MACE MUTUM WRITTERS ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 23*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE.
Kowa yanada masaniya Allah bai barin wani dn wani kuma dukkanin yayi farko tabbas yanada ƙarshe.
Kabeeru ne agaban hajiyar tofa yana ƙanƙe da yaro affan a hanunsa, kamar ba zai badashi ga kowa ba ko nono se uwar tayi da gaske yake badashi abashi, yaro yayi wayo kuɓul kuɓul dashi, wani abin mamaki tamkar kabeerun ne ya haifeshi duk da kuwa kama da yakeyi da mahaifinsa jini baya ƙarya daman.
" Yanzu kabeeru ashe har haka ka dawo? Ace matarka batazo tayi gaisuwa ba dan uwanka na jini ya rasu batazo nan tamana gaisuwa ba, lokacin rasuwar mahaifinka tasaka gaba kuka yi tafiya kacemin harkar kasuwanci zai kaika ashe ƙarya kakeyi, me kakeso rayuwarka ta zama kabeeru, tun kafin auren yarinyar nan fa kake ta mana ɗiban albarka, ka watsa mana ƙasa a idanu"
Kabeeru dai shiru yayi dn yasan shi mai ɗumbin laifi ne, laifi ma kuma mai girma sosai, sede har yanzu akwai wani dayake ji agame da ramlatun sosai , soyayyarta da wani abu kuma dayakeji kamar shakku ko tsoro, sede wanan karon yanaso ya farantawa yan uwansa, kodon ɗan uwamsa daya tafi ya barshi wata rabuwa data sanya shi cikin ruɗu da tashin hanakalin da baijinakwai ƙarshensa, sanan yadda yakeson wanan yaron baiji akwai wani abu da zaa sanyashi yayi domin yaron nan ya ƙiyi, son yaro affan ya shafe kowa harda ramlat da kan kansa duk da irin son dayake yiwa ramlatun da kan kansa, dama Allah ya iya kama mutum da duk hanyar daya so.
" Hajiya kiyi haƙuri zaa gyara, kuma zata zo insha Allahu"
Daganan hajiyar batace komi ba, se tace " kaje miƙa mata yaron zai sha nono ka bi ka ƙan ƙameshi"
Rai a ɗan bace yace " hajiya ni ba yanzu yasha nonon bane"
Ta taɓe baki kafin tace " zaka kaishi ko kuwa?
Ahankali ya soma takawa, ya ratsa ɗakin datake, tana zaune cikin hijabi karatun quarni takeyi muryarta na rawa da kuka,amma hakan bai hana sautin muryarta yin daɗi, ba, ya mance rabonsa dashi kansa ya karanta quranin ma, balle yajishi acikin gidansa, ya ɗauki lokaci mai tsawo yana saurarenta, yana tsaye da jariri a hanunsa, yaro fahad ya tsanyara kuka ya katse musu abubuwan dasukeyi dukkansu, da sauri ya miƙa mata shi yana cewa " gashi ki bashi nono na koma dashi can sashe na"
Ta amsheshi ta ɗora bisa cinya, ya na tsayeƙyam a kanta, saita ɗago idanunta ta dubeshi, ya ce mata " yaya dai kin zuramin ido ummu ki bashi nono mana"
" Katsaya akaina taya xan bashi nonon
Aai lokacin ya tuna ma ashe tafiya yakamata yayi, ya ɗan juya baya ya fice yana cewa " yana gama sha a kawomin shi"
Bata banshi amsa bama, bin bayansa tayi da kallo dede lokacin idanunta ya zubo da kwallah, ganin kabeer na daɗa sanyata tunowa da ya affan ɗinta, wai yanzu shikenann ya affan ɗinta baya nan bazai taɓa dawowa ba har abada kenan shikenan, hmmm da in an mutu ana dawowa da kowa baiyi kuka ba.
***************
***************Da misalin ƙarfe biyu na ranar sukayiwa garin tofa dirar mikiya, kowannensu idanunsa saye da wani ƙwamemen gilashi, da wasu mayafai da ake kira " fan ɗarinka tsirara"
Tabbas kuwa fan ɗarinka tsirara dn kuwa duk tsirarar suke, anyi musu iso cikin gida, ramlat dakyar take taka ƙasa wai gidan datti🙄🙄🙄🙄🙄, ta manta asalinta, mafi yawan lotuta ɗiyan talakawa futuk! Idan sun sami duniya suna ɗagawa fiye da ɗiyan masu kuɗi da kulum ake tuhumarsun, ɗiyan talaka sunfi kowa iya ƙasƙantar da mutum duk da dai wai ance wake ɗaya ɓata gari yake.
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...