ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 26*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE.
Har wata hajijiya ce ta riƙa ɗibansa, har kamar baya gani, zubewa yayi akan kujeran falon yana maida numfashi!
Habeeb! Habeeb kuma? Yaushe habeeb yafito zai masa yankan ƙauna?
Yaushe habeeb yakeso ya rabashi da farin cikinsa?
Ɗan adam mai wuyar gane hali!
Idan ance habeeb zai iya haka zaice ƙaryane, amma yau ga zahiri ( ko me yayi?).
Umman khulsum ce ta fito ta ganshi cikin wani hali, daf dashi ta zauna ta dafa goshinsa, taji zafi rau
Cikin faɗa tace " kai wai lafiyarka kuwa kazo ka zauna. Nan jikinka zafi kadde har yanzu kana tare da wnaan halin naka na ɓoyon rashin lafiya"
Cikin murya irin ta majinyata yace
" Umma dn Allah kiji wai khulsum aure zatayi ta tafi yarona"
Umma ta dubeshi cikin kulawa tace " taje de tayi aurenta wanan ba damuwan mu bane yaro kam zata bar mana shi"
Wani sanyi yaji ya ratsashi har zuciya
" Yauwwa nima dai haka nace umma"
Zai sake magana ummansa ta ƙaraso gurinsu tana cewa " ke mamana kada ki yarda ku fara abinda bazai yiwu ba"
Umman khulsum tace " yaya meye bazai yiwu ba ɗin"
Ummansa tace " wai abar muku yaro, a ina zai ajiyeshi"
Kabeer yayi caraf yace " gidana zan kaishi mana na ajiyeshi"
Umma tayi wata dariyar, takaici kafin tace " au har kanada wani gida da za'a iya riƙe maka ɗa? Ina matar take? Kaima yaushe kadena zuwa nan kana raɓe raɓen cin abinci balle wani ƙaramin yaro innocent wanda baiji ba bai gani ba, wanan matar taka ce zamu ɗauki ɗa mu baka dn bamu da hankali tariƙe, toh kama farka indai mafarki kakeyi yaro gun uwarsa zai zauna da ubansa, dn habeeb ubane gareshi"
Yadda ta sake haƙƙiƙancewa akan maganar ya sake nuna masa da gaske take, wanan karon jikinsa laƙwas yayi, duk yadda umman khulsum taso gyara abin umman taƙi fir!
Ita da ramlatu har abada!adua takeyi kuma Allah ya rabasu da ƙwallon mangoro su huta da ƙuda, seta nunawa kb kuskurensa akan affan zata bashi mamaki, wanan shine hanyar warzanashi ko zaiyi zuciya yasan meke masa ciwo.
Wasa wasa maganar habeeb da khulsum ta kankama, ta ɓangaren khulsum bawai tsabar tana son auren bane kawai de sotake ta nunawa kabeer uwa tanada iko da abainda ta haifa, bayan haka tanason bawa ɗanta tarbiya ta gari ba watsatstsiya ba irin ta ramlat dayake ikirarin zai kai ta rike masa ɗa, ko karen hauka ne ya cijeta bazata taɓa damƙawa ramlat ɗa ba yaushe ta tarbiyantar da kanta bare ɗa, ɗan ma ɗan wani wanda kuma ta tsaneshi take gaba dashi, shima yasan bai ɗauko zancen gaskiya ba kawaide son affan ne ya rufe masa idanu.
A bangaren habeeb yaji yagani zai auri khulsum dn taisaya mata dayake da kuma karamci irin na mijinta da kyautatawar dayayi masa kafin ya bar duniya, bai damu da zantukan yan uwa ba wai shi saurayine zai auri bazawara har da ɗa, mafi yawan mutane kuma suna zargin wai dn kuɗi yakeson yayi aure, wanda ba haka zancen yake ba, kawia de su mautane daman baa iyyyan musu komi kayi se anyi magana, mai kyawu ko marar kyawu ne, kawai kayi abinda zai fishshe ka.
Babu ɓata lokaci umman kb ta tura habeebu yaje gaisuwa can tofa inda aka karɓeshi hannu bibbiyu, saide haj tofa sunyi magana dashi ta sirru wanda bai faɗawa kowa ba, yana dai tunanin abin, yana lissafin yanda zai amshi abinda hajiyar tazo masa dashi.
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...