ZAƁEN TUMU 32

345 63 6
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 32*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Wani daƙuma ta kaiwa wuyan kabeerun wanda bai zata ba se ganinta yayi agun, saura kadan su faɗi ita dashi da yaro affan wanda yake hanunsa, ya saka ihu.

Bangajeta yayi da dai dain ƙarfinsa,  tayi taga taga xata faɗi amma ina daya masifa na cinta tayi ta maza tayi

Ta tsaya ƙyam, ta dada kukan kura tayi kan duk wani dayaje gurin tana wargazashi tana dure duren ashariya manya manya , ajiye affan yayai yayi kanta dn yasan halin haukarta sarai zata. Iya komi, daƙyar ya damketa yana cewa " meye haka, meye haka ramlat bakya ganin mutane ne"

" Sakeni munafuki ni zakazo ka wani rufawa zance ka turani can ashe man sheƙe ayarka kakeyi akazo aka buɗe gida bada sani na ba"

Cikin tsawa hajiyar tofa tace

" Kai saketa muga iya rashin mutuncinta saketa"

Kabeer ya ɗan sake ramlat yana ɗan tsoro tsooro, idanun hajiyar tofa ya sanya ta yar natsuwa.

Hajiyar ta dogaro yar sandarta ta iso gabanta, wani kallon ƙaskanci hajiyar tayi mata kafin ta doka mata tsawar da saida kowa ya firgita

" Keeeeeeee ramlat kike ko wa? Haka ya isa! Haka ya isa nace!

Jinina sun fi karfin wulakancin mace a rayuwa, duk abinda kikeyi kallonki kawai mukeyi dn mu dattawan ƙwarai ne, muna ƙoƙarin kau da kai ne kawai dn muyi miki adalci, amma yanzu kam kiyi taka tsan tsan duk wani tsubbunki da shirkarki munfi karfinki, ki sake tunani, aure ne de kabeeru yayi bqbu kuma wanda ya isa ya hana aukuwar haka dn yin Allah ne, ya rage gareki ki natsu ki zauna ko ki nemi hanyar fita, duk wani kawaici da mukayi miki hakanan ya isa tunda ke bakisan zuru ba, ki kiyayeni ingaya miki ki fita daga idanuna"

Jikinta yayi sanyi duk seta muzanta, hanunta duk yana zubar jini saboda gilasai data faffasa, da gudu ta juya ta fice tana kukan bakin ciki.

Ji yayi kamar zai ruga da gudu ya kamota dn tsabar tausayin data bashi, yasan shine bai kyauta ba anan kam wanan ɗin dayayi baiyi adalci ba.

Jiki a sanyaye aka gama taro aka watse, daga bisani kuma aka kai amarya cikin dakinta, hajiyar tofa ta musu nasiha, tsohuwa mai dattako ta nuna masa yayi adalci tsakanin matansa, sanan ya tursasawa matansa yin zumunci da yan uwansa da iyayensa da sauransu,

Haka aka watse aka barsu, tashin hankalin dayake ciki ya sanya ma bai bi takan amarya bq, ficewa yayi dn nemanta.

Amarya tun tana makure harta tashi ta kulle kofarta ta kwanta.

Yawo yakeyi har karfe 1 na dare bai sameta ba, gidan jammy ya isa, cikin tashin hankali, inada ya tarar batanan, tare da jammyn suka fice nemanta, a wani bar suka sameta tasha giya tayi tatul

Hankalinsa ya ƙara tashi, a zatansa wanan shine karo na farko da hakan ta faru dn tsananin ƙaunarsa da takeyi, kamar yadda yake tunanin kishinsa akanta.

Gidan jammy suka nufa da ita tanata kwarara amai, sai sambatu datake tayi,na hauka, saida bacci ya kwasheta bayan an mata allura ne, gabanin asuba kawai ya tuna da yar baiwar Allah daya baro a gida, gabansa ya faɗi,

Saida yayi sallah a unguwar su jammy ɗin sanan ya wuce gida,

Itakam harta tashi ma tayi sallah, tana daga kan sallayya tana tunanin rayuwar daza fuskanta, bata hango mutunci acikin idanun matar yayan nata ba, bata hango wani tarin alkhairi ba a tattare da wnaan zaman nata ba da su, dn ta lura da yadda madugu uban tafiyar yake wani rawar jiki akan matarsa, musamman data juya ta fita ɗinan ƙiris ya rage ya rufa mata baya, snaan gashinan ƙiri ƙiri kuma ya fice tun dare gashi har yanzu shiru..

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now