ZAƁEN TUMU 8

305 80 12
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 8*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Man ladan ya miƙe da ɗan carbinsa, zai fice, man liman ya dakatar dashi

" Man ladan akwai Magana mai muhimmanci da"

Man ladan ya dawo, ya zauna kusa man liman, ya ajiye dogon carbinsa a gefe, ya zurawa man liman idanu yanaso yaji wanan muhimmiyar maganar, Allah Allah yake yaji ko taimako aka kawo na abinci ko kuɗi, dn ya tashi baida ko sisin kwabo.

Maganar man liman ta dawo dashi daga dogon tunanin daya faɗa

" Man ladan inaso muhaɗa wani ƙulallen zumunci ne na har ABADA, Ni man liman nabaka auren ɗiyata ramlatu, kaje ka shirya cikin sati Uku masu zuwa azo a ɗaura aure"

Wata irin zabura ladan yayi a rikice ya soma cewa

" Man liman anya kuwa naji mai kake faɗa, ban gane kan zancen ba Ni ladan ɗin ko wani dai"

Ya soma waige waige dn bai san koda wani ladan ɗin akeyi bada shi wanan ladan ɗin ba mai neman rufin asirin ALLAH.

Ganin zai tara musu jama'a  man liman ya ɗan janyo shi ya zaunar dashi ya bari ya matsa

Kafin yaci gaba

"Sanin kanka ne akwai aminci da yarda a tsakaninmu mun wuce abokai saide yan uwa, agurin baka auren ramlatu tamkar rufin asiri ne gareni, wanan hallayar taya datake neman zubdamin ƙima da mutunci ya isa haka dole na dakatar da ita, ita ba karatu ba ba aiki ba, se yawon banza da wofi, kuma kai shaidane na irin tarin samarin dake cincirindo akofar gidana, kuma duk bana aure, shin zan zuba idanu na ga ɗiyata kwal ta lalata rayuwarta ne? Bazai yiwu ba dole ne  na aurar da ita ga wanda zaiyi hakuri ya zauna da ita kuma kaine na yarda dakai nasan ko bayan babu raina kai me iya riƙe iyalainane babu ƙorafi, dn Allah ka taimaka ka amince"

Wani sanyi guiwar man ladan tayi, maganar gaskiya shine abin nan da kamar wuya wai gurguje da auren nesa, ina shi ina  ramlatu, yarinyar data raina kowa, marar kunya, ga tara samari, ga kwaɗayi, ga uwa uba rashin tarbiya, sanan ga tsanin kyau dayake sanyata izza da girman kai, ko wata yar gwamnar albarka, shi kuwa talaka mai fafutukar yau da gobe kuma Sa'an ubanta, tsoho dashi , badon Allah bai bashi haihuwa ba da yana zaton zai haifi kamar ta shima ta ina abin nan zai yiwu,

Toh saide kuma girman man liman agurinsa da kimarsa bazasu bari ya watsa masa ƙasa a idanu ba, dakuma rai da kwaɗayi wa zai ga mace kamar ramlatu yaƙi shanshana? Babu shi ko don tsananin kyawunta dole mutum ya ruɗu da ita ya fitinu da ita.

Liman ya dafa shi yace " nabaka kwana uku kayi tunani"

Hankalinsa ya dawo gareshi.

Murya a sanyaye yace " tohh man liman, Nagode se kaji yadda ta kaya bayan kwana ukun"

Sukayi sallama kowa ya shiga gida.

**************************************************************

Party ne wanda ya tattara ɗiyan wane da wane, mawaki Don jazzy da tawagarsa ne su dija, su korode ɗan Bello, da sauransu suka haukata gurin nan da wakar " doro bucci"

Ba abinda kakeji sai bakin matasan nan da suke maka wakar, yayinda mawakiya dija ta amshi ragamar filin

" Doro  bad, double o seven, doro na yaro, we get money, doro like for  do anything , wey doro like for do, make no body try doro cos dey go wound wooo"

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now