ZAƁEN TUMU 14

366 70 10
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 14*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

"Menene aibun khulsum kabeeru?

Muryar hajiyar tofa ta karaɗe gurin cikin wani amo na maida martani,

A tunanin kabeeru wanan itace damarsa ta ƙarshe na mallakar ramlat ɗinsa kuma ya rabu da ƙaya ya huta

Kawai ya rufe idanunsa ya soma kushe khulsum ɗin da duk iya kaifin bakinsa,

" Hajiya khulsum batada adadin kyawun danake bukata ga matar da zan aura"

"Khulsum batada irin wnaan tarbiyar danake buƙata"

" Khulsum yar masu kuɗi ce nikuma yar talakawa nakeso mai hankali da tarbiya, wacce zata darajta kowa nawa, wacce zata tarairayeni, wacce zata riƙe talaucinta ta godema duk abinda na bata ba wacce ta saba da kuɗi ba , wacce............

Wani tafin hanune ya kifawa bakinsa mari har sau biyu, umma ce jikinta na rawa zata soma dukansa dn takaici , umman khulsum ɗin ta riƙota gam tana ceewa " haba haba yaya meye haka, yanzu kabeer ɗin zaki daka da girmansa?

Hajiyar tofa ta dubeta tace " kash kash

Meyasa kika hanashi ƙarasa zancen cikinsa, meyasa kika katseshi?

Cikin fushi abbansa yace " hajiya sai ta barshi ya gama rashin mutunci, a gaban iyayensa , yagama cin fuskar yar uwarsa agabanta ?

Hannu hajiyar ta ɗaga almar kowa ya dakata, wnaan faɗanta ne dn kuwa kabeeru da ita yake, dama tun can akan wnaan ne bata shiri dashi, ya cika raina halitta wanda hakan ba abi bane mai kyau, tun yana yaro ya soma wnan tsurfar, bazatace basu bashi tarbiya ba amma dai yau ɗin kabeer ya nuna mata tarbiyar bata isheshi ba, zata gyara masa zama kuma sannu a hankali, dn bazata bari wani
Ƙaramin alhaki ba ya wargaza mata zumunci da haɗin kan data ɗauki shekaru tana ginashi, tanaso ta nuna wa kabeer khulsum nada wata irin daraja da ƙimar da bai isa ya samo mace kamarta ba ita tasan wnaan, kuma sirrine agurinta shiyasa takeson tamasa gata tayi tuwona maina, amma tunda yaƙi bazata matsa ba, sede zata masa DAURIN TALALA, tanaso taga ZAƁEN TUMUN nasa , dn tasan bazai wuce tumun da damina bata masa gata ba, ya faɗi ƙasa , shikuma kabeerun ɗan tsautsayi ya ɗaukeshi baisan fanko bane, tarasa meyake damun yaran yanzu da ƙin barwa Allah zaɓi, kayi magana suce zaka musu auren dole, idan ka barsu kuma bazasu dauko nagari ba sai ƙyalƙyale banza, ba ga mazan ba, baga matan ba.

Alƙawari ɗaya tayi shine bazata taɓa yiwa wani ahalinta auren dole ba , dan tasani hakan babban kuskurene, tasani haramun ne a musulunci.

Gyaran murya tayi zata soma magana

Muryar affan ta katse ta
" Hajiya ni inason khulsum"

Wani murmushi hajiyar tayi, ta dubi affan lallai affan yaro ne mai sa'a, sa'ar ma ta gasken gasken, tun yana yaro haka yake, dukkan lamuransa na rayuwa Allah na sauƙaƙa masa su sosai, irin mutanen nan ne da ake kira masu sa'a , komi zasu samu suna samunsa ne ba tare da wani wuya ko wahala ba.

Jin hajiyar tayi shiru, khulsum ta sanya wani kuma mai ban tausayi tana cewa hajiya wallahi banason ya kabeeru nima na tsaneshi, mugune azzalumi ne, ni ki ban ya affan shine me sona baya tsangwamata kum......

" Yi mana shiru marar kunyar banza"
Cewar ummanta

"Kaji wani hukunci fa gacan marar kunyar banza can, babban banza, marar hanakali , ba a gurinsa ta koyo hakan ba, ki barta ta magantu dn Allah"

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now