ZAƁEN TUMU 9

344 68 10
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 9*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Jan hankali ga marubutan online

Ko kinsan duk abinda kika rubuta ko ka rubuta, za'a tashe ki ranan lahira kuma billahil azeemu saikin faɗi bayaninsa dallah dallah, raqeeb da atteed suna rubuta duk abinda kika rubuta sun ajiye shi a kundinki , rubutun batsa da abinda bai kamata ba ba namu bane, yaɗa fasadi ne a doron ƙasa shikuwa mai yaɗa fasadi a doron ƙasa kowa yasan makomarsa idan bai tuba ba, duk abinda kika rubuta yayi sanadin lalacewar wani ko kinsan kinada kamasho? Ko kinsan idan mutum ya karanta sha'awarsa ta motsa yaje yayi zina ko istimna'i akwai babban hakki bisa wuyanki, ada can da rubutu yake da tsari ana koyon abubuwane masu muhimmanci ana daukar ilimi tare da darasi, amma yanzu fa? Rubutu akasar Hausa dn zuwan kafafen sadarwa na zamani ya zama wani abu daban, kowa dai rubutu, da mai ma'ana da mararshi, kawai karenmu mukeci babu babbaka, dayawanmu suna zubar mana da mutunci, iyaye suna ganin laifinmu, al'umma tana nuna mu da yatsa, wallahi abin kunya ne ga musulma cikakkiya, kuma bahaushiya ta ɗebe kunyarta ta zauna ta rika rubuta blue Film a matsayin wai koyarwa ko wayar da kai , wayewa ba hauka bane fa, ko su Turawa ba haka sukeyi ba sunada tsari ko akan iskanci ne, abun takaici ne wanan, ga kuma masu karantawar kuji tsoron Allah, ku kuke bawa masu rubutun karfin guiwar yin ire iren rubutun nan, ku tuna zaku haihu kuma idan ɗiyanku sun karanta littafinku ko sunga abinda kuke karantawa zasuyi koyi dashi! Ana barin halal dn kunya ma balle haramun, shi kansa rubutun har yanzu malamai na tarƙiƙi akan ya hallatta ko bai halarta ba,amma muke sake munana abin, kuyiwa Allah ku sassauta kurage ko ku haƙora da rubuce rubucen batsa dn mu, dn ƙannenmu, dn 'ya'yan mu, da kuma mazajenmu dn zaki ɓata yarinya tazamo miki masifa tashiga rayuwar mijinki ko ƙaninki ko ɗanki,dn kuma lahirarmu itace abar tsoro! Karkice wai bakice kowa ya karanta ba, kina da hakkin rubutu, abinda kika rubuta ɗin shine Allah baya so, kina haddasa fitina, idan aka barmu da yadda zamanin ma ya lalace ya isa! Dn girman Allah ba sai an kafa rubutu ba, kuyiwa Allah ku dawo mana da martabarmu, da mutunci mu ta marubuta, mai rubutu da gyara aka sanshi bada gurɓatawa ba.

Dafatan saƙon nan zai isa duk inda ya kamata.

Ta duba gabar ta duba yamma  Tarwal, babu komi sai tarin bishiyu dasuke kaɗawa sun rangaji, setaji kamar motsin wani abu anan ta tsuguna tana kuka, yau ta tabbatar kabeer baida imani, ko me tayi masa bata cancanci irin wnaan hukuncin ba, tafi mintuna talatin tana kuka,  kafin ta tuna da jakarta, ta duba inda ta wurgar da  ita ta rarrafa ta ɗaukota, ta lalubo wayarta, hanunta na rawa ta danna kiransa , ta ƙare rud'unta bai ɗauka ba a karo na farko , ta ƙira a karo na biyu..

Yana tsaka da ayyuka yaga kiranta , da sauri ya ɗauka dn sai yaji kamar wani abune yake faruwa, kukan data sanya ya tsoratashi

" Yaya Affan ka taimakeni, dn Allah"

Wnaan wayar itace mafarin ƙaddararsu ita da shi din.

Jikinsa na rawa ya miƙe kira yakeyi " mussa lafiya , kina ina, kina inane faɗa mun"

A ina zatace masa tana nan, batasan gurin ba banda baƙin jeji n da akazo aka yar da ita,

Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun kawai yake kira, barin komai yayi ya fice ya shiga motarsa suna wayar

ZABEN TUMUN DAREOù les histoires vivent. Découvrez maintenant