ZAƁEN TUMU 34

351 61 13
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 34*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Jikinta har rawa yakeyi, data iso bakin ƙofara ɗakinsa, wnana shine zuwanta na biyu, bata taɓa shiga ba,

Na farkon yace ta zo takai affan ɗakinsa ya kwanta, ya mika mata hanunsa a bakin ƙofa ta kaishi ya kwanta sai ko yau da luba ta sanyata yin abinda bata ttaɓa yi duk rayuwarta, yau ta shiga ukunta ta ina zata fara?

Ta jingina kenan, a bakin kofar tana dogon tunani, taji kamar motsi, a bayanta, tana tunanin ko luba ne ta biyo bayanta, ba shiri ta faɗa ɗakin da sauri , yana kwance, idanunsa a rufe tamkar mai barci, ta tsaya ta kasa komi.

Kamar daga sama taji yace " baby come nd massage my head pls"

Wani abu ya tokareta, jin shiru ya sashi buɗe idanunsa ya ɗan dubi gurin da take tsaye, mamaki ya kamashi sosai,
" Lafiya dai?

Ta danyi diri diri kafin tace

" Zak....ka....yi... Wanka ne?

Idanunsa ya ɓuɗo sosai dn ya gaskata zancen dayake ji,

Cikin shakku yace " khulsum wanka?

Ta sadda kai kasa

" Ehh wanka, zan hada maka ruwa ne"

Wanan karon tashi yayi ya zauna, duk da ciwon kan dayake ji yana damunsa dn tsantsan tunani.

Saita shige banɗakin, masha Allah ta ambata, banɗakin yayi mata kyau matuƙa komi a mai kyau saide rashin tsabtarsa, cikin zafin nama ta soma wankewa har saida ko ina yayi tas tas, sanan ta haɗa ruwa mai ɗumi cikin kwamin wanka, tasha ji umma na cewa tun yana yaro yafi so a tara masa ruwa mai dumi ya shiga asa abin kamshi yayi wankansa.

Abubuwan wankan gashi nan birjik a kan wani katon shelve, masu tsada,ko ita mace bazata gwada masa abubuwan gyaran fata ba.

Ta gama ta fito duk ta ɗan jijjiƙe, bata kalleshi ba tace " na haɗa ruwan wankan"

Ta fice dn zuwa sauya kaya.

Har ta fita yana mamaki,

Ya daura towel ya shiga banɗakin, mamaki ya kamashi komi fes fesse ƙamshi dayake tashi, ruwan wankan nasa ya duba, har sha'awa ya bashi,

Ya shige ciki yana mai lumshe idanu, ruwan yayi masa dai dai yadda yakeso, ga kamshin bath foams na tashi, ya ɗan daɗe kamin ya fito, daga bayen , ya ƙara tarar da wani abin mamakin, jallabiyane mai dogon hannu fara ta fito masa dashi, tare da wani dogon wandonta ta feshe da turare ta ajiye bisa gado.

Yana sanya kaya ne ta shigo, tayi saurin juyawa, tana. Cewa " yi hakuri bansan kaya kake sawa ba, abincinka na jiranka"

Ya biyo bayanta dn sauri har ta isa kan tebur ɗin,

Ta soma zuba masa tuwon shinkafa miyan busashen kuɓewa dayaji kifin haɗejiya, se ta zuba farfesun cow tail a gefe ɗan dai dai, ta tsiyaya masa ruwan lemon abarba mai lemon tsami aciki kaɗan.

Kamshin kaɗai ya kusa ƙosar dashi, ta nemi guri ta zauna, yana ci yana jefa mata hira, bai taɓa jin daɗin abincin ba irin na yau,

Ya gama ta kwashe komi,zata bar gurin yace

" Umma ta matsa wai se annema miki me aiki kema, tunda ramlat ta samu me yi mata ayyuka me zuwa da dawowa, ke tace ta kwana zaa kawo miki"

" Tohhh"

ZABEN TUMUN DAREDonde viven las historias. Descúbrelo ahora