MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 2*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Daga bakin kofar gidan tayi cilli da salihancin da duk wata kunya data k'irk'ira ta yafa a fuskarta.
Gidan na kunshe da dakuna na kwana guda uku se madafi da bandakin kewaye, ko ina kace kace su ala dole talakawa kenan (illar farko da marasa Hali sukeyiwa rayuwarsu data d'iyan su, wai kana talaka sai tsabta ta gagareka, kudi basa daga cikin cikin sharad'i na tsafta, sede in Kai kazami ne dama can! Kar ayi wa talauci sharri).
Tana yatsina ta shige d'akinta, da gudu bashari ya fyalla sai dakin uwarsa yana haki ya dafe k'ofa yana rattab'o bayani kamar wanda aka sanyashi dole ya fada " iyatu ga can ya RAMLAT"
Yayi saurin rufe bakinsa dn tunowa da bugun da RAMLAT din tayi masa kwanaki kan yace mata ya RAMLAT bai kirayeta da sunan 'yan gayu ba na anty
Yace " ai anty RAMLAT ta shigo da kaya nik'i nik'i tayi d'akinta, wani bak'o ne ya kawo mata su yazo da wata ƙatuwar mota da kyar ta shigo layinmu aradu......
Wacce aka kira iyatu bata tsaya jin karshen zancen ba ta fice tamkar an harba Kibiya, tasan hali, yanzu sai ramlatu ta b'oye abubuwan data samo ba karamin aiki ta bane, bak'in halin ramlatu ba boyayye bane agurinta.
RAMLAT na bubbude ledan taji an fad'o mata d'aki jifff!! Kamar jam'ian tsaro, har Saida zuciyarta ta buga, ta dafe kirjinta cikin tsoro, wani warta iyatu tayiwa bendirin kudin guda, ya yage suka zube a kasa tabisu da gaggawa tana tsincewa itama RAMLAT ta rufa mata baya tana rarumar iya abinda zata samu kamar zasuyi kokawa.
Dayawa iyatu ta samu, sanan ta mik'e tana cewa " wane ke yarinya kinyi kad'an nayi dakon cikinki na watanni tara, na Haifa in Baki nonuwana na tsawon shekaru biyu" tanayi tana bubbuga kirjinta kamar wata yar tasha
" Kishanyesu tas, naci Kashinki da fitsarinki, na shekaru goma, ubanki bai tab'uka komi ba akanki na Turaki makaranta , ki dauko aji in kuma biyan k'udin makaranta, nice tuyar gyada, matsar mai, aikatau, karuwanci ne kaɗai banyi ba akanki, kuma kizo da abin duniya ki shige d'aka, karya kike dan ubanki, ubanki ma yayi kad'an bare ke wata ramlatu"
Cikin b'acin rai RAMLAT tace " Ni iyatu nace ku dena b'atamin suna da wnaan ramlatu, wasu wai raulatu, Ni sunan RAMLAT"
Ta k'are maganar cikin b'acin rai, ta kuma bankawa uwar harara
Wata dariya iyatu ta shek'a kafin ta soma tafa hannuwa bayan ta cuse kudin a cikin rigar nononta wacce ba'a san adadin lokacin data dauka bataga ruwa ba.
Tace " a hayye nanaye Ni merama jikar audu dan buzu, duniya tazo karshe zamani ya ci gaba, a kama rago ayi maka ya kan suna dashi kace Bakaso, toh seki kuma yanka wani ragon ki mana rabon suna inna uwasu me jiki duk tsoka, sannu yar gayu, ubanki talaka ke fad'in rai, gashinan banda limanci da kiran sallah ba abinda ya iya, gayyar na ayya, bazan kiraki da RAMLAT ba sunanki ramlatu nace rammmlatu, se inji duka uwata"
Harara 'yar k'asa k'asa RAMLAT tayi mata ta kau da kai, ta tattare guntun abinda ya rage, tana hamdala da iyatu bataga guntun kud'in da ko zata mutu saita dauka, saboda kwad'ayi da zalamarta sunfi komi yawa acikin halayyarta,
Kawar da b'acin ran iyatu tayi ta cigaba da duba kayan wani zobene ma zinare da kuma wani abun hannu daya sha ado na zircon babban, murna ya isheta duk da kasancewarta d'iyar talaka , wanan bai hanata sanin abubuwan more rayuwa ba, musamman ma dayake ita d'in masoyi yar abin duniya ce, zata iya yin komi kuma dn ta sameshi, idan akace KOMAI toh KOMAI din zata iyayi ciki harda manyan SAB'ON ALLAH! Ba damuwarta bane inda zata samu d'in.
Wanan itace RAMLATU BELLO LIMAN Wanda kawayenta da duk wani dan bariki yake kiranta da RB LIMAN.... Ni kuma na kirata da mai fuska biyu ko kuwa ramlatu kyawun dan maciji. Ko me rayuwa ta tanadar mata oho.
![](https://img.wattpad.com/cover/234330389-288-k196264.jpg)
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...