MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 40*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Ulaysha Prison (سجن عليشة) Riyadh Saudi Arebiyah.
Wata babvar fursuna ce da kasar saudi suke kambama ta da tsaro mafi tsanani, mafi yawancin wanda ke wanan fursuna mutane ne da aka yake musu hukuncin daurin rai da rai ko ko kisa, ko dai wata azaba mai tsanani, mafiya yawancin wanda aka kama su da hodar ibilis nan ake kaisu kafin a yanke musu hukunci mafi muni, wanda kisa ne ta hanyar sare maka kai da HAUNIzaiyi, wanan zai nuna maka kasar bata wasa da duk wanda yayi gigin shigo mata da ƙwayoyin maye ko duk wani abu daya shafi maye.
Yadda aka rikoshi har abin tausayi, duk ya sauya kamarsa, wani dɗaki aka ɓude aka hankaɗoshi ciki, dakin yanada rangwamen hanke, tsabar azaba baya iya ganin komi,
Bayan tafiyar jamian tsaron ne yaji an ɗagoshi an zaunar dashi, ruwa aka soma bashi, sanan tsohon ya dogara ya ɗauko wasu tarkace ya zauna ya soma goge masa ciwunkan fuskar tasa, ya kuma bashi magani, sanan ya shinfideshi.
Se barci mai nauyi ya ɗaukeshi.
Farkawar da zaiyi duk jikinsa yanna masa ciwo, da ƙyar ya tashi.
Daidai nan aka wurgo musu kwanon abinci, abinci ne mai kyau, kaji, shinkafa madara da kuma kayan fruit dangin pear da tufa.
Abincin tsohon ya tura masa ya soma ci kamar zai haɗa da hanunsa, saida ya gama yq soma maida numfashi
" English? Arabiya?french? Africa?"
Tsohon ya jefo masa tambaya,
A hankali yace " english nigeria"
Tsohon ya tsura masa idanu sosai, kafin yace " hausa"
Da wuri habeeb ya gyada kansa
" Inajin hausa baba kaifa?
Tsohon yayi murmushi kafin yace " kwananka biyu kana barci, ka tashi ka shiga bandaki kayi alwala kayi sallah tukunna"
Wani daɗi habeeb yaji kamar zai kasheshi yasamu bahaushe ɗan uwansa, toh amma mai ya kawoshi nan?
Dn azaba a zaune yayi sallar bayan ya idar ya soma kwallah yana adua na neman ceto gun rabbi.
Har ya gama tsohon namasa kallon ƙuru.
Ya juye ya dubeshi yana cewa " baba nagode kwarai"
Murmushi yayi
Kana ya tambayeshi " meya kawo ka nan?
Shiru habeebu yayi snaan ya soma da cewa " na taho lafiya ƙalau daga nijeriya, ina zuwa nan aka buɗe jakata saiga hodar iblis kuma wallahi baba ni bansan da ita ba, ni danazo taron ƙarawa juna sani daga kamfanin danake aiki mai ya kaini tallar cocaine"
Tsohon yace " ayya yaro u have been framed( an maka maƙarƙashiya), hala kanada maƙiya acan ko?
.habeeb ya furzar da wata iska mai ɗumi yana tunano wasu abubuwa, yadda matilda ta dage kan tafiyarsa dakuma murmushin daya hango a fatar bakinta, wani murmushi daya san idan tayishi toh fa kayi kuka da kanka, baya raba ɗayan biyu itace ummul aba'isin shigarsa wnaan hali tunda ta gano bazai bata haɗin kai ba kenan acuci BKs.
" Hukuncin kisa ne ya hau kauwunan gabaki ɗaya"
Habeeb ya mike a razane yana cewa baba munshiga uku innalillahi, innalillahi, yaya xamuyi kenan?
ESTÁS LEYENDO
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...