MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 38*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Yau ɗin wani wa'azine ta maida hankalinta tanaji na wanna babbar malamar da africa take taƙama da ita wato malama JUWAIRIYYA JOS, mace wacce tayi fice gurin nusar da mata dn me suka zo duniya , su ɗin su waye ma?
Yau wani wa'azi ne da malamar ta tsage akkan JAZIBIYYAH, wanda a turance ake ma laqabi da MAGNETIC FORCE, wanda hausawa suke ce ma KURAR ƘARFE, wanan wani wa'azi ne da sai macen data gama zamowa shashasha, itace bazata ƙaru dashi ba
(https://www.facebook.com/100050587064941/videos/151005376845664/) ga link na wa'azin dm girman Allah ku kalla ku saurara, wmaam zai canza rayuwar mata da dama insha Allahu
.Yau khulsum din ta samu wata irin ƙwarin guiwa da azama, na sosai da sosai, wanana bayani kan jazibiyar tasa ta gano ashe abin bama a kyau yake ba, halittace kawai in kayinwasa da halittar da Allah yayi maka ta jazibiyya toh kai kaso kuma zakaga ba dai dai ba
.Yau tun safe ta tashi da gyara gidan baki ɗaya, sashensa ta shiga ta gyara tsaf, tasanya kamahi na turaren wuta na chad da gimbiya ta aiko mata wnaan kyautace ta musamman dagagimbiyar zuwa gareta, tare da wata farar humran da namiji bazai iya gujewa ƙamshinsa ba komin taurin kansa, sai su turaren wanka, da kulacca ba irin wacce ta saba gani ba da ake saka mata lotion kayita gumi in ka shafa,. Ita wnaan da madarar turare akeyinta da wasu itatuwa, tunda aka kawo kayan kamshin ya cika ɗakinta ya kama ɗakin kuma tun bata ma ɓudesu ba, a zuciyart ata riƙa rayawa tana cewa ko ita gimbiyar wace irin macece? Tayi alƙawarin zuwa takanas dn ta ganta dai wani lokacin.
Abinci ta ɗora, nanma ta ingantashi yau abimcin dayafi so ta dafa masa , jollof rice da ɗunƙulen nikakken naman rago aciki, sai salad na dankalin hausa, da kuma sobo, tayi masa wani samfari na daban, hakan kuwa yanada nasaba ne da jin ta'aliƙin da shek albani gombe yayi wanda akema laqabi da " BARDEN SUNNAH" yayi bayan ita malama juwairiyyan ta gama nata waazin, inda ya ke nusar da mata kan kiyaye abu uku gurin yin abinci, na farko
" Sanin abincin da miji yafi so, na biyu gyara wanan abincin da tsarashi yayi kyau yayi daɗi, yayi ɗanɗano, na ukun shine ƙare abincin akan lokaci bba sai yunwa ta gajiyar da shi maigida ba, tabbar abubuwan nan guda uku suna tafiya a jere idan daya bai samu ba sauran ba zasuyi tasiri ba"
Yadda gidanta ya rikice da ƙamshin abincin da kamshin turare sai ya bada wani samfurin na daban.
Wanka tayiwa yaranta sanan tayiwa kanta wankan da bata tabayin irinsa, tayi kwalliya cas da ita, abin baa cewa komi.
Sai gabanin magriba ya dawo.
Kamshin ne kawai ya jashi tamkar raƙumi da aƙala, har sashenta.
Zuciyarsa tayi masa sanyi da ɗaɗi ganin iyalinsa cikin kwanciyar hankali da kuma tsafta.
Farhana ya soma ɗauka ya rungume sosai yana maida numfashi, affan ma ya zo dagudunsa ya rungumeshi, sanan itama khulsum ta taso ta iso gareshi, ta rungumeshi tare dayi masa sannu da zuwa
Sai yaji duk wata kasala ta sauko masa, wani kyau tayi masa na musamman yau, ga wani ƙamshi ya rasa ta ina yake fitowa daga jikinta da da kuma sashenta da jikin ɗiyanta.
B.salma ta kira ta bar mata yara, ta bishi sashensa,. Ya na tsaye a ɗakin yana mamakin yadda komi ya canza,
Yaji ta iso gareshi, ta baya ta masa wata runguma data sanya shi jin kaɗuwa, ta na masa wani salo maa shafa da bai santa dashi ba duk sai ta rikitashi ma ya rasa yaya zaiyi.
STAI LEGGENDO
ZABEN TUMUN DARE
Storie d'amoreMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...