Bayan su Khadija sunci abincin dare sukayi kallo wani korean film my love from another star da yake Amira mayyar korean filmce sunayi tana fassarawa Khadija, basu suka tashiba sai da Abdulrahman ya kira Amira ta haye gado aka fara soyayya ita kuma Khadija ta cigaba da kallonta tana cikin kallon itama wayarta ta fara kara ta dauko wayar ta kurama screen din ido 'love' ita dai bata taba ganin wannan sunan a wayartaba ita har tana saurima ta zata yaya Bellone dan tunda ya tafi basuyi wayaba idan ta kirashi bata samun wayar wai wajen da yake babu network, har wayar ta katse bata daukaba aka kuma kira shima ta tsaya tana kallonta sai da Amira ta dago kai tace "wai ba kiranki akeyiba?" Khadija tace "anty Amira bansan number dinba" tace "to ki dauka sai ki tambayi waye amma a haka ai ba zakisan wayeba" hannunta har rawa yake tayi sliding screen din sannan ta saka wayar a kunnenta tare da cewa "assalamu alaikum" daga daya barin akace "amen wa alaiki assalam khadijatul kubra" tace "ina wuni" ya amsa da "lafiya kalau kinje gida lafiya?" tace "lafiya kalau ban gane mai maganaba" ya danyi dariya "yanzu baki gane muryataba? Ni kuwa kinga ko a bacci na farka zan gane muryarki" Khadija tace "yi hakuri ban ganeba wallahi" da sauri yace "noo ba laifi kikayiba Usman ne" sai kuma ta washe fuska kamar yana ganinta tace "lahh yaya Usman yi hakuri ban ganekaba" Usman yace "baki damu dani bane shiyasa, da har ina fargaba na zata kinyi bacci kar na tashi sarauniya" ta danyi dariya tace "aa banyi bacciba kallo ma nakeyi" yace "wanne film kike kalla" Khadija ta dan yamutsa fuska kawai sai taji tana kunyar ya gane batayi karatuba ta fara musmus da baki yace "ko ba'a fadar sunansa?" da sauri tace "eh sirrine" ya fara dariya yace "to ke dawa kuke kallon film din sirrin" innocently tace "ni da anty Amira" yace "Amira kuma?" Khadija tace "eh ai ban tafi gidaba anan zan kwana" Usman yace "wow kice yau a gida daya zamu kwana haba no wonder naji wata nutsuwa ashe kina kusa danine" ita dai tayi dariya bata bashi amsaba dan batasan amsar da zata bayarba ya cigaba "tunda kikace da Amira ma kike kallon nasan bazai wuce wadannan masu kananan idonba irin nata" Khadija tace "lahhh ai kuwa idon anty Amira manyane masu kyau" Usman yace "amma basu kai naki kyau ba" haka sukayi ta hirarsu har su Amira suka fara sallama wajen 1am tana juyi kawai taga Khadija na waya batasan sanda tace "kai Khadija wai har hanzu wayar kikeyi? Ke dawa" kafin ta bata amsa Abdulrahman yace "wacce khadijan ce ke waya yanzu" Amira tace "wacce Khadija kuwa ka sani?" a zuciye ya mike zaune daga kwanciyar da yayi yace "ita da uban waye suke wayar" Amira ta daga kafada kamar yana kallonta tace "Allah masani maybe yaya Bellone" Abdulrahman yace "inda Bello yake babu network bata wayar" Amira ta mika mata wayar tace "ungu yaya Abdulrahman" Khadija tacewa Usman "yaya Abdulrahman na min magana bari na dauka" yace "ok ba matsala ina jiranki" yayi tsammanin zata kashe ko tasashi a hold tunda yayi tsammanin da wayartane zatayi wayar har yana mita "mostly annoying mutane sunansu Abdulrahman i don't know why" ita kuwa Khadija tana karba tace "hello yaya..." bai bari ta karasaba yace "ke dawa kike waya a darennan" ta fara in-ina ya doka mata tsawa "magana nake miki ke da ubanwa kike waya a darennan? Wa kika sani da har kukayi exchanged na number zai fara kiranki da daddare? Dama abinda kikeyi da wayar kenan? Kin san kuwa halin samarin garinnan?" muryarta na rawa tace "yaya gani nayi fa anty Amira ma tanayi" ya kuma har zuka yace "karki rainawa kanki hankali Khadija duk abinda Amira tayi shi zakiyi? Shekarunku daya? A waje daya kuka taso ko cikin mutane iri daya kuka taso? Bayan wannan ma ita Amira dani take waya tun tana yarinya na santa idan da zan lalata mata rayuwa da tuni wani zancen akeyi yanzu amma ke kuma fa yaushe kika shigo garinnan barantana har ki gayan wani Amira kikagani tanayi? Ranki zai mugun baci wallahi idan na kuma kamaki da irin wannan laifin ki kashe wayar yanzu ki kwanta ko ma waye na gaya miki" kai kawai ta daga hawaye na zuba a idonta idan akwai abinda ta tsana tsawace ko sanda tana gida ta gwammace mutum ya daketa da yayi mata tsawa hargitsata takeyi gaba daya, hannu na rawa ta mikawa Amira wayarta sannan ta kashe tata ba tare da ta kuma yiwa Usman wani bayaniba gado kawai ta haye taja abin lulliba ta rufe fuskarta ta kama kuka.
Bayan su Amira sunyi sallama ta shiga toilet har ta fito Khadija na kuka, sai data gama shirin kwanciyarta sannan ta zauna bakin gadon tace "Khadija kuka kikeyi?" shiru bata bata amsaba Amira ta cigaba "Khadija ba zaki ganeba yaya Abdulrahman sonki yakeyi shiyasa yayi miki fadan wayar da kikayi kuma da ace ansan dawa kikeyi an yadda dashi da sauki amma wallahi Khadija da zakiji abinda akeyi da waya wallahi sai kinji tsoron riketa gaba daya kiyi hakuri ki daina kukan haka kinji?" Khadija ta bude fuskarta idonta har yayi ja tace "yaya Usman ne fa ba wani bane yaya Abdulrahman yaki ma ya bari nayi masa bayani kuma ni ba kuka nake dan yayimin fadaba kuka nakeyi saboda na bata masa rai alhali shi kullum burinsa ya farantamin" Amira tace "Usman kuma? Na gidannan?" Khadija ta daga kai Amira tace "dama kuna wayane wait yaushe ma kuka fara magana dashi har kuke waya?" nan Khadija ta kwashe duk yadda sukayi tun farkon haduwarsu ta gayawa Amira, ba karamin mamaki Amira tayiba tace "tab amma me yasa baki gayaminba tun farko?" Khadija ta yi tsuru tana kallon Amira tace "da matsalane?" Amira tayi saurin cewa "aa ba wata matsala kawai nayi mamakin da bansan komai akan abin bane ki kula dai kawai yanzu ki kwanta kiyi bacci dare yayi sai da safe" Khadija ta kada kai kawai sannan ta lumshe ido sauran hawayen dake idonta ya karasa zubowa ta cigaba da ajiyar zuciya har bacci ya dauketa.
Washe gari sai can yamma sannan Abdulrahman yazo ya dauki Khadija tunda yazo take faman buya a bayan Amira shi kuwa yayi kamar baisan ma abinda takeyiba ya cigaba da janta kamar yadda ya saba. Daga ranar Khadija bata kuma yin waya da daddareba tana ganin anyi isha to ba zata kuma daukan wayar kowaba indai ba yayyen nataba duk da dama sune masu kiran.
Tunda Bello ya tafi lagos bai sami yin waya dasu Khadija ba sai daya kwana takwas shima suna cikin magana network din ya kuma daukewa daganan basu kuma maganaba sai ranar daya shigo lagos din tukunna, Abdulrahim kuwa kullum ne sai sunyi video call dashi yawanci ma hirar daren da sukeyi dakin baba shima sai anyi dashi computer zasu saka su kirashi ko shi ya kirasu suyi ta hirarsu har baban, Amira ta fara shawarar komawa makaranta tanaso ta karo karatu amma yanzu pediatric takeson komawa, ita kuwa Khadija malami Abdulrahman ya dauko mata tunda babu Bello babu Abdulrahim shi kuma ba lokacine dashiba balle ya dinga koya mata, nan da nan sai ga Khadija kanta yana budewa ashe kaine da ita dandai ba'a bata damar karatun bane, dama kuma babu abinda takeyi shiyasa kullum tana cikin karatu shi kuma Abdulrahman sai ya koma kullum cikin siyo mata littafai irin comic dinnan da films na harkar education wadanda ake koyarwa a cikinsu yadda koda break ta dauka a karatun kallon da zatayi ko karatun da zatayin still dai kamar koyo takeyi.
Sai da Bello yayi wata hudu a lagos sannan ya dawo bayan ya kammala duk wani abu da shell suka daukeshi dan yayi musu,ba dan karamin alkhairi ya samoba wanda ko a mafarki bai taba tsammanin zai samuba ko NNPC din daya yake kulafuci da bayajin a shekaru goma zai samu abinda ya samu da shell a wata hudu sannan kuma ga babban aiki da suka bashi a cikin special agents dinsu wadanda zasu dingayin aiki a ko ina, ba karamar tsaraba yayiwa kanwarsaba, lokacin da ya dawo mainland yawo kawai yayi tayi duk abinda ya gani kayane ko jewelry kai hatta da teddies idan ya gani sai ya siyowa Khadija komai ya gani yace wannan zai yiwa Khadija kyau wannan Khadija zatasoshi, ranar da ya dawo ba karamin murna Khadija tayiba dan tayi missing dinsa sosai har da girki aka shirya masa akayi kwalliya shidai Abdulrahman sai dariya yakeyi mata, kuma ba laifin girkin nata yayi dadi sosai kamar ba 'yar koyoce tayiba.
Tunda Bello ya dawo ya fahimci bayan karatu kuma akwai abinda ya fara daukewa Khadija hankali, koyaushe tana cikin danna waya ko tanayin wayar yanzu har earpiece take sakawa idan zatayi waya saboda dadewar da takeyi idan kuma yayi mata magana sai tace wai ita ba waya takeyiba, hankalinsa ya fara tashi kardai ace soyayya takeyi dan shi kam tun ranar da tazo garin ya kallafa rai akanta irin love at first sight dinnan kuma ba karamin yado tayi cikin ransa a watanninnan ba babban burinshi shine yau ace Khadija ta zama tasa babban burinsa shine ya samu aiki ya aureta ta zama mallakinsa yadda zai kareta babu wanda zai kuma koda yi mata kallon banza balle ya daga hannu yace zai daketa ko ya zageta to yanzu ya samu aikin amma kamar wani yayi masa shigar sauri, duk da yaga hankalinta ya karkata kan wanda take wayar dashi dole zai jajirce shima don ya kwato soyayyarsa yana ganin babu wanda ya dace da kanwarsa sai shi ba kuma zai barwa kowaba.
Mataki na farko daya fara dauka shine hanata wayar da takeyi, indai yazo ya tarar tana waya sai yasan yadda yayi ya kwace wayar ya ajiye can gefe yadda ma ba zata kuma yiba, wani lokacin kuma sai yace wai ta bashi aron wayarta zaiyi amfani da ita haka zata hakura dole da wayar shi kuma yana zuwa daki zai kashe wayar ya jefar kan gado ya cigaba da harkarsa.
Bayan wannan kuma sai ya cigaba da kafa fadarsa a zuciyar khadijan bai fito ya gaya mata sonta yakeyiba amma fa ko makaho ya shafa yasan sonta yake wani lokacin ma idan suna zaune a gida idan Abdulrahman ya sakata abu sai Bellon yace "kinga zauna bari nayi masa kawai matarka na can tana hutawa kana saka matar mutane aiki" ko kuma idan tayi abu Abdulrahman ya harareta ko da kuwa hararar wasace sai yace "haba Abdul karka tsoratarmin ta ita mana" ire iren wadannan maganganun har Khadija ta saba dasu indai daga bakin Bellone.
Amira ta samu admission a BUK medicine ta koma karatu amma sun gama shiryawa Abdulrahim na dawowa zasu shigar da maganar aurensu Abdulrahim da Aisha da kuma Abdulrahman da Amira a lokacin ma sukayi tayiwa Bello dariya wai idan baiyi wasaba sai 'yayansu sun zo sun rakashi zance.
............
Na sani na yau yayi kadan amma kuyi hakuri yau i was busy da kyar nayi wannan dinma kuma bakwayin comment shiyasa.
Su waye sukeson Khadija da Usman su waye kuma keson Khadija da Bello?
Ni dai team..... 🚶🏽♀️🚶🏽♀️🚶🏽♀️
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
