MACE MUTUM WRITTERS ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 24*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE.
Hajiyar tofa ta tashi ƙafa da ƙafa a wani dare, ta tafi guurin mai share mata kukanta, wani mutumin daya taka rawar ganin gurin ceto iyalanta duk tsawon rayuwarta, wani bawan Allah da bautar Allah kadai ya sanya gabansa shiyasa komi nasa yake zuwa da sauƙi, kyawun halinsa kuwa bazai faɗu ba, mutum ne managarci wanda samun ire iren sa a wanan ƙazantacciyar duniyar zaiyi ɗumbin wahala, tsohone tukub tukub , ko gani bayayi daman kuma ance da makatar aka haifoshi sede tarin baiwa da Allah ya azurtashi dashi mai yawa, takun ka kadai zaiji ya gane kai wanene, wanan tsoho dai shine jigon komi na the tofa's.
Seda ta is akan dardumar tayi masa sallama, ta zauna hanunta ɗauke da yaro affan, wanda yake ta wasansa,
Yar gyaran murya yayi kafin yace " yar mutan tofa barka da zuwa"
Cikin girmamawa haj tofa tace " barka dai baba ba'abah, dafatan mun sameku lafiya?
Ya ɗan ajiye tasbahansa yana miko mata hannu alamar ta bashi yaron yana cewa " lafiya yar tofa"
Ta mika masa yaron tana mamakin ya akayi yasan da yaro a hanunta dn bai nuna alamu ba, sai ta tuna irin abin mamaki nasa wanda tun suna yara yake dashi, dn yayi wanan ai ba wani abin mamaki bane, mutumin da ko hanunka ya rike zaice wane ne, ko yani sautin takunka ,aice wane ne dn yayi wnaan ai ba abin mamaki bane ko kaɗan,
Adduoi masu tarin yawa yaro affan yasha na wajen awa guda kafin ya dauko wani dabino ya tauna ya kuma fuszar a fuskar yaron sanan ya bashi a baki, ya dauko wani ruw aya shafe masa jiki sosai, sanan ya mika mata shi
Yana cewa " wanan yaro mai abin mamaki ne ku kula dashi sosai, da alamu zaiyi tsawon rayuwa mai tarin albarka, saide mahassada kuma da bakin ido zasu dameshi, amma a rike adua da Allah komi sai yayi kyau, kada ayi wasa dashi"
Ta amsa da " toh ba'abah zamu kiyaue insha Allahu"
Bayan shiru ma wani lokaci haj tofa
Ta ɗan gyara zamanta sosai ta fuskanceshi ta fara zayyana mata abinda ya kawota, na tsawon lokaci, shiru yayi tukkuna na kusan minti 20, kafin ya fara yi mata wasu jawabai a sarƙaƙe dn shi komin cikin sakakiya zai faɗeshi, wala Allah ko kuma yanayin baiwar tasa ce haka sai Allah
" Naso ace kun tuntuɓeni kafin ya aure waanan shaiɗaniyar, dn zata zamo silar abubuwa marasa daɗi dayawa, kuma auren nasu mai tsawo ne in an ɗaura shi kuma gashi an ɗaura, sanan tanada sa'a a rayuwarta komi tasa gaba yana yiwuwa, kuma tsafi shi ta riƙa kuma kinsan yanda tasirin tsafi yake akan mumini, sede muyi iya koƙarinmu akan hakan, amma da zaa samu mace mai nagarta mai haihuwa wacce ba budurwa ba, wacce mijinta ya rasu se a aura masa ita, yazamo kada wanan shaiɗaniyar ta ji, kuma ya zamo da yardar ita yarinyar, sanan zaa sanar da ita halin dayake ciki taimako zatayi, nagartarta ce zata iya ƙwatoshi daga cikin ramin daya auka, toh shi koda bada saninsa bane akayi auren zai samu waraka, zakuma ki dage dayi masa aduoi, kuma abashi magungunan da zan bayar yayi amfani dadu na kwana 7 batare da tsallake ba, sihirin zai ragu, sanan wanan yaron zai iya zama garkuwa gareshi tunda yana sonsa bilhaƙƙi da gaskiya, SOYYAYYA ta gaskiya ita zata tserar da muhammad kabeer daga mummunan TARKO n dayake gabansa, kije kiyi tunani sosai akan abinda nace koda bayan shekaru biyu ne ko fiye da hakan, idan bana raye toh, in ina raye kuma zan ci gaba da agazawa, amma kibar wasiyar abinda na faɗa kema dn halin rayuwar, bamusa karshen ranarmu ba"
Mal ba'abah ya kare zancensa cikin murmushi mai ƙayatarwa, magunguna ya bata da aduoi masu tarin yawa dda zaa tofa a ruwan zam zam ko ruwan sama, da hayaƙi da sauransu, sanan ta tafi zuciyarta cike da lissafi kala kala.
VOCÊ ESTÁ LENDO
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...