ZAƁEN TUMU 7

352 122 5
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 7*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Wani kallo RAMLAT din tayiwa IYATU sanan tace " dagaske?

Iyatu ta ƙyaɓe baki kafin tace " ki zauna nan ayi babu ke, da ke aka ce miki tayaya nake zaune da irin wanan tattauran mutumin, mai shegen gaddamar tsiya, an gaya miki yanzu ana zama haka?

Ai dn na lura ke matsoluwa ce shiyasa ma bana saki cikin harkokina kina bani mamaki ramlatu"

Ta katseta " iyatu RAMLAT"

Tace " toh jaraba ba RAMLAT, naji, Ni mamaki kike bani kamar bani iyatu bace na haifeki, kika tsotsa nonuwana ba, halinki saike,"

Shiru RAMLAT tayi tana tunanin abinda mahaifiyarta ta tazo mata dashi zuciyarta tana wasi wasi, ta yarda ta amince ne kokuma ta ƙi amincewa hakan.

" Salami alaikum wai ana sallama da RAMLAT inji KABEER"

Muryar wani yaro ta amsa kuwwa acikin gidan, mikewa RAMLAT tayi ta wanko fuskarta, ta bulbula turaruka ajikinta ta shinfiɗa wani zabgegen hijabi, ɗan kwalli kawai ta zizarawa idanunta, dn tasha jin ana cewa kwallin asalin na kajol yana fito da kyawun kwayar idanunta, wanda hakan ki rikita mazaje da dama.

Ficewa tayi cikin azama,

Yau da wata galleliyar jar mota, kirar kamfanin marsandi ya zo, tanata walkiya, wani sanyi taji yan ratsa zuciyarta, a hankali ta buɗe kofar ta shiga ta zauna kamshin turaren ta ya gauraye motar, ya lumshe idanunsa yanajin wani abu na tsirga masa, ya ayyana aransa " wanan shine  true love"

Murya a sanyaye yace

" Babyna wai har yanzu fushinne?

Ta ɗan turo bakinta cikin shagwabar data san zata kassarashi da ita

" Kb ya bazanyi fushi ba, tashin hankalina shine na rasaka a rayuwata, ko wata ramin sanadin kwacewaka ko rabani dakai, kasan harka da yaran masu akwai Ni ba yar kowa ba, kila tafini komi shiyasa nake tsoron rasaka"

Kansa ya ɗan dafe yanajin haushin Khulsum da Affan wanda ya jawo masa wnaan masifar

Cikin rarrashi yace " inajin dai RAMLAT kawai so kike ki wahalar min da kanki, bayanin nan nayi miki shi tun jiya nake fama, UMMUKHULSUM ƙanwatace, yar kanin babana da kanwar mamana, tazo karatu nan Abuja , mukaje ɗaukota a airport shikenan fa, dn Allah ki kwantar da hankalinki, bata kaiki komi ba balle ta fiki, kuma wallahi bata cikin irin tsarin matan da Ni nake so, kisani bana ganin wata a duk faɗin duniyar nan wacce ta wuce ke, ki kwantar da hankalinki KABEERU  TOFA nakine har abadin abadina..... Da kb yasan abinda wanan kalmomin zasu haifar masa agaba da bai furta su ba daya janye kalaman sa tun wuri ya taunesu ya haɗiyesu.

Wani far fari tayi da idanunta haɗe da wani murmushin nasara, tasan ta gama da kb sede uwarsa ta haifi wani.

Hanunsa yakai zai riƙo hanunta, ta ɗan ja baya a razane, tana cewa " um um baby kar muyi haka, karka zamo irin mazajen nan da suke son taɓa jikin yan mata tun kafin akaiga aure"

Wani birgeshi tayi, yakuma ji kunya, wanan itace mata, tabbas yayi Sa'a samun ire iren su RAMLAT sai an tona,

Yayi kasa da kai

" Afuwan gimbiyata , duk acikin rarrashine hakan wai"

Ta katseshi " toh kar ka kuma ba kyau dn Allah babyna kaji, ka bari har mu mallaki juna ko?

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now