ZABEN TUMU 42

329 70 3
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 42*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Haj mami ta nemeshi da kanta dn su tattauna, ya samesu a babban falon gidan.

Hajiyan tana sharɓe ƙwallah ta sake yi masa gaisuwa , shima yayi mata, duk sai yaji babu daɗi , naylah duk ta fice hayyacinta , ya tuna faɗansu na ƙarshe da ya ceto ta a hanun saurayinta wai wizzy ko wizard shi bai ma iya sunan, wanda ya sanya ta bugu kuma yakeson ya keta mata haddi, kb ya ƙwaceta da kyar ya casa wizzy irin dukan nan na kawo wuƙa sanan ya tafi da ita, seda ta wuni cur kafin ta farka, ta tashi zata masa tsiwa ya tsitstsinka mata mari, wanda yayi sanadin yin shirunta ya ɗora mata jawabai kamar haks

" Ke naga alama so kike ki maida kanki dabba! Wace batasan inda ya ke yi mataciwo ba, ko kinsan shaye shayenki ya kusa lala ta miki hanji, ko kinsan wanan ɗaniskan yaron keta miki haddi ya kusa yi ya miki tsirara Allah ya kawoni, dana ban yarda da inda kukaje ba hakan yasa nabi bayanku a karo na biyu kuma Allah ya taimaka na ganshi bai kaiga samun nasara ba, ke ko kunya bakiji? Bakya tausayin mahaifinki? Kudi hauka ne naylah?

Daga nan ya cilla mata key yayi tafiyarsa tun lokacin ya ƙudura ya haƙura da aikin nan, kada nayla ta sa masa hawan jini da ɗiwa.

Ya dubeta yaga duk ta koɗe, abin tausayi

.h mami ta katseshi da cewa" alh ya bar wasiya kai zaka raba gadonsa yadda ya cancanta, sanan ya ware wasu kuɗaɗe yace abaka, sanan.

Ni da anyi takaba zan koma saudi nida naylah, dn bamu da kowa a nan"

Seta fashe da kuka,

Jikinsa a sanyaye yace " nayi alƙawari zan riƙeku anan ɗin saboda shine wasiyar da alh yayi mani, sanan nikam ban bukatsr duk abinda ya bari wanan na bsrshi cikin gadon naylah"

" Bazai yiwu ba uncle kabeeru, zaka karɓa dole tunda wasiya ce"

Cewar nayla wanda itama kukaan takeyi.

Haka sukayi ta muhawara dai babu wanda yaci nasara.

Yan uwan alh aka nemo da kuma malami akayi rabon gado mai tsanaki, inda kusan komi yaa zama na nayla ne, wacce ita yanzu abin duniyar ma sam baya gabanta mutuwar mahaifinta ta doketa a ƙoƙon zuci.

A wnaan rintsin ne kuma zancen zuwa kotun su ne ya tashi, inda misbah ya maka ƙara a kotun ƙoli ta najeriya, nan yayima khulsum ɗin bayanin komi taji tsoron mutan duniya , wai ramlat ce tayi haka nan

Affan ne ya dora musu da cewa " abba inason faɗawa ummi kulum setace batason gulma, anty mai kyau ma tace seta kashe uncle habeebu"

Nan suka sanya salati sunata mamakin wanan magana, nan yaron ya feɗe musu daga biri har wutsiya,

Sun tsirita ainun da ramlat!

Wanan ya ƙarawa kabeeru kaimi sosai kan neman haƙƙinsa.

***********

Dirarsa abuja sai ya zamo gurin yayi masa sabo komi ya ƙara havaka,

Apartment na misbah ɗin suka sauka,

Suka huta, sanan suka tattauna kan yadda za'a ɓullowa abin

Barister bello gada shi zai jagoranci masu ƙara, wan, wanda yake aboki ga misbah ne .

" Ramlat dole fa zaki hakura da wanan zancen, na rigada na yanke hukuncin"

Ramlat ta dubi ambursa cikin marairaicewa tace " menene dalilinka na bawa matilda matsayinka?

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now