ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 19*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE.
Bayan watanni shida
SAUYI
Twin house no 2
Daga bakin ban ɗakin yake yana mata sannu, se kelaya amai takeyi, harda kwanciya, daga ƙarshe shigowa yayi kawai, ya cicciɓota tana gocewa dn kada ta masa amai a jiki amma ina! Warin turarensa dolce nd gabana me suna the king ya sake bugar hancinta taji ya shiga cikin kanta, tuni ta soma kwararo amai, jikinsa ya soma rawa ganin ta galabaita har kamar ta sume, da kyar tace " tura......r.....r ..eee ....nn..ka, ba...na .....sossoo"
Ruwa ya zuba mata, sanan ya cire kayansa da nata din ya ajiye, ya wanke jikinsa ya canza jallabiya, itama ya ɗauko abaya yasa mata, ya ruƙota ko rufe gidan baiyi ba ya kama hanyar asibiti, abinka da masu maiƙo, cikin gaggawa taga likita akayi gwajin maleria, dana ciki, na maleria ya zamo - na ciki ya zamo +, "shikenan affan zai zamo abban baby"
Cewar dakta shuraim wanda ya ke zaune kan kujera me jujjuyawa, gabansa tari fayil fayin ne na majinyata, se babban teburi daya rabasu dashi, kunya ta kama ummukhulsum, ta sadda kai ƙasa, affan kuwa harda sujudushshukuru dn nunawa Allah godiya, yau wai shine zai mallaki ɗan kansa, ya rungumota yana cewa " nagode mussa ta nagode, Allah saukeki lafiya, Allah ya baki lafiya"Ta amsa a kunyace ameen yaya affan"
" Well well, babyn is 12 weeks, yanzu se a kiyaye a na barinta ta huta, tanacin abinci banda aikin wahala har zuwa wata biyar , zamu bata magunguna akula da shansu, zancen amai kuma se a hankali zata bari"
Dakta shuraim ya katsesu.
Affan ya mikawa dakta hannu yana cewa " mungode doctor , sai kaga tukuicin ka, bari muje pharmacy ku amshi maganin"
Sukayisallama dashi, ya riko ta kamar zai mata tafiyar, har saida idanun mutane yayi yawa akansu ganinkaffa kaffa dayakeyi da ita
A hanyar gida hanunsa cikin nata ƙyam! Kamar zai naɗe ta, gidan ummah yakaita, yace zaije aiki ya dawo, kallon farko umman ta gano yar ta na ɗauke da abin arziki, murna fal cikinta, duk setaji damuwart game da kabeeru ta ragu, dn tana cikkn damuwa matuƙa, wani abu mummuna ya faru da ɗan nata TILO!
" Ki ajiye wanan kwanon kizo ki zauna nan laraba ta kawo miki abinci me kikeson ci" cewar ummah
A kunyace ta dawo ta zauna
Tace " ummah yunwa nakeji amma bansan me nake so ba"
Umman ta dubeta cikin jin daɗi tace " dama haka abin yake bari na nema miki abinda yafi dacewa dake"
Ta miƙe ta shiga kicin da kanta,
Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa ta haɗo mata faten tsaki me ɗan tsami tsami, da kunun koko shima me ɗan tsami tsami, ta ajiye mata" Toh bisimillah yar ummahh kici me isarki"
Zama tayi kuwa ta shanye komi tsaf har tanaji kamar bata ƙoshibama, dn dadi, ta daɗe bataci abinci ba har haka, kulawar da ummah ta bata setayi mata daɗi, har barci tayi sosai bayan tasha magungunanta.
Sai gabannin magriba ta farka ta tashi tayi sallolinta, wani faten yana jiranta, da kunun tsamiya, dama ta tashi kamar anyi yasar rijiya acikinta,
Ta zauna kenan zataci abincin suka shigo, idanunsa ya sauka a kanta sai yaji wani sanyi, suka yiwa juna murmushi, ta daɗa jawo mayafin abayarta ganin ba shi kaɗai bane, inda take zaune nan affan ya zauna ya soma tayata cin abincin shima,
![](https://img.wattpad.com/cover/234330389-288-k196264.jpg)
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...