john yace "it's my pleasure he was one of my favorite student send him my regards" eng bakura yayi murmushi yace "i will" sannan ya juyo ya fito daga office din, yana shiga motarsa ya dau wayarsa yayi kira bugu biyu aka dauka "eng ina fatan kaje" eng bakura yace "tabbas naje yanzu haka ma ina cikin makarantar but Mr John yayimin suggesting wani daban wani student dinsune da ya gama last five years dan nan kanone sunansa bello mukhtar" daga daya bangaren akace "eng dan nigeria kuma? Kana ganin zai iya?" eng bakura yace "ban ganshiba amma a yadda mr john ke kambabashi nasan zai iya yace he is more than capable" wancan yace "to yanzu da yaya zamu sameshi?" eng bakura ya dago paper din da mr john ya bashi yana kalla yace "ga email address dinsa sai dai ka nemeshi bari na turo maka" wancan yace "ok it will not hurt to try turomin number din" eng bakura yace "right away sir" sannan suka katse wayar a take ya kwafe address din ya tura masa sannan ya tayar da motarsa ya doshi get din fita daga Stanford University.

...........
Abdulrahim na fitowa ya zauna kan kujera ya tallafe hannayensa kan kwuiwar kafarsa ya sunkuyar da kai, a hankali hawaye ya fara taruwa a idonsa sannan ya fara diga a kasa kan kafet din wajen, Abdulrahman ya biyo bayansa Khadija na bin bayansu suna fitowa suka hangoshi kan kujera nan sukaje suka sakashi a tsakiya, Khadija ta dafa kafadarsa a hankali tace "yaya Abdul..." bai bari ta karasaba ya dago da sauri rungumeta tare da sakin wani irin kuka mai ban tausayi, gaba daya jikinsu ya kuma mutuwa a hankali ta saka hannu itama ta rungumeshi tana dan dukan bayansa alamar rarrashi shi kuma ya fara magana "what have i done? What have done Khadija gaba daya rayuwata na kareta cike da tsanar mahaifina na kareta cike da shirin daukan fansa a kan mahaifina na kare rayuwata babu abinda na tsana kamar mahaifina, Khadija har kiran kaina nayi da shege saboda kawai kar a hada sunana dana mahaifina babu irin maganganun da ban gaya masaba har alkawari nayi sai na kashe mahaifina ashe duk ba laifinsa bane ba shine mai laifinba, Khadija wacce irin banzar rayuwa nayi? Na karar da rayuwata kin wanda ya kamata da ace shi nafi so sama da kowa, nazo nan ina rayuwa naki zuwa gareku saboda tsanar da nayi masa burina kawai nayi karfin da ina zuwa daukoki zanyi yadda bazan kuma komawa ba bazan kuma ganinsaba saboda bana bukatar na wani abu ya sake hadani dashi ashe ba laifinsa bane" dole yayi shiru saboda kukan dayaci karfinsa jikinsa har karkarwa yakeyi sai da Abdulrahman yaga suna shirin faduwa daga shi har khadijan sannan yayi kneel down a gabansu shima ya hadasu gaba daya ya rungume shima yana kukan tare dasu.
Sun dade a haka kafin Abdulrahman ya sakesu ya dago Abdulrahim yana goge masa hawayen fuskarsa yace "Abdul ka daina kuka ba laifinka bane kamar yadda ba laifinsa bane kaima ba laifinka bane iya kacin abinda ka sani kenan, a wajenmu shi mai laifine har zuwa wayewar garin yau yanzu mukasan asalin abinda ya faru dan haka ba laifinka bane ka daina wannan kukan please" Abdulrahim ya dago yana kallonsa yace "Abdul duk da haka kai me yasa bakayi abubuwan da nayiba? Kai me yasa bakayiba ai duk laifi daya akayi mana amma kai bakayi haukan da nayiba ni bani da hankaline shiyasa bana tunani idan zanyi abu ka duba abinda nayi ranar da muka...." dif ya dauke wuta yana kallon Abdulrahman sai kuma ya zamo kasa ya kuma dora hannu aka yace "na shiga uku" Abdulrahman yayi sauri ya rike hannayensa daya dora aka yana kokarin saukesu kasa yace "Abdul please ka daina wannan abin wai meye haka" Abdulrahim yace "me kakeso nayi yanzu idan bance na shiga ukuba? Ka manta irin maganganun dana fada ranar da muka kaishi asibiti? Rayuwata bata da amfani ubangiji ma bazai yafeminba bansan me zanyiba yanzu" ya cigaba da kukan da yakeyi a hankali sukaga Mal Musa ya tsugunna a gaban Abdulrahim ba tare da duk sun kula da fitowarsaba ya saka hannu ya sauke hannun Abdulrahim shima hawaye na sauka a idonsa yace "Abdulrahim ka daina wannan kukan ba laifinka bane babu wanda za'ayiwa abinda nayi muku yace bai kullaci mahaifin nasaba, ko ni kaina sai da na kullaci kaina bana kuma jin zan taba yafewa kaina kubra bata cancanci abinda nayi mataba sadaukarwar da tayimin bata cancanci hakaba, ba asiri akayiminba ko menene dan haka ka daina kuka ban kullacekaba idanma ka sabamin na yafe maka tuntuni kuma tunda ni kayiwa laifi na yafe maka Allah ma ya yafe maka Abdul ya isa haka" a hankali ya jashi jikinsa ya rungume shi kuma ya cigaba da kuka yana sake bashi hakuri.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Mga kuwentong kahuhumalingan mo. Tumuklas ngayon