MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬*ZABEN TUMU 39*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Muryartace ta dawo dashi daga naxarin dayakeyi, yauma NAYLAH
Tana sanye ne da wani leshi mai tsada sosai shima an masa yakan ƙauna an yi dinkin wasu riga da siket wanda sukaci nasarar matse mata ƙugunta gam!
Wayarta ta iphone latest tana hanunta tasaka a speaker da alamu waya takeyi, ya bude mata kofar ta shiga ya rufe
Ya dawo ya shiga ya soma tukata, ko kallonta baiyi ba.
" Darling kana ina ne"
" Ina cikin makaranta baby, kina ina?
Ta ɗanyi harr da idanunta kamar yana ganinta kafin tace " mu haɗu a anan mama mia yanzu zan iso"
Ta katse wayar tana me cewa " i love u too"
Cikin makarantar da skyline uni ya shiga da ita ta kwatanta masa inda zai kaita ya aniyeta.
" Kaje ka dawo nanda awa uku"
Ta bar gurin ya tsira mata idanu harta ɓace ba wai dn tsananin kyaunta ko jikinta mai ɗaukar hankali ba, a'a sai dn kawai yanaji a ransa rayuwarta na cikin garari, tsoron duniya ya sake kamashi, lallai akwai babban nauyi akan iyaye wajen tarbiyan ɗiyansu, shi yanzu ya gane abin bafa bawai a arziki yake ba ko taulaci ba, daga gun iyayen ne, ramkat ce ta faɗo masa rai, baya son tuna komi game da ita, da kuma cin amanar ƙauna da tayi masa, ashe all dis whiledukiyarsa na ɗaya daga cikin abinda ta fi so fiye dashi, lokacin da so ya rufe masa idanu ya kasa fahimtar komi, se yake gani macece tagari ya samu, ko don talaucin iyayenta zata samu tarbiyya ta gari,ashe kuskure yayi maigirma, yanzu ne yake ganin rayuwa, yanzu ne ake masa gwajin imani na ƙeƙe da ƙeƙe, ai shikam yanada labarin bayarwa a duniya!
*********
Awa uku tana cika kuwa ya dawo saide bai sameta ba agurin, yafi minti 49 yana jira, sai gata an riƙota tana ta tanɓele, shi ya zaci ma ciwo takeyi, saida suka ce ya buɗe motar su sakata ya gane abinda ya auku, shaye shaye tayi kenan?Ya tambayi kansa
" Me kuka mata?
Ya daka musu tsawa
Wani yaro mai ɗan tsolon gashi a tsakiyar ka kamar ba ɗan hausawa ba yace
" Kai dallah malam meye na mana tsawa, mu mukace taje ta kurɓi abinda yafi ƙarfinta? Daga cewa tasha ƙaɗan ta zuke dukka"
Sauran suka mara masa baya suka bar gurin duk ɗiyan masu kuɗi.
Bayajinn zai kaita gida acikin wanan halin, yaya iyayenta zasuji?
Sai kawai ya kama guri ya zauna ya zuba mata idanu hankalinta baya jikinta, yana mamakin ɗabiar da matan zamannin nan suka ɗauka ta shaye shaye, abin ko tsari da jinsin su bai yi ba,yana mamaki har wane jin ɗaɗi ne ko damuwar da zata sanya ka shan kayan maye??
Wanan wata tambayace daya kamata ayiwa dukkanin matan da suka tsunduma rayuwarsu cikin musiba ta shaye shaye...Allah ya tsaremu da tsarewarsa.
*****************
Gurin cike yake maƙil da mutane, yan kasuwa da kuma yan jaridu, taro ne da ya amsa suna taro, dayawa sunzo ne dn su tabbatar da abinda Suke zargi ko aukejin jita jitarsa.
Wasu sunxo ne dn ganin ƙwaƙwaf, wasu kuma sun zo ne dn suji yadda zancen hanun jarin da suka saka cikin kamfanin ya tsira ne ko ko dai ya rufta dasu?
![](https://img.wattpad.com/cover/234330389-288-k196264.jpg)
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...