ZABEN TUMU 4

397 92 3
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 4*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Jamsy ta lailayo wata Ash'ari ya ta zuba, baki na karkarwa tace " banson karya RB"

Daga Daya bangaren RAMLAT tace " bantaba miki karya ba aminiyata, kizo Kisha labari kawai".

Cikin yan mintuna jamsy tabrank'ayo tana sauri kamar zata kifa,

A yagalallen d'akinta ta samota tayi baza baza da ita dama gwanar k'azantace, RAMLAT dai nacikin matan nan da sai za'a fita za'a nemi soso da sabulu ayi wanka, in an fito a shafa hodar fankeke, a zuba turare, ana yauk'i ana gwalli, idan an dawo gida a kwanta a dak'in tsumma.

Jamsy ta nemi gurin zama tana ya tsina fuskarta tana cewa " Allah ya yaye miki wanan muguwar k'azantar RB , mace har mace a waje amma a makwancinta babu kyawun gani, ina tausayawa wanda zai dauki wanan k'ajagar"

Ta tsuke bakinta bayan tagama maganar wanda ya zamto mata al'ada,

RAMLAT ta bud'e dara daran idanunta kyawawa kamar na barewa, ta motsa d'an bakinta kamar batason yin magana tace " hmmmmm ki iya bakinki kina magana da matar ceo ne fa na kamfanin BK"

Sororo jamsy ta dubeta kafin ta matso sosai tana rage murya

" Lasamin inji aminiyata"

Tar tar RAMLAT ta bawa jamsy labarin mai cike da ban mamaki, wai bafillace ya fadawa matar ubansa yace " kaji rabo".

RAMLAT ta kwace mata mafarkinta, idan kyau ne itama tanada shi, ga tsarin jiki mai jan hankali wanan yasa ma take tsaka da ganiyar karuwanci ta yana kai mata ko kuwa Allah kadai yasan adadin mazan data kwanta dasu, mazan data mori dukiyarsu, mazan data rabasu da matayensu na sunna , tasan ita shaidaniyace ta ajin farko, amma wani abin mamakin RAMLAT tafita Sa'a, takan samu komi cikin sauk'i ne, batare da tasha wata wahala ba, sab'anin ita da saitasha wahala kafin take samun abinda takeso.

" Toh yanzu me ake ciki kun had'u ne?

Tayi mata wanan tambayar dn duk a rud'e take, ta manta ma ta ce yazo gida

Cikin sigar harara tace " bansani ba , mutumin dana ce miki yazo hargida kuma kina tambaya mun had'u?

Ta k'are maganar cikin jin haushi

Jamsy ta d'an wake

" Au au na manta toh ya kukayi d'an hanune ko kuwa?

Da sauri ta katseta " ke wanan ustazu ne aradu, ba maganar ahashanci ta kawoshi ba, da aure yazo"

Jamsy ta lailayo wani Ash'ari ya ta kunduma " dan abu ta kazar ub****ki, yaran masu kudin nan har wani salihancin ke garesu, kyau yagani yazo ya dan dala, ki bada kai bori ya hau"

Dariya RAMLAT tayi dn ta gano hassada kawia kawarta keson mata idan da sabo ta saba, tasan ita mai Sa'a ce shiyasa ma halin jamsy bai damu ta ko kadan

Dafa ta tayi, cikin shu'umanci tace , " wanan karon na aure ne yazo jamsy, aure zanyi insha Allahu baizo da wasa ba kuma nima a salihance zan bishi mu tafi ahaka, bazai taba ganewa Ni mai FUSKA BIYU BACE!......

Wanan kenan .





**************************************************************

Affan ya rungume Alh kabeeru da Alhaji Bature yana kwallah yace " Abba's Allah ya bamu ikon rik'e muku amanar da kuka damk'a mana, Allah ya kauda din abinda zai kawo mana son zuciya ko don kai, Nagode Nagode da kokarinku gareni, Allah bani ikon zama d'a nagari wanda zakuyi alfahari dani ko bayan ba raina"

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now