MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 37*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
LAMARIN DUNIYA
Washe gari da sassafe sai gashi kamar an jehoshi daga sama,
Ya samosu a dakin suna cin ɗumamen tuwon gero yaji manshanu lutsu lutsu ga. Kunun tsamiya agefe yanata ƙamshin kayan yaji, ga kuma gasashen naman rago dayaji albasa da kayan yaji da daddawa.
Yawunsa ya tsinke, he cnt remember wen last yaci abinci ba?
Zama yayi bayan ya gaida su suka amsa masa fuska a sake.
Hajiya tofa ce ta loda masa abincin ya cinye kuwa tas!
Har saida ya basu tausayi,
.saida kowa ya natsa hajiyar ta katsesu
" Kai kabeeru yaushe matarka zata koma ɗakinta?
Wani tashin hankali yaji ya masa dirar mikiya, ta koma?
Gumin dayake tsatstsafo masa ne ya sanya hajiyar tagani abinda take kokonto din ya tabbata, tabbas aikin
Sihiri abu ne mummuna, wai yau jininta ne ya zamo haka ," Zuwa gobe zan tattara na maido maka da ita, tare da mai tayata zama zan kuma zauna nima na sati biyu kafin ta ƙare wanka"
Wani ƙwarjini da hajiyar tayi masa ne ya hanashi ce mata komi sai toh!
Amma fa can kasan ransa hantar sa har wani kaɗawa takeyi dn tsabar tsoron me zaije ya zo.
Fitarsa ne hajiyar ta dubesu tace " tun yaushe ne ya shiga cikin wanan yanayin"?
Ummansa tace " ranar da akayi haihuwar dai da safe yaje ɗauko abin bukata shikenan komi ya canza, bamu.muka ganshi ba sai bayan kwana biyu"
Cikin faɗa haj tofa tace " se kuka zuba masa ido? Ko kuma se kika kama wanan ɗacin ran naki da bambamin banza da ba zai gyara komi ba ko?
In banda rashin hankali wanan yaron kana gani ai kasan aikin sihiri ne"
Ta dubi khulsum itama ta samu rabonta
" Shasha shai kuna sakaci da tsarki kam ai zakuga komi, ko wand irin sharri sai ya isar muku ai, in banda rashin hankali a wnaan zamanin na hutu ma ruwa har acikin bayen ka kuma an rarrabe maka me sanyi da me zafi ma amma bazaku yi tsarki ba akan kari dn tsabar lusaranci kwana da junan kawai kuka iya, baku tsare hakkokin saduwar ita kanta wai ku yan boko, yaran yanzu wai daga kunji shiru kuna zaman lafiya namiji namuku yadda kuke so sai ku dauka wai shi kenan komi ya ƙare bazaku nemi taimakon Allah ba?
Idan akwai likacin tsananin adua ai wnaan lokacin ne kuwa, bare masu kishiyoyin da kun tabbatar babu Allah a ranku,".
Ta saukar da huci kafin taci gaba
" Bana manta lokacin da akayomin kishiya wata yar kudu wai dan ta iya karatu da rubutu zata taimakawa malam da kula da arziƙinsa,wallahi data zo sai da nazamo kamar kashi a idanunsa nida yayana, wnaan wani abu ne da baku sanshi ba baku taɓa jinsa ba sai yau, nasha azaba kamar ta shekaru biyar, saida malam ba'abah ya farkar dani, muka hadu da yan uwansa da iyaye muna adua ana ta karya sihirorin, data min tayi masa, hatta warin jaɓa saida ta shafamin, daga karshe ta shafemin gabana wallahi ko bawali banayi nakoma namiji, toh anan ne iyayena suka sa hannu da malm ba'abah, aka mata fata fata!
Da kyar suka rabu,ire irensu annoba ne ai, kadangaren bakin tulu kenan, dataga zata rasa kawai sai tayi kan mai uwa da wabi ta kusa kasheshi, shine aka kamata, sun haihu da daya ta haifi wani abu kaman dodo, yazo ya mutu, toh wallahi munyi shekaru kafin mal ya daowo dai dai
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...