ZAƁEN TUMU 13

320 66 10
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 13*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Gudu take sheƙawa da dukkan ƙarfinta, har ta isa bakin titi, saura kaɗan mai tasi ya doketa, yaja wani birki mai ƙara, yana mai rufe idanuwansa gani kawai yakeyi ya bugeta ma.

Da hanzari ta faɗa cikin motar tana haki

" Karo site"

Tace dashi, a firgice ya juyo, ya dubeta, kyaunta ya daɗa tabbatar masa to gamo yayi da wata aljanar

Baisan lokacin da bakinsa ya soma furta , " wa innahu min sulaimana wa innahu bismillahirrahmanirrahim"

Jikinsa na rawa,. Ganin zai ɓata mata lokaci ya sanyata cewa " kai dallah malam ni mutumce kqmar ka, ka kaini inda na gaya maka"

Ta ɗagomasa kafafunta farare tas tana cewa "ka ganni da kofato ne ko me? Dazaka wani firgice ragon maza kawai"

Duk masifar datake ciki bai hanata tsiwa ba.

Da ƙyar ya yarda da abinda tace mar da kuma shaidar ƙafar tata, yaja motar suka bar gurin.

Tafiya ce mai tsawo daga gwagwa karmo zuwa karo site, akkalla awa guda, har suka isa bai gaji da ƙare mata kallo ba, bai taba ganin kyau irin wnaan ba, kuɗi masu yawa ya cajeta itakam ko ajikinta ta miƙa masa ta faɗa gidan kai tsaye.

Tun daga falo ta gano jamsyn na tare da wani ƙaton a ɗaga, sanan ta ƙara tabbatar da hakan jin wasu sautuka da gurnani na fitowa daga ɗakin jamilan, nan ta kwanta ta naɗe akan kujera, gabanta nata faɗuwa har barci ya kwasheta.

Da safe jamsyn tayi gamo da ita akan kujera shame shame.

" RB, lafiya? Ki  tashi"

Tana ɗan bubbugata, a firgice ta farka kamar zatafice da gudu, tana cewa " na kasheshi, na kasheshi!

Da ƙyar jamsy ta damƙeta, tana jijjigata dn ta dawo hayyacinta,

" Ke meye haka ramlat, ko dai kinyi gamo ne, meya faru, nutsu ki faɗamin meya faru?

Jikinta na mazari tace

" Nakashe baba ladan"

Wata tsuka jamsy ta ja

" Toh se me? Daman ƙuda gurin kwadayi yakan mutu ai".

Wanan shine mafarin hargiysewar rayuwarta........

******************

"Allah ka azurtamu da yaya nagari, ka bamu zuri'a ɗayyaba,kabamu yayan da zasu zamewa al'ummar musulmi alkhairi ba musiba"

Wanan yakamata ya zamo shine aduar kowane uwa da uba cewar abba,

Wanda yake zaune yana karanta wata jarida, da aka rubuta wani kanun labarai, da wani ɗan datyijo mai kamala ajiki rubuce kamar haka " kotu ta ɗaure mahaifin wata yarinya dayayi mata auren dole har ta halaka mijin"

Jikin umma a sanyaye tace " A'llah ka rabamu da mummunar ƙaddara "

Abba ya soma bawa umma labarin yanda abin ya auku...
" Yarinyar ita ta kai ƙarar mahifinta ta kai kanta ofishin yan sanda , lokacin data aikata taasar, shine fa aka taho da mahaifin, wanda ya kasa cewa komi, nan yan ƙungiyar kare hakkin ɗan adam sukayi ruqa sukayi tsaki aka ɗorawa uban laifi, har kotu ta rufeshi na tsawon watanni daga nan ƙungiyar musulunci tabi ba'asi aka gano akan rashin ji uban ya aurar da yarinyar, suka karɓa masa nasa yancin"

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now