MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 15*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Ina neman afuwarku najina shiru da kukayi.
Wayar tatace ta damu jamsy da ƙara,
Tana tsaki ta daga wayar da nufin katseta , ganin sunan ya sanyata kwalawa ramlat ƙira,
Ta fito har tana tuntuɓe , dn jin irin ƙiran datayi mata na ban tsoro
Daga wanka tafito dn tsoro har jikinta da guntun kumfan sabulu, ta isketa
" Lafiya jamcy, menene ya faru? Waya mutu"
Wayar jamsy tamika mata wacce take ta tsuwwa, ta amsa taga sunansa, jikinta a ɗan sanyaye ta ajiye wayar ta juya tana gunguni
" Aikin banza, na ma zaci wani abun ƙwarai ne ma wallahi"
Taja tsaki, jamsy tabi bayanata tana masifa
" Malama ban gane me kike nufi ba da hakan, kimin bayani dalla dallah ki?
" Bayanin me zanmiki bayan abinda kika gani"
Jamsy tace " me nagani kuwa anan banda rashin hankali irin na mata"
Tana sanya rigar mama ta katse , idanunta cikin na jamilar tace " dawowar AMBURSA na ya wargaza komi, ya wargaza kowane lissafi da tanadi danayi shine kawai abinda nakeso ki gane"
Cikin mamaki da shock jamila ta dubeta, ta ƙaraso gabanta tana dan bubbaga mata fuska, alamar tashin mai barci
" Hala dai ramlat bacci kikeyi, ko kuma can gun iskancin naki kika ɗibgo shaye shaye?
Jamila ta saukar da murya dn rarrashi saboda bataso rashin hankalin ramlat ya jawo musu babbar hasara, hasara irin wacce mai rai yakeyi idan tashin ƙiyama tazo na bai tara komi ba na daga lada dn guzurin can.
Hanunaa ta riƙo, tana cewa
" Baby i told u ki rage ɗiban jaji, your brain is to small for that, haka ranan kikaje kika shaƙi abinda yafi ƙarfinki, kiyi a hankali fa, banson kanki a kunce fa"Yadda jamila ke magana ne ya daɗa ƙular da ita sosai, setaga kawai wani sabon salo ne na raina mata hankali da ajawali.
Tace ta mai fizge hanunta da riƙon d ajamin tayi mata
" ba abinda na sha da hankalina nake wnaan maganar, na rufe shafin kabeeru saboda kin san abinda nake ƙauna ya dawo, bayan haka lokacin danake tsananin buƙatar sa ya ina? Ina ya gudu ya barni? Seda nayi jinyar zuciyata, na mance komi sanan se ya dawo yace min me?
Gabanta jamilar ta iso ta tsaya idanunta cikin nata
Tace " ban taba ganin wawuya irinki ba, waye ya faɗa miki a bariki ana soyayyar ƙwarai? Har wata yarda kake bawa ƙadangaren bariki? Yai tsawon shekarunki nawa da ambursa ɗin, ya yi maganar aure?
Ta katseta da wuri
" Ai yace ƙudin aurena yake nemowa ni matar manya ce, dole saida kuɗi"
Jamila ta tuntsire da dariyar takaici tace " u see ur self, u re a fool ramlat, ke banza ce wallahi, shifa ambursan da kansa yace miki ke matar manya ce bazai iya riƙeki ba, se ya nemi kuɗin dn yasan kalarki, ke kuma ga ready made yazo nemanki da auren kina jiran gawon shanu! Kina jiran tsammanin mai naƙuda da batasan abinda zata haife ba, like seriously
ramlat?
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...