Washe gari da safe suna tashi daga karatun asuba lokacin karfe bakwai na safe sai suka tafi gidan Dady kamar yadda ya umarcesu, ranar Amira tun da sassafe ta tashi da kanta taje tayi wanka ta saka uniform dinta bayan ta shafa mai, sai a lokacin Momy ta shigo da niyya tashinta amma ta tarar ita harta gama shiryawa, Momy na mamakin wannan sauyin yanayi tace “haba Amira babu wanka a haka zaki saka uniform? Cire kizo muje nayi miki wanka kinji?” da murnarta tace “Momy ai nayi wankan” Momy tace “waye ya yi miki?” Amira na dauko takalman makarantarta cikin lokar takalmanta tana cewa “da kaina nayi yanzu na iya da kaina zan dingayi” Momy tayi dariya tace “aa Amira baki iyaba wuce muje na sake miki” dagudunta tayo waje tana cewa “wallahi Momy na iya nayi da kaina daga yanzu da kaina zan dingayi” dole ta kyaleta kar kuma a tsokano tsuliyar dodo.
Ranar haka Amira ta zauna taci abincinta da kanta ba wata rigima tana ta faman zancen yau Dady zai saka su yaya Abdulrahman a makaranta zasu dinga tafiya tare, tun Usman na jinta yana dauke kai harta isheshi, da karfi ya daki table din da suke cin abincin a kai yace “would you shut off your mouth? Kin damemu haba yarinya baki da magana sai yaya Abdulrahman this yaya Abdulrahman that idan na kuma jin ko sunansa ne a bakinki sai na fasa miki baki kazama kawai mai wasa da almajirai” tsuru tsuru tayi da ido tana kallonsa yana gama bala’in ta kalli Abubakar da niyyar kai kara sai kuma ta jiyo ana kwankwasa get ai kuwa ta manta da wani Usman da warning dinsa ta dire daga kujerar da take kai tayi waje da gudu tana cewa “Momy kizo ki bude kofa gasu yaya Abdulrahman nan sunzo zamu tafi makaranta” dariyace ta kubcewa Abubakar yana cigaba da dariyarsa yacewa Usman “kagani ta maida kai shashasha daga gama fadanka ko maida numfashi bakayiba tayi abinda ka hanatan wai kai menene matsalarka dasu Abdulrahman ne?” mikewa Usman yayi ya harari wannasa sannan yace “babu” yayi cikin daki a zuciye dan baya ko son su shigo su tarar dashi a falon baya ko son ganin fuskarsu balle wannan Abdulrahim din mai ji da kan tsiya kamar dan gidan sarkin santanbul.
A can tsakar gida kuwa ana bude kofa Amira ta tafi da gudunta da niyyar rungume Abdulrahman sai kuma taci birki saboda ganinsu babu uniform, gaba daya suka zube suna gaishe da Momy ita kuma ta amma musu cikin sakin fuska sannan ta juya ta koma ciki ta barsu da Amira wadda tayi kicin kicin da fuska, murmushi sukayi mata sannan Abdulrahman yace “yaya dai Amira naga kina hade rai” tace “ina uniform dinku?” Abdulrahman ya daga kafada yana cewa “bamu dashi” ta bude baki da mamaki sannan tace “tab aikuwa ba za’a barku ku shiga makarantarba dan kowa sai ya saka uniform yake shiga” kafin ya bata amsa Momy tayi kiransu ta window din kicin dake cikin harabar tana cewa “Abdulrahim ku shigo ku ci abinci ku manta da wannan akun dan kun kusa makara” da sauri suka amsa da to Momy sannan sukayi cikin gidan gaba daya.
Suna shiga falon Dady na fitowa shima ya gama shiryawa Amira tace “Dady ina uniform din su yaya Abdulrahman?” yana zama kan kujera yace “princess sai munje an yadda za’a daukesu tukunna sannan zan dinka musu uniform kinji ko? Yanzu kizo kici abincinki kar mu makara” tace “ni na gamaci ku nake jira kawai” Dady ya kada kai sannan ya fara zuba abincinsa, su Abdulrahim suka matso suna gaisheshi ya amsa musu cikin sakin fuska sannan Momy ta kawo musu nasu abincin suka koma waje sunaci Amira ta tasa su a gaba tana faman basu labarin makaranta.
A mota Amira ta makale sai a cinyar Abdulrahman zata tafi suka kyaleta Allah yaso motar babbace dan haka ta dauke kowa a hanya suka sauke Abubakar ya hau wata motar zuwa kumbotso su kuma suka wuce makarantar su Amira, ana zuwa kowa ya fita banda Dady dasu Abdulrahim sai Amira itama ta tsaya a bakin kofar motar Dady yace “maza yi sauri mana Amira kun makara fa kar a dakeki” tace “Dady su yaya Abdulrahman nake jira” Dady yace “princess su yaya Abdulrahman banan makarantar zasu shiga ba kin gane yanzu zan kaisu tasu maza ki shiga taki” ai kuwa ta fara buga kafa a kasa tana cewa “Dady ni anan nakesu a sakasu” Dady yace “zo kiji wata Magana yarinyar kirki” har ta fara zubar hawaye da yake Amira akwai lafiyar hawaye, tana zuwa wajensa yabude kofarsa ya dauketa ya dora akan cinya yana goge mata fuska yace “ya isa kukan haka kinga yanzu a makarantarku ba lokacin daukan sababbin dalibai bane canma dan dai abokinane shiyasa zai daukesu nan kuma ba abokina bane sannan princess yanzu Dady bashi da kudin saka su yaya Abdulrahman anan makarantar amma idan na samu zan dawo dasu nan ai kina yimin addu’ar Allah ya bani kudi ko?” da sauri ta daga kai ya cigaba ”yauwa yarinyar kirki yanzu ki kara sosai kinga yaya Abdulrahman za’a saka a makaranta dan haka yanzu ki tafi ki shiga makaranta kar a dakeki kinji?” ta kuma daga kai sannan ta sauka daga cinyarsa ya sunkuyo yace “bazakiyiwa Dady kiss ba?” har ta juya zata tafi sai kuma ta juyo tayi masa a kumatu shima yayi mata sannan ya daga mata hannu “bye bye” itama ta daga masa ta zagaya sannan ta dagawa su Abdulrahman ma ta shige makaranta da gudunta.
YOU ARE READING
ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)
Teen FictionLabari akan rayuwar almajirai da irin wahalhalun da sukesha Labari akan Yan biyu masu kama daya da irin soyayyar da suke yiwa junansu Labari akan bakin kishi da illolinsa matsalolin da yake jawowa cikin iyali da sakamakon masu yinsa. Labari akan il...
