Barka da sake saduwa acikin wanan sabon littafi nawa mai suna ZABEN TUMU, wanda wata fada ce ta Hausawa na kan zaben abu marar kyau cikin rashin sani, littafin nan zaiyi magana ne kan wanke zargin da duniya takeyiwa diyan masu arziki, da yadda mace zata kwato zuciyar mijinta daga hanun matan da suka rayu cikin kissa da barikanci da duniyanci, da muggan asiri,har ila yau zai taba bangaren maza masu ra'ayin auren mata masu kyau bawai neman zabi nagari ba agun Allah. Nayi wanan rubutu ne dn nishadi da fadakarwa, kuma labarine kagagge dana rubutashi shekaru 10 da suka wuce tun banda wayo sosai, yana kundin rubuce rubuce na, na dauko na kakkabeshi, domin ku da kaunar da kuke ma littafan, dn naso na huta amma damuwarku tasa nace bari na fitar muku da wanan koma yaya dai, da babu gwara ba dadi toh muje zuwa.
Nayi alkawarin typing duk sanda na samu iko, se ayi hakuri da yanayi, wanan littafin salonsa mai saukine, kuma ba lallai yayi yawa ba.
Allah amfane mu da duk abinda zan rubuta.
FARKON FARI
Wata babbar Jeep Prado ce ta kutso kai cikin unguwar da akafi mata lakabi da "getto area" a unguwar KARMO dake garin Abuja, sosai me tukin motar yake cikin nishadi, yana jujjuya sityarin motar cikin kwarewa, da kyar motar ta kutsa cikin wani matsatsen layin, ta ja ta tsaya a kofar wani sakwarkwataccen kofar gida, wanda ginin katangar duk ta rushe, an dan sa tampol an yane katangar, direban ya dubi wanda yake zaune a bangaren mai zama banza yace masa " Affan mun iso fa, I can't wait to see her"
Wanda aka kira Affan ya saki baki cikin mamaki bai zaci haukar amininsa har ta kai haka ba, ya dubi kangon dn bai dauki wanan gida ba, ya dawo da dubansa gareshi yace " kB like seriously?"
Wanan wata sara ce da Affan din ke amfani dashi in yanason Karin bayani ko kuma yanaso yasan gaskiyar abin.
" Yes i AM damn serious"
Idanu affan ya kafeshi dasu, mamaki ya isheshi hakan ma ya hanashi magana.
Wayarsa ya dauka kirar samsung ta karshen kudin, bugu daya ya sameta " baby ki fito mun iso"
Cikin mintuna goma ta fito, Affan ya zuba mata idanu ta gilashin motar Ba abinda yace cikin zuciyarsa sai " fatabarakallahu fa ahsanul khaliqeen"
Kyau iya kyau ya ganshi ayau mace tamkar aljana, farace fat! Har wani ja jaja takeyi, doguwar zar da ita, bata da muguwar kiba batada muguwar rama, fuskarta na dauke da idanu manya kuma farare tas! Girarta cikakkiya, ta mallaki dogon hanci mai kyau pointed nose, kirjinta acike taf, kugunta ma Masha Allahu, itace dai asalin coca cola shape da maza suka jarabtu da ire irenta, duk da mayafin data yafa hakan bai hana Affan bin kwakkwafin surarta ba, sai daga baya yayi istigfari ya dan kauda kai, bude kofar wanda aka kira KB yayi ya fita jikinsa har wani mazari yakeyi, da murmushinta ta doki ganinsa, tuni zuciyarsa ta narke kamar yadda kankara ke narkewa idan taji zafi, a Dan kunyace ta gaida shi
" Ina wuni yayana Ashe zakazo?
Tagama maganar tana wani fari da idanunwanta, fari irin wanda kilakai ne kawai suka sanshi, mafi yawancin matan mu na gida basusan da ire iren wanan kallon ba, ( hmmmmmmmmm)
Bayan dan gyaran murya yadubeta a wani narke yace "RAMLAT LIMAN yaya zanyi bazan zo ba bayan kin sace zuciyata kin gudu da ita, nakasa sukuni"
Yar dariya tayi mai daukar hankali kafin ta dan matse murya tace " hmmm kada ka kodani da yawa, Ni ban isa satar zuciyar Sarkin samarin duniya ba"
Shima dariyar yayi tare da gyara tsayuwarsa ajikin motar yana wani lumshe idanu kamar majiyin barci
A hankali ya furta mata " har kinfi haka babyna
Daga cikin motar Affan duk ya kosa, so yake su tafi dn akwai abubuwa masu muhimmanci da abbansu ya tura su suyi, amma yazo ya shashance anan, shikam bai gano alkhairi ba acikin wanan abun. Bude kofar yayi, ya fito , wasu kudaje suka tashi duuuuuuuuuu! Kamar a matattarar abatuwa.
Cikin kyankyami ya fito ya isa inda suke, warin kwatami duk ya hanashi sakat,
" Amma dai ka manta da aikin da Abba ya samu ko?
Muryar Affan ta katsesu, idanunta ya hadu dana Affan yayi saurin kauda kai, azuciyarta yana cewa a'uzubillahi minashshaidanilla'inun rajim"
Se alokacin KABEER ya farga da lokaci, ya dubeta yace " ga aminina Affan"
Cikin ladabi tace " ina wuni amininmu"
"Lafiya "
Affan ya amsa a takaice, yana duba agogon dake saye a tsintsiyar hanunsa, ya kara dubansu yace " pls ku hanzarta"
Sanan ya juya zuciyarsa cike da tashin hankali,dn RAMLAT ta tsoratashi bayason mace irin haka, sam bai ji ta masa ba, bayan tsananin kyawunta akwia wani boyayyen shaidanci daya lura tana manne dashi, bazai taba baro amininsa ya shiga wnaan tarkon ba ( abinda bai sani ba shine MATAR MUTUM KABARINSA ce kuma duk abinda ALLAH ya tsara saiya auku).
A gurguje tayi mata sallama kan zai dawo gobe, bude motar yayi ya bude yar dirowar dake manne da gurin mai zaman banza, ya zaro dami damin kuɗi na Naira dari biya biyar guda biyu, da wata leda yar karama, ya mika mata, ta tsaya tana dubansa cikin tuhuma,. Fuska a dan kwabe yace " karbi mana"
Ta dan ja baya kadan tana cewa " a haba dai wanan Toshin yayi yawa fa"
Sake dame fuska yayi
" Ki karba dn Allah baa maida hanun kyauta baya, duk wanda yayi hakan toh shi shaidan ne"
Cikin dan jin tsoron abinda yace ta amsa tana cewa " dagaske?
Ya gintse dariyarsa dn ganin ya tsoratata, " dagaske ne wallahi,"
Ta dan narke " tohh insha Allahu bazan kuma maida hanun kyauta baya ba, kuma Nagode Allah ya Kara budi, Allah Kara arziki"
Wani dadi ya rufeshi, yanajin tabbas ya samu abinda yake mafarkin samu tuntuni, burinsa yana hanyar cika.
Sallama sukayi cikin shauki kafin su rabu.
Tafiya sukeyi kb sai babatu takeyiwa Affan wanda hankalinsa baya ma kansa har Saida ya zungureshi da gefen hanunsa yace " wai lafiya dai kuwa Affan?
Affan din ya dan dubeshi yace " amma dai ba aurenta zakayi ba ko?
Wani birni kb ya jaaaa wanda yayi sanadiyar hankado da Affan gaban motar har ya dan bige, saura kadan su bugawa wata motar dake gabansa, na bayansa kuma da badon ya kauce ba shina da ya buge su,
Cak kb ya tsaya ya dubeshi yace " banason maganar banza Affan wane irin ba ita zan aura ba, me zai hanani aurenta meye ainun RAMLAT tell me, tell me I am all ears"
Mamaki ya cika Affan wai daman akan maganar Tata ne kb yaja wanan birkin zai kashesu akan Turi kut! Lallai abin ya girmama,
Ta ina zai fara masa bayani har ya fahimceshi, tunda abu yayi nisa haka nan.
Dubansa yayai a sanyaye yace " kafin ka kashemu mu isa gida tukuna sai na maka bayani kayi hakuri"
Da kyar ya rarrasheshi suka nufi inda aka aike su din daganan sukayi gida.KABEER TOFA kenan da AFFAN KADAGE Aminan juna na kut da kut. Kuma masoyan juna na tun yarinta sede bamusan me KADDARA ta tanadar musu ba!
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...