Chapter 46

37 10 1
                                    

Shirye shirye sun kankama sosai ta kowanne fanni, ginin su abdulrahman ya kankama duk ukun akeyi duk da cewa Bello ba yanzu zaiyi aurenba ko budurwa ma bashi da ita amma dai yace wallahi ba zasu taho su barshi acan gidanba shi kadai shima gudowa zaiyi, gidan su Aisha ma shiri sukeyi sosai dan antynta dake maiduguri ma kanwar cp tazo ta tafi da ita shima uncle Ahmad uncle dinta dake india har yazo gaba daya shi da iyalinsa yayi aure tuntuni da matarsa da yaransu biyu Fatima da Irfan.
Gidan dadyne kawai babu abinda akeyi dan da anty zulai ma tazo take cewa "yaya dama cewa nayi kaga bikinnan ba wani da yawa aka sakashiba ya kamata ace mun fara komai da wuri kar lokaci ya kure mana me da me kake ganin zamu fara yanzu" dady yace "zulaiha ai kune mata ku kukasan me ya kamata ayi sai dai kuyi magana da Mariya ko kuma su safiya(kannen momy) zaki tuntuba?" anty zulai ta kalli momy dake ta danna waya kamar ba da ita ake maganaba tace "anty Mariya bakice komaiba ko kun fara wasu shirye shiryene" momy bata dago kanta daga kan wayartaba tace "babu shirye shiryen da muka fara kuma ba zamu faraba dan babu wani aure da za'ayi tsakanin Amira da wannan almajirin" dady ya tsaya kawai yana kallonta can yace "Mariya menene matsalarkine da Abdulrahman? Me ya tabayi miki wanda yasa kika tsaneshi haka?" ta ajiye wayar ta gyara zamanta tana kallon dady sosai tace "ta yaya kake tsammanin zan dauki 'yata kwaya daya da Allah ya bani na bawa almajiri? Kuma almajirin ma nawa na gidana dana bashi sadakar abinci da gwanjon 'yayana?" dady yace "sai kuma ya zama menene aibun hakan? Dan yana almajiri har yanzu almajirinne? Dan kin bashi kwance har yanzu kwancen kike bashi? Dan yayi miki aikatau har yanzu aikatau din yake miki? Mariya ki dawo hayyacinki dama rannan Amiran ta gayamin wai tace miki ba zata iya rayuwa bashiba kikace wai Allah ya jikanta ai ba ita kadai kika haifaba ko? Saboda rashin hankali? Ku mata wani lokacin idan kukaki gaskiya sai tunaninku ya koma kamar na yara wallahi" anty zulai tace "to banda abinki anty Mariya da kike cewa kin bashi kwancen kayan yaranki kema dai kinsan yanzu sai dai ya bawa yaran naki kwance kuma what matters is abinda yake yanzu ko abinda zai iya zama nan gaba ba abinda ada ya taba zamaba beside almajirancin ai ba haramun bane" momy ta daga wa anty zulai hannu tace "kinga zulai karki nemi ki rainawa kanki hankali bana son gulma da kinibibi ke idan 'yar kice zaki bashine? Ko kuwa dan ke baki haifi 'ya macen kinsan wahalartaba?" anty zulai tace "Amira 'yatace ko da banyi nakudartaba sannan kema ba rawa kikayi Allah ya baki macenba ni kuma ba laifi nayi daya bani maza zallaba kuma wallahi da ace ina da macen kuma yazo yace yanaso babu abinda zai hanani na bashi as long as halinsa da asalinsa masu kyaune" dady ya daga musu hannu yace "kunga dan Allah banason rashin hankali mekenan? Amira dai yarinyatace kuma na bayar da ita banajin kuma kin isa kisani na maida musu kudinsu indai har ba wani genuine dalili kika kawo a kan yaron wanda addini ya yadda dashiba" momy tace "amma rannan fa haka suka hada kai suka yiwa Usman duka nan yayi ta jinya dana gaya maka ma ko shiga bakayi ka dubashiba yan dabane ko wannan ma bai isa dalilin da za'a hanashi 'yaba?" dady yace "ban yadda sun hadu sun dakeshiba koda ma sun dakeshin tabbas wani abu yayi musu mai girma tunda lokacin da suna yara duk abinda yayi musu ai basu taba dukan nasaba lokacin ma da basu da hankali kenan basu da aikinyi balle yanzu" momy ta kuta sai kuma ta mike tsaye tace "shikenan sai ka aurar da yarinyar na gani ba da izininaba idan kuma zakasa ta bijireminne to sai mu gani" ta sunkuci wayarta tayi daki a fusace, anty zulai ta kada kai to "too haka anty Mariyan ta koma?" dady yayi ajiyar zuciya yana kwanciya sosai jikin kujerar da yake zaune sannan yace "wallahi akan yaronnanne duk ta koma haka kuma duk laifin Usmanne shi yake zugata da su safiya ma sun zugata amma tunda yaron yayi kudi sai kuma suka koma bayansa amma na rasa shi Usman menene matsalarsa ita kuma akwai biyewa yara"
A ranar da Bello da ya dawo daga delta suka takurawa Abdulrahman sai da suka maida Khadija gida shi dama so yayi sai ya sakeyi mata echocardiogram ya tabbatar ta samu lafiya kafin ya sallameta shi kuma akwai interval din da ake dauka tsakani kafin a sake wani amma yanzu dole ya maidata gida.
Tana komawa gida kuma Bello yaje ya marairaicewa hajiyarsa akan ta lallaba su Abdulrahman din su bari ta tafi da Khadija Dubai a cewarsa idan aka fita da ita kasar waje ta dan huta zatafi warwarewa akan a gida da zasu barta ita kadai ko 'yar uwa mace ma babu, nan da nan kuwa hajiya ta karfi shawarar tasa dama kullum tana sha'awar idan taga uwa ta tasa yarta a gaba sun tafi kasashen duniya shopping sai taji inama itama tana da ita da sunje gashi dama tun dawoqar Bellon basu taba fita wata kasa tareba sai dai babura kawai.
Ba karamar drama kuwa akashaba kafin suka yadda da tafiyar tata Abdulrahman fadi yake "ni hajiya bawai banason taje bane kinga bata da lafiya cikin jirgin nake tsoro tunda bata taba hawaba zata iya tsorata idan zai tashi hakan kuma zai iya janyo mata relapse" Bello yace "karka damu Abdul tare zamuje bazan bari ta tsorataba" duk suka tsaya suna kallonsa har hajiyan dan dai ita basuyi dashi zai bisuba amma sai ta basar batace komaiba, Abdulrahim ya kalleshi yace "ha! Speaking of jin tsoro ka manta yadda kayi ranar da ka fara hawa jirgi? Hajiya kingansunan wannan ya rikeni ta nan wannan ya kankameni tanan kamar zasu yagani wai duk tsoro sukeji as if an gaya musu mutuwa ake in an shiga jirgin" Bello ya harareshi yace "karka rainawa kanka hankali yaushe naji tsoro?" Abdulrahim yace "kaidai ne kake neman ka rainawa kanka hankali" hajiya tana dariya tace "ohh Allah zasu fara ku dai kamar masu ganin hanjin juna indai kuka zauna sai kunyi fada" Abdulrahim yace "wallahi hajiya Abdulmalik dinne dan rainin wayo baya bani girma kwata kwata" Bello ya harareshi yace "kaifa bakasan asalin date of birth dinkaba maybe ma na girmeka" Abdulrahim ya bude baki zaiyi magana Abdulrahman yace "dan Allah ya isheku mu koma maganar gaskiya maganar tafiya da Khadija ko aa" a karshe dai suka yadda za'a tafi da ita wanda dama tunda aka sallameta daga asibiti ta dawo nan gidan prof saboda can din ba kowa bai kamata su barta a gida ita kadaiba.
Daganan kuwa Bello harkar visarta ya tafi nema suka fara cuku cukun tafiyar dama ko passport bata dashi dan haka ya maida hankali kan shirin tafiyar tasu shi kuma Abdulrahim nasa hankalin na kan harkar gininsu.
Bayan sun kammala komai ana saura kwana biyu su tafi lokacin biki saura sati shida Bello Abdulrahman da Abdulrahim sukaje wajen dady bayan sun gama gaisawa wannan karon Abdulrahim ne ya fara magana "dady dama zuwa mukai mu nemi wata alfarma a wajenka" dady yace "to ina jinku" Abdulrahim ya cigaba "dama dady akan shirye shiryen bikinnanne mukace ba sai kayi komaiba zamuyi a matsayinmu na 'yayanka yayyen Amira duk wani abu daya danganci abinda zata bukata abinda za'a saka mata a dakinta zuwa abinda za'a ci ko wani hall da za'a kama dady munaso a bar mana zamuyi komai" dady ya girgiza kai yace "haba Abdulrahim ban taba tsammanin zakuzo mun da wannan maganar ba kuma kunsan bazan yaddaba kuna cikin hidima ga gini ga biki baku da wani mataimaki sai Allah sannan ni kuma maimakon na taimaka muku a matsayin uba sai na kara muku wani nauyin? Bazai yiyuba beside Amira ita kadaice 'yata mace dan haka tunda aka haifeta nake da burin aurenta dan haka banajin zan bari ku kwacemin wannan damar" Bello yace "amma dady...." dady yace "bafa zan bari kuyi komaiba nima inaso nayiwa 'yata bajinta wannan damace da nake da ita kwaya daya ku barni na damata" duk sukayi shiru ba haka sukasoba sunso dady yabar musu komai a hannunsu tunda suna dashi bawai basu dashiba ga lefe ma ance an dauke musu su ginine kawai nasu sai sauran kananan hidimomi shi kuwa yanzu zaice zaiyi kayan daki yayi gara duk shi kadai, Abdulrahman yace "shikenan dady tunda kace haka dole zamuyi respecting abinda kake bukata amma idan kana ganin babu damuwa muma adan bamu wata damar daga ciki muma muji cewar a bikin kanwarmu munyi wani abu" dady yace "babu damar da zan baku kuma abubuwan dake gabanku sun isheku bankiba dai kananan bukatu nata wannan zaku iya daukewa amma banda abinda yake responsibility nane ban yaddaba" sunaji suna kallo haka aka tashi zaman da dokakkiyar gwuiwa dady ya kafa ya tsare ya hana komai tafiya.
Kamar yadda suka tsara ranar tafiya nayi Khadija Bello da hajiya suka daga sai Dubai da niyyar hado lefe, duk da a wajen Bello shifa da gaske hutu yakeson kai Khadija so yake ya cire mata duk wani tunani akan Usman da abinda ya shafeshi so yake ya tabbatar ta manta da wani waishi Usman yadda zaiji dadin kafa tasa gwamnatin, sai yanzu ya fahimci mistake din da yayi kamata yayi ya koyawa Khadija sonsa ko ta halin kaka bai kamata ya sadaukar da soyayyarsa ga wani waishi Usman ba da ace bai nace an barsu tareba tabbas da bata kusan rasa rayuwarta akansaba duk laifinsa, kamar yadda yayi alkawari kuwa bai bari taji tsoro lokacin da zasu tashiba tunda suka shiga jirgin yake mata surutu zai da aka gama boarding sai ya dauko katuwar earphone ya saka mata a kunne yace ta dinga bin wakar ko ta dinga lissafi daga 1-100  sai kuwa gashi kwata kwata bataji karar tashin jirginba har sai da suka daidaita a sama sannan ya cire mata ya kuma kama yi mata hira.
Amira ta cigaba da zuwa makarantarta kuma yanzu mostly idan ta dawo gidan anty zulai take tafiya haka da weekends ma saboda duk wani shiri da akewa amarya su halawa da dilka da sauransu anty zulaice keyi, ga wani malami da suke zuwa wajensa yana basu rubutu na tsari dan tabbas irinsu Abdulrahman sai da tsari idan ba hakaba sai wata banzar ta sihirceku ta koroki tana ganin mijinki das das ga yarinta ga kyau uwa uba ga kudi, dan haka ba dan karamin shiri akeyi mataba sannan kuma suna fita kasuwa zuwa yanzu babu abinda basu siyowa Amira wai na sunan kayan dakiba, komai kuma me kyau me quality saboda kamar yadda dady ya fada ita kadai suka dora ransu a kanta dagashi har kanwasa da mahaifiyarsu ita kadaice macen da zakuyi mata bajinta suma suji cewar sun aurar da 'ya, zuwa yanzu banda kayan daki da sauransu kayan da zata saka da bikinma hatta da pant da bra an gama siya komai sun shiryashi ba kuma tare da taimakon momyba ko da kuwa da shawarane tun daga waccen ranar ma anty zulai bata kuma tuntubartaba sometimes dai tana yiwa su anty safiya magana to da yake ma ba a garin sukeba suma dai suna nasu shirin acan.
Yan Dubai kuwa suna dira suka fara abinda ya kawosu kullum Bello yana tare dasu yana faman barkwanci yana sakasu dariya idan akaje siyan kayama sai ya gama shakiyancinsa tukunna kafin ya barsu su siyi abinda zasu siya, wata rana basu fitaba hajiya tace su huta amma maimakon su huta din kamar yadda tace sai ya dauki Khadijan suka tafi yawo a karshe suka yada zango wani ice cream parlor aka kawo musu menu ya kalleta tana ta faman dubawa yace "wanne zakisha?" kafada kawai ta daga sai kawai ya zabar mata da kansa, bayan an kawo musu ta zauna tana ta faman juya cokali cikin ice cream din ya kare mata kallo yace "love zai narke fa" Khadija ta dan yamutsa fuska tace "ai nace bazan kuma shan ice cream da sanyiba sai ya huce" Bello ya saka dariya yana tuna ranar da suka fara bata ice cream shi da Abdulrahim ta dinga ihu tana cewa kanta zai fashe, sai kuma dramatically ya juya ya kalli surrounding dinsu ya kuma kallonta sannan ya dan kwanto kan table din dake tsakaninsu harda rage murya yace "kinaso ayi miki dariya ne kinashan narkakken ice cream?" bata dai ce komaiba sai shima ya zama serious yace "come on love me ya faru?" ta girgiza kai hawaye na taruwa a idonta nan da nan hankalinsa ya tashi ya dawo kusa da ita yace "subhanallahi Khadija menene me ya sameki?" da sauri ta fara girgiza kai tana cewa "babu komai yaya Bello babu abinda akayimin" Bello ya kura mata ido yace "ko gida kikeson komawa?" ta girgiza kai sai kuma ta daga kai tana share hawayen ya danyi murmushi yace "haba Khadija dan kinyi missing din su Abdulrahman sai kuma ki kama kuka? Bakunayin wayaba? Haba love kawoki kasarnan fa nayi dan kiji dadinki idanma kina da wata damuwa ki manta da ita amma maimakon haka sai kuma ki sakawa kanki wata damuwar? Kinsan kuwa idan wani abu ya sameki sai Abdulrahman ya kusa kasheni? Please love ki saki ranki munkusa komawa insha Allah" ta karasa goge idonta sannan a hankali kamar mai rada tace "me yasa kake cemin love?" ya dan hade gira yana kallonta yace "me?" ta dago idonta ta sakashi cikin nasa ta maimaita "me yasa kakecemin love?"
Wani mugun faduwa yaji gabansa yayi yadda take kallonsa cikin ido ya kamara in ina "amm... Dama ai kinga.. Come on Khadija tun yaushe nake fada miki hakan?" tace "eh dalilin da yasa tuntuni kake fadadin  nakeson ji" yace "Abdulrahim ma ba sweetie yake ce mikiba shi me yasa baki tambayeshiba?" ta tsaya kawai tana kallonsa sai kuma ta dauke ta maidashi kan wasu couple a gefensu, Bello yayi ajiyar zuciya yace "fine ina kiranki da love ne because you are the love of my life Khadija tun ranar dana fara ganinki tun daren da kuka shigo ke da Abdulrahim da Abdulrahman na fito ina tsokanarki da dije wallahi tun a lokacin nasan you are the one tun a lokacin nasan my life will never be the same ame again bansan yadda zan cigaba da rayuwa babukeba ni kaina bansan irin son da nake miki Khadija" ta sake goge hawayen dake bin idonta kamar an kunna fanfo murya a dashe tace "amma me yasa baka hanani soyayya da yaya Usman ba? Me yasa ka goyamin baya?" Bello yace "saboda kince zakiyi farin ciki idan aka barki dashi kince kina sonsa ni kuma babban burina shine kiyi farin ciki koda kuwa hakan na nufin ba tare da ni bane koda hakan na nufin ni zan kare tawa rayuwar da bakin ciki koma worse na rasa raina all i ever want is for you to be happy" Khadija ta saka hannu ta rufe fuskarta ta cigaba da kukanta zuwa yanzu gaba daya ice cream din nasu ya gama narkewa amma babu wanda ya damu a cikinsu sun ma manta da wani batun ice cream.
Bello ya kuma matsawa kusa yace "please Khadija ki daina kukannan kinsan kuwa yadda nakejin kukannan naki? Burina ki daina banason wani abu ya sameki kinsan halin da kike ciki" ta bude fuskarta tare da share hawayen duk da tana sharewa wani na zubowa tace "ai bada glass akayiniba balle na fashe komai nayi kuce kinsan halin da kike ciki eh na sani nafi kowa sani dan nace inasonsa dan nace zanyi farin ciki dashi shikenan sai ka kyaleni bayan kasan halinsa? Sai ka sadaukar da soyayyarka bayan kasan ba farin cikin zan samuba? Shikenan kai ba zakayi fada ka kwaci soyayyarkaba sai sadaukarwa ka iya?" Bello ji yakeyi kamar ya dora hannu aka ya zunduma ihu me yasa komai yake neman kwabe masane? ya kuma marairaice murya ya dauko tissue din dake kan table din ya mika mata yana cewa "I'm sorry Khadija please ki daina wannan kukan na karbi laifina I'm sorry ok?ungo goge hawayenki mutane na kallonmu" ta ture hannunsa mai tissue din ta tashi ta nufi hanyar fita daga shagon, har ya mike ya bita da sauri sai ya tuna bai biya kudin ice cream dinba ya koma da gudu ya biya sannan ya biyo bayanta amma sama ko kasa ya nemeta ya rasa, babu irin neman da bai mataba duk wani waje da yasan zata iya buya a dan tsukun ya duba babu ita kawai ya tsaya ya dora hannu aka baimasan abinda zaiyiba.
Yana tsaye yana kallon mutane kowa na harkar gabansa wayarsa ta fara kara yana dubawa hajiyace ya shiga uku yasan cewa zatayi su dawo gida dan magriba ta kawo kai shi yanzu ina zai nemo Khadija? Me zai cewa hajiya? Karma a fara tunanin abinda zai gayawa yan uwanta dan bashi dashi, da kyar ya daure ya dau wayar kafin ma yayi magana hajiya ta fara fada "Abdulmalik ashe baka da hankali ban saniba? Wannan wanne irin haukane da magribannan zata turo Khadija ita kadai? Da ta bata ko wani abun ya sameta fa? Ko kuma ta kasa gane hotel din da ya zakayi? Kasan ba sabawa tayi da irin wadannan kasashenba idan ma tana bukatar taimako da yaya zatayi bayani? Kai me kakeyi da bazaka kawota da kankaba?" baki kawai Bello ya saki sai da hajiya ta sake cewa "wai Abdulmalik kana jina kuwa?" da sauri ya danyi gyaran murya yace "hajiya Khadija tana nan wajenki ta dawo hotel wajenki?" tace "eh gatanan maganar da nake maka kenan me yasa ka barta ta taho ita kadai?" bai san sanda ya zube a wajenba dan kafafunsa ba zasu daukeshiba wani irin relief kawai sai ya kama dariya.
Bayan ya dawo da daddare ya shiga dakinsu zasuci abinci tunda suka zauna ake kallon kallo tsakanin Bello da Khadija babu wanda ya yiwa wani magana hajiya ta ajiye cokalin hannunta ta kalli wannan ta kalli wannan sanna tace "fada kukayi dazu ko?" a tare sukace "a'a" da sauri ita kuma ta sake hade rai tace "to wannan kallon kallon na magani da menene? Ke dama dazu da kika shigo naga alamar kuka kikayi me yayi miki? Ko tsoro kikaji?" Khadija ta girgiza kai tace "aa" hajiya ta sake kallonsu Bello har wani sunkuy da kai yake kamar yana gaban surukai tace "kwaji dashi gulmammu" sannan ta dau cokalinta ta cigaba da cin abincinta ta manta dasu.
Bayan sun gama cin abincin hajiya ta shiga wanka shi kuma ya sake zama gaban Khadija kasan kujerar da take kai yace "love please I'm sorry wallahi i thought Usman ya sake halinsa i thought tunda yana sonki bawai kin fito daga kauye ko yayyenki almajirai bane ko ubane baki dashi bazai dau hakan a matsayin aibuba dan ni nasan irin son da nake miki wallahi ko menene aibunki bazai bari na ganiba na zata shima irin son da yake miki kenan shiyasa na bar masa please kiyi hakuri kinji bazan sakeba" ta dan langabar da kai tace "shikenan na yadda" yace "kin hakura?" ta daga kai yace "ban yaddaba" tace "Allah kuwan" yace "to yimin murmushi na gani" batasan sanda ta saka dariyaba tana rufe fuska, Bello yayi ajiyar zuciya sai kuma ya mike tsaye ya rike kugu da hannu daya dayan kuma ya dan dungure mata kai playfully yace "wanene yace dazu ki taho ki barni ki taho ke kadai? Kinsan kuwa zuciyata ta kusa bugawa da ban gankiba na zata wani abinne ya sameki? me yasa?" ta cigaba da kallonsa ta tsakanin yan yatsunta tana dariya yace "au dariya kikeyi ko? Bari kiga" sai ya fara waige waigen neman abin duka ita kuma ta cigaba da dariyarta, ya zaro charger din wayar hajiya yana nadawa yace "ina miki magana ma kinamin dariya ko?" yadda yayi babu wanda zaice ba dukanta zaiyiba sai ga hajiya ta fito daga toilet ta tsaya tana kallonsa tace "kai menene haka?" da gudu Khadija ta tashi ta shige bayanta tana cigaba da dariya Bello ya harareta yace "hajiya fada nake mata takemin dariya" hajiya ta kamo hannun Khadija suka dawo kan kujera tace "ashe ba dadi dazu da nake maka fada nima ka sakamin dariya?".


..........................
Hi angels
Jiya na gama typing sai cajina ya kare banyi muku posting ba da gaske nakeba da nace bazan posting.
Ilysm❤️

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Where stories live. Discover now