MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 46*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Haka rayuwar dai take cike da tarin abin mamaki , cike da ƙudirin ubangiji kala kala, dukkan rayuwar rubutaccen lamari ne daga rabbi, kilan da ɗan adam yasan da hakan ba zai ɓatawa kansa lokaci ba gurin matsawa kansa da hassada da hankoron neman duniyar da ba tasa ba.
Daga gidan kurkun aka gungurota a keken guragu, bataga kowa nata ba, duk da yau ta kasance rana ce da akayiwa masu laifi irinta da wanda suka ma fita, wanan wata afuwa ce da sabon sgugaban ƙasa yayi masu alfarmarta, wasu ƙwallah masu zafi ne suka zubo mata dn takaici da nadamar datakeji acikin ranta, nadama irin wacce batada rana ɗinan.
Ta faɗa kogin tunani sosai, hankalinta ya bar duniyar datake ciki ya lula da ita can wata duniyar, jin an motsa keken data ke kai ne ya sanyata ɗago kanta dn ganin waye cikin firgici, tana fata bawai mayar ta zaayi ba cikin musibar data fito ba, da kuwa ta kuru!
Fuskar data gani ɗin ce ta girgiza tunaninta matuƙa,
" Kwantar da hankalinki mama ba da niyar cuta nazo miki ba, nazo gurin nan ne dn tallafawa ire irenku, jiya nasamu labarin shugaban kasa zaizo shine na iso da tawagata dn taimako"
Jikinta ya s ake macewa, sede ta ɗan risina ganin bata ma ganeta ba,
Juyawa matar tayi tace " ku sata a mota, akaita gida zatayi kwatancen gidanta, ga wnaan mama kija jari"
Ta ɗora mata rafar yan dubu dubu akan cinya,
Harta bar gurin kallonta takeyi, jiki a sanyaye, aka sata a mota ta faɗi umguwar da take wasi wasin ko zata ga iyayenta. Saide taci rashin sa'a dn labarin data samu shine iyayen mata sun koma.can garinsu da zama.
Tashi. Hankali wai ba'a saka masa rana! Yau wai itace tazamo musaka, kuma marar galihu?
Lalai duniya abar tsoro ce! idan ta ɗauketa da faɗi ma toh yanzu kam ta tsuketa tsut! TANADA LABARIN da zata bawa MATA masu ire iren halayyarta.
Da kyar ta samu ta kwana a makota, da safe ta bawa yaro kudi ya gunugurata zuwa kan hanya ta samu me mota ya dauketa ya kaita tasha sai garin mahaifanta.
Tagano gurinnda mahaifanta suke da ƙyar!
A hankali ta tura keken nata zuwa tsakar gidan wasu yara ne guda hudu maza sunata wasansu abin shaawa kyawawa, daga gefe wata matace mai kamala take tuka tuwon garin masa vita, gidan ya kaure da kamshin daddawa yar usuli, hankalin yaran ya koma kan wani dan matashi daya shigo gidan hanunsa ɗauke da leda manya manya, da gudu suka rufeshi da murna " oyoyo baffa am oyoyo"
Ya rungumesu yana kiran sunayenau yana raba musu abinda ya kawo musu.
Hanakalin matar ya dawo kansu tana ɗan murmushi irin na kamala ɗinan,
Wata yarinya matashiyace ta nufo gunsu saye da hijabi cikin kwalliyarta tsaf! Irin kyawawan fulanin nan ne, ta isa gareshi ta amshi guntun kayan hanunsa.
Ganinta ya sanyasu yin turus!
Dan basu ganta ba sai wanan lokacin.
Idanu ya zuba mata sosai amma ya kasa ganota,
Har saida mahaifinsu ya fito ya gansu sunyi tsaye cirko cirko tukunna
Duba ya kai gareta sosai snaan ya ganeta.
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...