A ranar da su Abdulrahman suke graduating sai ga prof bello hajiya dady da amira duk sunzo taya shi murna, ai kuwa yayi murnar sosai kamar bakinsa zai yage, Amira an kara girma itama ta kammala karatunta a school of nursing tanan kano dan haka sukayi ta tsokanarsu wai likitoci dan taga yana karatun likitane itama taje tayi da abdulrahim ya tasata a gaba da tsokana sai da tayi kuka sannan ya kyaleta, bayan an gama shagalin cikin makarantane kuma suka dau hanya sai new port inda suka kama wani guest inn anan bakin beach sukasha celebration dinsu, tun la'asar suke abu daya har dare iyayen da suka gaji sukayi tafiyarsu suka barsu abdulrahim da bello suka kunna kida sukayi ta dikar rawa su abdulrahman da Amira kuma suna gefe sunayi musu dariya.
Bayan jikin su bello yayi sanyi kuma sai suka baje wai a waje zasu kwana suka kwanta a cikin yashi su abdulrahman kuma suka tafi yawo, yashin beach din kawai sukayi tabi suna tafiya bayan sun cire takalmansu a wajen da su abdulrahim suke, suna tafiya iska tana kadasu karar crashing na waves na cika kunnuwansu, a hankali suke tafiya amira na ta kallon ocean din tana jin wani farin ciki yana shigarta wai yau itace a wannan wajen da bata taba tunanin zatazoba kuma duk sakamakon yayyenta wadanda bama su hada jiniba, su abdulne suka biya musu kudin jirgi ita da dady suka taho anso tahowa da momy taki yadda ita kanta da kyar momyn ta barta ta taho dandai da dadyne.
Waje suka samu suka zauna cikin yashin idan wave ta taho tana feso musu da ruwa, amira ta kalli abdulrahman wanda ya kurawa cikin ocean din ido tace "me kake tunani?" dan ajiyar zuciya yayi yace "khadija! duk lokacin da naje wani waje mai kyau ko naci abu mai dadi sai na tuna da ita sai naji inama tana tare dani ina ma tare muke jin wannan dadin" amira tayi masa murmushi tace "ka kwantar da hankalinka kun kusa haduwa da ita insha Allah daganan kuma ba zaku sake rabuwaba" shima yayi murmushi yace "insha Allah" amira tace "yaushe zakuje wajenta?" sai da ya danyi tunani sannan yace "bansaniba amma bazai kai nan da satiba insha Allah tunda kinga jibi zamu koma Nigeria da ason rainane ma ranar da muka koma washe gari zamu je to amma dai sai mun koma gidan tukunna abdul yace sai an shirya dakinta duk da duk wasu furniture an siya an turashi shiryawane kawai kayan sakawa kuma nace mu bari sai mun daukota dan bamusan size dintaba" amira ta kada kai zuwa can tace "to kuma idan kukaje kuka tarar anyi mata aurefa?" abdulrahman yayi shiru har sai da ta fara dana sanin abinda ta fada ko ya bata masa rai sannan yace "bansaniba bansan yadda zamuyiba amma abdul yace wai koma waye ya aureta yayi asara dan sai ya daukota" daganan duk sukai shiru ba wanda ya kuma magana da dan uwansa sai da zuciyoyinsu da sukeyi.
Sai da sukaga wajen yayi shiru sosai babu alamar mutane sannan abdulrahman yace "dare yayi tashi muje mu kwanta ko ma tashi gobe da wuri" amira ta mike tana duba agogon hannunta sai ta bude baki tana kallonsa yace "ya akai" tace "karfe biyu" murmushi kawai yayi yace "da nawa kike tsammani?" da sauri tayi gaba tana cewa "wallahi bansan dare yayi hakaba" sai da ya hada da dan gudu sannan ya taradda ita suka jera zuwa inda su abdulrahim suke sun baje kan carpet din suna ta shan baccinsu ya dala musu duka duk suka mike a firgice yace "sai ku tashi mu wuce ciki" abdulrahim yayi tsaki ya koma ya kwanta yace "karka dameni sai da ka gama shan soyayyarka zaka wanice mu tashi ni anan zan kwana" abdulrahman yace "kadai san iskar wajennan tayi maka yawa ko?" bello ya mike yana cewa "ni wallahi har hancina ya fara toshewa ciki zan koma" abdulrahman yace "dama ai gangancine kwanciya anan shark yazo ya hadiye mutum" abdulrahim yace "kula dai ba wannan yar kauyen bace balle ka tsoratani anan ne da shark din?" amira ta hade rai tace "wacece 'yar kauyen?" abdulrahim yace "wadda ta tsargu" ya juya ya cigaba da kwanciya ai kuwa ta tsugunna ta danki yashi ta watsa masa sannan tayi guests inn din da gudu ta barshi yana zazzage jiki bayan ya mike a tsorace.
Washe gari sai da sukayi sallar azahar sannan suka fita su abdul suka dauki amira sai Disney Park sune daga wannan ride su koma wannan, da suka gama da nan ma yawonsu suka tafi daga nan sai nan danma fans din abdulrahim na kawo musu cikas. Yauma basu koma gidaba sai dare washe gari suka koma California suka shiga store store amira tayi tsaraba sosai dukda dama sunyi mata da yawa sun tura ta gida.
Ranar da wuri suka koma gida suka fara shirin tafiya gida dama sun kammala sallama da kowa abdulrahman ya gama da makaranta shi kuma abdulrahim ya dau hutu a club dinsu washe gari da sassafe suka nufi airport.
Su abdulrahman na zaune suna jiran a fara kiransu da yake da wuri sukazo, abdulrahman bello da amira na zaune a gefe suna hira fans kuma sun zagaye abdulrahim a gefe sai hoto ake da autograph, su dady ma na gefe suna hira su abdulrahman sukaji anyi musu sallama ta bayansu, da sauri duk suka juya sai sukaga zainab abdulrahman ya saki fuska da sauri yana cewa "ahh zainab me kikeyi anan?" tace "wallahi zamu koma gidane tun dazu na hangoku nace kamarku sai da na hango abdulrahim cikin mutane na tabbatar ku dinne badai kuma Nigeria zaku tafi ba?" yace "wallahi kuwa yau zamu tafi ya kike ya jikin naki?" tace "alhamdulillah da sauki na warke thanks to you" abdul yace "karki fara ina mama da abdullahi?" zainab tace "yaya gashi can wajen siyen ticket gasu mama can kuma zaune kafarta na ciwoma shiyasa bata karaso kun gaisaba kasan jikin tsufa" yayi dan dariya kafin ya bata amsa bello yayi gyaran murya duk suka juya suna kallonsa sai kuma abdulrahman yace "yauwa zainab wannan dan uwanane abdulmalik wannan kuma kanwatace amira amira wannan sunanta zainab bello ga zainab dan nasan gyaran muryar da kakeyi kenan" zainab tace "aa kace abdulmalik kace bello wanne kenan" bello yace "duk daya ki zabi wanda yayi miki" sai kawai ta danyi dariya sannan tamaida kallonta kan amira ta mika mata hannu "assalamu alaiki" wani kallon tara saura amiran tayi mata sannan tace "ameen" ba tare da ita ta mika mata nata hannunba sannan ta juya ta bar wajen tayi wajen su dady.
Kowa sakin baki yayi yana kallonta, su dai basuga abin bacin rai anan ba abdulrahman ya bita da kallo har ta kai wajen su dady sannan ya dawo da ganinsa wajen zainab yace "I'm sorry zainab..." tayi saurin katseshi "ba komai ba sai ka bani hakuri maybe wani ya bata mata rai ba matsala" yace "bansan me ya faruba wallahi ba haka takeba ba halinta bane" tace "na gaya maka ba komai ka bani number dinka ta Nigeria yadda zamu dinga zumunci" ya karbi wayar da take miko masa ya saka mata number dinsa har yanzu yana cike da mamakin abinda amira tayi, bayan tayi saving tace "bari na koma Allah ya kiyaye hanya ka gaishemin da abdulrahim idan ya sami fitowa" yace "muje na gaishe dasu maman abdulrahim kuma zaiji insha Allah bello muje ko?" suka jera har wajen su maman nata lokacin ma abdullahi ya dawo shima suka gaisa sannan suka dawo jin an fara kiran jirginsu.
Tun daga lokacin amira tayi kicin kicin ta daina kula kowa, ko abdulrahim sarkin tsokana daya dawo haka yayi iyayinsa ya kyaleta amma taki kulashi daya tambayi abdulrahman abinda akayi mata shima kafada kawai ya daga masa yayi gaba, ko da suka shiga jirgin seat din amira abdulrahim da abdulrahman a hade yake amma sai tacewa bello suyi exchange shi ya dawo nata ita kuma ta koma kusa dasu prof. Wannan canjin na amira ya tayarwa dasu abdulrahim hankali sosai dan harsu dady sun fahimci fushi takeyi da suka tambayeta tace ba komai suka tambayi su Abdul din su kuma sukace basusan abinda akayi mataba. Suna isa Nigeria suka tarar da drivers din prof guda biyu suna jiransu a airport din suka shiga daya ya wuce dasu abdulrahim gidan prof dayan kuma ya dauki su amira suma zuwa gida.
Dayake da wuri suka taso sunyi zuwan wuri duk da a baccin gajiya suka karasa ranar washe garima haka suka wuni bacci sai la'asar sannan suka shirya suka tafi gidan dady inda zasu dau umar zuwa gidansu dan cikin satinnan suke son zuwa zamfara dan haka suna bukatar gidansu ya kammalu cikin yan kwanakinnan.
Suna shiga amira na zaune a falo tana danna waya sukayi sallama ta amsa amma still ba kamar yadda ta sabayi musuba, suna zama momy ta fito suka gaisa tayi musu murna sannan ta shiga kitchen, abdulrahim yace "amira" hankalinta nakan waya tace "naam?" yace "wai me akayi mikine? Me ya sameki? Wani laifin mukayi miki? Idan wani laifin mukayi miki ki gaya mana mu baki hakuri wannan punishment din ya isa haka duk kin tada mana hankali, tun jiya babu wanda bai kiraki a wayaba kin ki dauka yanzu mun shigo kina wani sharemu menene hakanne?" zuwa yanzu ta daina danna wayar amma still bata bashi attention dintaba sannan fuskarta a wani hade take, jin tayi shiru bello yace "wai ko akan wannan yarinyarne" tayi saurin dagowa ta kalleshi "wacce yarinya" abdulrahim ma yace "wacce yarinya?" bello yace "wata yarinyace muka hadu da ita a Airport" amira cikin tsiwa tace "ina ruwana da ita da zanyi wani abu akanta? Ni na ajiyeta ko zamana take? Wanda ya damu da ita shi yasan da zamanta ni batama isheni kalloba balle na bata raina akanta" abdulrahim ya kalli abdulrahman da ya wani kashingide yana murmushi yace "wai Abdul wacce yarince ake magana akanta?" bello kuma ya kama dariya harda tintsirowa kasa yana rike ciki, abdulrahman ya wani marairaice murya "Allah sarki zainab ce fa bello bana son sharri me zainab tayi mata da zakace dan ita take fushinta?" abdulrahim yace "wacece zainab?" amira kuma ta mike "eh dama ai bance ita tayimin wani abuba balle kace nace Allah ya baka hakuri an taba 'yar gwal to banceba yaya bello ne ya kawota cikin maganar," sai kuma ta tsaya ta kare masa kallo shima ita yake kallo har yanzu yana kwance cikin kujera yana buga uban murmushi, kawai sai ta saka kuka tayi daki da gudu. Ai kuwa me zasuyi ba dariyaba gaba dayansu suka kwashe da dariya abdulrahim yace" nifa har yanzu bansan wacce zainab ake magana akai ba" abdulrahman yace "wannan yarinyar fa 'yar Chad wadda muka kwace hannun nigoginnan" sai kuma ya bashi labarin abinda ya faru a airport ai kuwa shima yaci dariya yace "kace kanada jan aiki irin wannan kishi haka" abdulrahman yace "banason wulakanci nagaya muku ku daina kunki ko?" bello yace "munafukai zaku dawo hanyanema ni kawai dan Allah a fasa kwan musha biki" kafin ya gama rufe bakinsa abdulrahman ya dima masa dundu suka cigaba da dariyarsu.
Daga baya umar ya shigo suka fice zuwa inda zasu, a lokacin yake gaya musu ai har an jera komai na gidan furnitures din an saka komai sai abinda ba'a rasaba, da sukaje gidan kuwa tun daga bakin get sukasan ba karamar haduwa yayiba, get din dayane na asibitin da gidan sai dai asibitinne fuskar building din gidan na daga gefe, karamine ba wani girmane dashiba dan sunce samartaka kawai zasu karasa a cikinsa, kana shiga katon falone mai dauke da kitchen da dining room kitchen din budadde kamar na turawa kusan zubin na apartment dinsu na California dining room din kuma yana tsakanin kitchen din da falon sai kofa guda daya wadda nan ne dakin khadija, da suka shiga dakin kuwa su kansu sai da sukayi tasbihi ga ubangiji saboda haduwar dakin, katone ciki daya da toilet ba wasu tarkace bane sosai a dakin illa round bed wanda yaji bargo da filalluka sai mirror, study table, dan wani waje mai kamar falo da kujeru guda biyu kawai da table a tsakiya komai anyi masa wajensa kamar dakidaki, wajen mirror din anyi masa design kamar walk-in closet da wajen kaya da komai duk da ba'a saka kayanba tukunna haka study area din har da bookshelf amma shima babu littafan, komai na dakin baby pink ne da white kan gadon har da wata katuwar teddy, dakin yayi musu kyau nesa ba kusaba anan suka kusan cinye lokacin sannan suka haura sama shi kuma dakunane guda uku suma an tsarasu sunyi kyau kamar ba za'a mutuba suma da furniture da komai sai hawa na biyu shi kuma ceiling length glass ne a wajen gaba daya fadin gidan a daki daya yake amma ba daki bane wani irin gym ne na gani na fada wanda ko a California sai mutum ya zuba kudi kafin ya mallaki irinsa, wajen yaji kaya babu machine din da babu har da wata 'yar bar a gefe daga can karshe kuma wajen kamar library akayi masa zagaye da bookshelf mai kyau cike kuma da littafai na kowanne fanni novels, health, business, environment da petroleum kamar wani libry din makaranta.
Ba su suka bar gidanba sai bayan isha dama an gama hada solar gaba daya gidan da asibitin dan haka ita aka kunna suka cigaba da zagayensu, suna fita daga nan suka ajiye umar a gida su kuma suka tafi makarantarsu zasu je su gaisheda malam su kuma gaisa da abokansu na nan makarantar, suna zuwa wajen ya hargitse ana ta hayaniya da murnar ganinsu da kyar suka samu aka barsu da malam din suka gaisa suka dan taba hira sannan suka fito wajen friends dinsu. Dama bello tunda ya dawo yakan dan shigo su gaisa su Abdul ne dai tun wancan zuwan da sukayi dan haka aka baje aka fara hira ana tafawa, da sukaji yunwa ma suka saka wani yaro ya siyo musu nama suka hadu da sauran abokan sukaci suka koshi, ba su suka tashi shirin komawa gidaba sai past 1am har motar da suka dauko gidansu bello abokan suka rakosu suna sallama, sai da abdulrahim ya bude kofar driver sai kuma ya shafa ciki "bello nayi gaining weight" bello ya kalleshi yace "a ina? Beside kai macene? Ina ruwanka da wani maintaining shape?" abdulrahman yace "tab lallai ka manta abdulne ko ka kwana biyu bakwa tare shiyasa ai yanzu ma yafi da wannan da kake ganinsa" bello yace "to yanzu ya za'ayi? Sai ka bari gari ya waye ai ga gym can ka dankara sai kaje kayi abinda kayi niyya" abdulrahim yace "noway bazan iya kwana da wannan tumbinba yadda za'ayi ku kaini kofar kwalli na danyi jogging kunga dare yayi babu motoci sai ku jirani ko ku tafi na taraddaku a gida" bello yace "kai abdul wallahi kai bala'ine dan Allah ka bari gobe kayi" yace "kaga idan ba zakaba abdul ya kaini shima idan ba zashiba nayi tafiyata abune me sauki" dole suka shiga motar tare suka kaishi kofar kwalli police station, ya bude booth ya dauko takalmansa har bello na tsokanarsa "kai dai kawai kace dama a shiryenka kake" bai kulashiba ya saka takalmansa sannan yace "kunanan ko zaku wuce?" abdulrahman yace "kayi sauri ka dawo munanan" shi kuma ya kada kai sannan ya miki titi da gudu.
Tun daga kwalli sai da yakai round din gidan gwanma sannan ya tsaya ya dan huta ya kuma juyowa, yazo dai dai round din silver jubilee wata mota tazo ta wuceshi kamar daga sama kawai sai gani yayi wata motar da fito daga side din state road ta daki waccen din ita kuma wadda aka daka din ta hantsila ta kifa ya zamana tayoyinta na sama. Da sauri abdulrahim ya tsaya yana salati sannan ya nufi wajen da niyyar kai taimako amma ga mamakinsa sai yaga wasu mutane su biyu sun fito daga waccen motar jikinsu gaba daya rufe da bakaken kaya sannan suka nufi motar da ta hantsila din, jinin jikinsa yasha sai ya buya cikin wani duhu yana kallon abinda ke faruwa ya fasa zuwa dan ya fahimci accident din ba na Allah bane.
Motar suka bude wadda tuni driver dinta ya zama unconscious suka bude kofar baya sai gani yayi sun zaro wata yarinya, da fari da hijabi jikinta sai dai garin kokawar da sukeyi da ita hijabin ya cire, budurwace ba zata wuce shekaru sha shida zuwa sha bakwai ba sai dai da alama yarinyar ba yar kasarnan bace ko kuma ba jinin nan bace, farace tas irin farin da ba na Nigerians ba sannan da hijabinta ya cire sai ya ga gashinta ya zubo kusan har kan duwawunta shima ba irin na Nigerians ba, a take abdul yasan he is hook for life hoton wannan yarinyar bazai taba barin kansaba ba kuma zai taba bari wani abu ya sametaba koda kuwa shi zai rasa tasa rayuwar dan haka ba tare da tunaniba ya fito daga maboyarsa ya kuma tunkari mutanennan shi kadai.
Bazai iya adar da yadda fadan nasu ya kasanceba yasan dai yaci galabar mutum daya suna kuma cikin fada da dayan wanda shima har ya kaishi kasa yana jibga sai da ya tabbatar ya ji jiki sannan ya mike ya juya yana kallon yarinyar wadda ta dunkule a waje daya jikin motar da suka fito da ita, gashin kanta ya rufe fin rabi na jikinta saboda tsahonsa da kuma cikarsa kuka take jikinta yana karkarwa, da sauri ya tafi inda take da niyyar rarrashinta dan jin kukan nata yake har cikin zuciyarsa sai dai baisan abinda ya faruba ya daiji wani abu mai tsananin karfi ya dakeshi a ciki wanda karfinsa yasa har saida Abdul din yayi tsalle baya sannan ya fadi kasa faduwar tasa kuma tayi daidai da wata kara da ta karade daren gaba daya, wani irin azaba yaji tun daga cikinsa ta hade gaba dayan jikinsa in seconds, da sauri ya saka hannu ya dafe cikin nasa inda azabar ta fara wani danshi danshi yaji yana dago hannunsa yaga jini sannan ya daga kai yaga wani mutun tsaye a kofar waccan motar da irin shigar dake jikin mutanen da suka gama fada yanzunnan hannunsa rike da bindiga a take Abdul yayi concluding harbinsa akayi kuma a ciki shikenan bashi da rabon sake ganin khadija dama dalilin da yasa yayi ta delaying zuwan nasu kenan bashi da rabon ganinta.
........................
Hi guys
😭😭😭😭 RIP Abdul Rahim
BINABASA MO ANG
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
