Chapter 34

65 11 2
                                        

Su Khadija na zaune suna cin abinci Amira ta fito daga ganinta kasan kuka takeyi da sauri tayi hanyar fita daga gidan, Khadija ta mike tsaye tana cewa "anty amira? Ina zaki?" bata bata amsaba ta bude kofa ta fita tana fita Khadija ta ture kujerarta da niyyar binta Abdulrahim ya rike hannunta sannan ya girgiza mata kai alamar ta kyaleta dole ta nemi waje ta zauna duk ranta ba dadi batason a kuma samun wata matsalar a dalilinta a dalilin maganar da ta fada sannan kuma ta tura Abdul din wajen Amiran da niyya.

Sai can sannan Abdulrahman ya fito jikinsa ba wani kuzari yaja kujera ya zauna, Khadija tace "Yaya na zuba maka abincin?" Sai ya girgiza kai yace "barshi kawai na koshi" sannan ya tashi ya dauko lemo cikin fridge ya fara sha, kana kallonsa kasan tunani yake sam hankalinsa baya kansu, Khadija na kallo Zainab tayi ta kallonsa tana kokarin su hada ido amma sam hankalinsa baya kanta kansa na kasa.

Bayan sun gama cin abincin suka kuma dan taba hira kafin akayi kiran sallah sannan samarin suka fita masallaci su kuma yan matan suka shiga dakin Khadija suka yi sallah, bayan sun idar suna zaune Zainab tace "Khadija da gaske bikin Abdulrahman za'ayi" Khadija ta daga kai tace "da gaske me kikagani?" Zainab tace "kawai kuma auren soyayya zasuyi?" Khadija tace "sosai tun suna yara suke soyayya fa, dan sunce tun anty Amira na shekaru hudu suke tare kuma har yau, tun daga lokacin suke soyayya sosai har yanzu" Zainab tace "an saka rana?" Khadija tace "eh saura wata hudu watan maulidi za'ayi amma ba'a yanke rana ba tukunna" Zainab ta kada kai kawai hafsat dake gefe tace "ni kuwa idan na kalleki sai naga kamar ba Khadijan da kullum ake bani labari ba" Khadija tace "yaya Abdullahi na yawan maganata?" tace "sosai har sai da mukayi tsammanin gamo yayi da aljana a dajin ba mutum bace" Khadija tayi dariya tace "a dajinmu babu aljanu" hafsat tayi dariya tace "babu dajin da babu aljanu Khadija" Khadija tace "amma lokacin da yaje garinmu ba'ayi bikinkuba ko?" hafsat tace "ba'a dade da bikinmuba yanzunma ko shekara bamuyiba" suna cikin haka Abdulrahim yayi knocking kofar dakin suka amsa ya dan leko sannan yace "yana jiranku" suka mike Khadija ta basu kayan kwalliya suka dan gyara fuskarsu sannan suka fito, har kofar gida suka rakosu bayan sunyi exchange na numbers suka tafi Khadija tana ta faman daga musu hannu har suka fice daga get din asibitin.

Suna komawa gida Abdulrahim yace "Khadija akwai abinda zakiyi yanzu?" ta girgiza kai alamar aa' ya juya ya kalli Abdulrahman "Abdul kaifa" Abdulrahman yace "Amira nakeson na kira" yace "ok kuje kuyi wayarku idan kun gama please ka dan sauko zamuyi maganane" suka nemi waje suka zauna Abdulrahman ya daga waya ya kira Amira har ta gama ringing bata daukaba ya kuma kira kusan 5 missed calls amma bata daukaba dan haka ya ajiye wayar ya kalli Abdulrahim yace "taki dauka, me ya faru kace zamuyi magana" Abdulrahim yace "are you going to be ok?" Abdulrahman ya daga kai kawai Abdulrahim ya kalli Khadija sannan ya kalli Abdulrahman yace "tunda Khadija tazo bamu samu damar zama ta bamu labarin irin rayuwar da tayiba haka muma bamu bata labarin rayuwar da mukayiba kunga dazu da munsan me ya faru da ita da ba zamu kasa gane Dr Abdullahi ba da matsayinsa a rayuwarta, ina ganin ya kamata musan labarin juna ko ya kukagani?"

Khadija ta daga kai tace "eh gaskiyane ko yaya Abdul" Abdulrahman shima ya daga musu kai Abdulrahim yace "ka tabbata kana lafiya baka bukatar bin bayanta?" Abdulrahman ya daga kai yana kallonta yace "ba komai nasan tana lafiya na kira Aliyu yace taje gida lafiya kawai ban saniba ko ta daina kukan ko har yanzu tanayi" Abdulrahim yace "to kanaso mu bita?" Abdulrahman yayi shiru Khadija tace "gaskiyane ya kamata muje mu ga halin da take ciki tunda taki daukan wayar" Abdulrahim ya mike tare da daukan key din mota kan kitchen island yace "muje?" duk suka mike sukabi bayansa.

Suna zuwa gidan su Abdul suka zauna a mota Khadija kuma ta fita ta shiga, su dady suna zaune a falo dady na kallon news momy na hada masa abinci Khadija ta gaishesu sannan ta tambayi Amira momy tace "shiga tana dakinta bamatajin dadi tunda ta dawo daga aiki" Khadija ta shiga dakin da sauri ta tarar da Amira a kwance a kan gadonta idonta a rufe amma kuma kana ganinta kasan ba bacci takeba, Khadija ta zauna bakin gadon tace "anty Amira?" amira ta waigo ta kalleta sai kuma tayi sauri ta tashi zaune tace "Khadija? Yaushe kika shigo? Ke dawa kukazo a darennan?" Khadija tace "nidasu yaya Abdul ne me yasa baki dau wayarkiba yaya Abdul nata kira?" Amira ta sunkuyar da kanta tace "ba komai kawai bansan abinda zance masaba bansan kuma shi me zaiceminba zai iya cewa duk abinda ya fadamin dazu wasa yakeyi Zainab yake so Khadija zuciyata ba zata iya daukaba, yace tsoro yakeji amma baisan nafishi jin tsoronba, Khadija bazan iya rayuwaba idan babu yaya Abdulrahman ba ni nasani dan wallahi nasan idan ya gujeni zuciyata bugawa zatayi" Khadija ta kama hannunta tace "anty Amira ki kwantar da hankalinki ba zaki taba rasa yaya Abdulrahman ba na tabbatar miki yana mugun sonki ba wasa yakeba duk abinda ya fada miki dazu duk da bansan me ya fada dinba amma nasan tabbas yana mugun sonki, tunda kika taho ko zama ya kasa saboda damuwar halin da kike ciki har yaya Aliyu ya kira dan ya tabbatar kinzo gida amma duk da haka ya kasa kwantar da hankalinsa ki dau waya kiyi masa magana" Amira tayi shiru hawaye na zuba a idonta ta rasa abinda zatace,  Khadija tace "zan gaya masa kina lafiya idan ba zaki iyayi masa maganaba" Amira ta daga kanta kawai Khadija ta kuma cewa "to ki kwanta yanzu kiyi bacci ki daina kukan haka kar kizo kanki yana ciwo ko wani abun" Amira tayi mata murmushi sannan ta kwanta Khadija taja mata bargo ta lullubeta ta zauna kusa da ita a hankali Amira ta bude idonta tace "Khadija kije suna jiranki" Khadija tace "zan tafi amma sai kinyi bacci tukunna" Amira tayi murmushi tace "ni fa ba yarinya bace karki manta nama girmeki" Khadija tace "duk da haka sai kinyi bacci tukunna" dole Amira ta rufe idonta tana murmushi har baccin ya dauketa, sai da Khadija taji numfashin Amira ya fara sauka a hankali alamar tayi bacci sannan tayi murmushi ta tashi ta fito babu kowa yanzu a falon amma ta jiyo motsi a kitchen ta leka ta zata momyce zatayi mata sallama sai ta ga Usman yana suyar kwai da earpiece a kunnensa, ya juyo kenan ita kuma ta leka da sauri ya saki fuska yana cire earpieces din guda daya yace "wow what a surprise Khadija yaushe kikazo?" tace "tun dazu ina dakin anty Amira na zata momyce ma zanyi mata sallama zan wuce" ya ajiye plate din hannunsa ya dafe kirjinsa daidai zuciyarsa yace "ouch har naji zafi kina nufin da tafiya zakiyi ba zaki nemeni mu gaisaba?" tace "ayya ai naga dare yayine shiyasa" Usman yace "kawai dai baki damu dani bane shiyasa ni inanan ko bacci na kasa ina rufe ido zan ga fuskarki amma ke zakizo har gidannan ki kasa nemata" Khadija ta saki baki tana kallonsa cikin mamaki yace "ko baki yaddaba?" tace "to menene zai hanaka ka kasa bacci kai kuwa? Tab!" sai kuma ta daga masa hannu tana cewa "sai da safe ana jirana a waje" da sauri ya biyota gabansa yana faduwa badai saurayine ya kawota ba? Ya sha gabanta yace "ke dawaye wa yake jiranki?" tace "su yaya Abdulrahim ne dare yayi idan momy ta fito kace mata na tafi" da sauri ta zagayeshi tayi waje kafin ya gama fahimtar abinda ya faru ya biyo bayanta tuni motarsu ta tashi yace "shit yauma ban samu number din tata ba Usman you are such an idiot"
Ita kuwa Khadija na fitowa taga Abdulrahman sai gazaye yakeyi a waje tana fitowa yayo wajenta da sauri yana cewa "my God Khadija ina kika tsaya kin barni cikin tashin hankali na zata ma wani abunne ya faru" ta bude kofar mota ta shiga tana cewa "shiga muje babu abinda ya faru zan gaya maka a hanya" da sauri ya bude motar shima ya shiga suka kama hanya sai da sukayi nisa ya waigo yace "uhmm inajinki me tace" Khadija tace "tananan kalau sai da tayi bacci ma sannan na fito amma fa bata yadda kana sonkaba" yace "kamarya bata yaddaba?" Khadija tace "anty Amira tace bata yadda kana sontaba dan tace idan kana sonta tuntuni me yasa baka fadaba sai yanzu? Ni ina ganin kawai kayi duk yadda zaka yi ka tabbatar ka nuna mata da gaske kana sonta idan fa kana son nata kena?" yace "haba Khadija me kike fada? Wallahi Allah da ya sakamin sonta shi kadai yasan irin yawan son da nake mata kima daina kokwanto" Abdulrahim dake driving yace "wannan kuma kai ka jawowa kanka sai kayi fighting for her indai da gaske kanason nata" daga nan ba wanda ya kuma magana har suka koma gida suna zuwa kowa ya watse yayi dakinsa labarin da ba'ayi ba kenan.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Historias para obsesionarse. Descúbrelo ahora