MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 36*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Wanan shafi sadaukarwane ga new baby NANA HAUWA
Kuma sadaukarwa ne ga
Baby girl din kawata YUMMA
( Aisha yusuf)Allah ya raya mana su.
LAMARIN DUNIYA!
Ran ummansa a ɓace ta ke gwada wayar daga bisani tayi cilli da wayar a gefe tana bambamin fada
" Ya Allah yaushe kabeer zai hankali irin na mutane,wai ace tun safiya mutum ya fice yanzu ana kwala ƙiran magriba bai dawo ba, wayoyinsa duk baya ɗauka"
Ummanta ta katseta
" Yaya ta yiwu wani abun ne ya riƙeshi ko kuma ba lafiya ba, amna nasan haka kawai baban nawa ba zai yi komi da gangan bq"
Wata uwar harara umnansa ta zubawa ƙanwartata
" Ah ke kam kabeer na laifi ne gunki?
Har akwai wani abu mai muhimmanci daya shige matarsa da yar jaririyarsa akwai shi?
Umman ta gama tana mai watsa mata tambayar.
Shigowar sageeru ya sanyasu maida hankali kansa
Ya dan risina ya gaidasu, sai kuma ga hqbeebu shima ya shigo suka gaidasu sanan suka ɗauki baby tare da yi mata adua.
Da tayata barka
Ummansa ta tsaresu da tambaya
" Ni ina ogan naku ne?
Sageer ya dubi habeeb
" Yazo office kuwa yau?
" Kai anya kuwa? Ni bamu haɗu ba yau, agun shaheedah ma nakejin haihuwar
Salati ummansa tasaka tana cewa
" Toh ina ya shiga? Tun safe shiru?
Habeebu ne yace " ina yace zaije umma?
Tace " wai fa gidansa zaije yace"
" Bari muje can ɗin mu duba ku kwantar da hankalinku"
Suka barsu cikin mamaki da jimami da tararradi.
Bugun ƙofar da akeyi ne ya dawo dasu hankulansu,
Ramkat ta ja tsaki tana cewa
" Se mutane suna hutawa se wasu banzaye su zo su damesu"
Ganin ranta a ɓace ya sanya ya fara rawar jiki dn wani mugun tsoro da shakarta yakeyi tunda yaje ya ɗaukita da sanyin safiya yana bata baki, shine har ta yarda ta ɗawo ɗin tare da sharuɗda iri iri, ciki harda rabuwa da matarsa!
Ita taje ta buɗe ƙofar , tana watsa musu wani kallo, irin na raini.
Sageer ya fara gaidata
" Rankishidade ina wuni"
Ta amsa a dakile shikam hqbeebu daman jininsu bai gamuwa tun lokacin affan na raye dn ya gano take takenta, sanan yasan halinta sarai! Ya kuma santa da duk kalolin barikancinta.
Fuska a ɗaure yace " maigidan yana nan ne?
Ta ɗan taɓe fuska
" Yana nan menene?
![](https://img.wattpad.com/cover/234330389-288-k196264.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...