ZABEN TUMU 22

300 63 6
                                    

ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 22*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE.

" Ka taka birkin sosai ɗan uwa"

Shine abinda kabeer yake faɗawa affan ɗin daya rikice yana cewa " the brake has failed, baya ci birkin fa dan uwa, we have been framed, wanan wata maƙarƙashiyace, idan bamu rayu ba, Allah ka dubi bayanmu, idan ka rayu ɗan uwa ka kulamin da iyalina da iyayenmu"

Daidai lokacin motar tasu ta bugi wata babbar mota, tayi wani gefe motar ta cika da hayaƙi, kuma ta wuntsila saman gada ta faɗo.

Mutane sukayi tururuwar zuwa ceto rayuwan mutanen da abin ya shafa amma saide kash! Yawancin wanda abin ya shafa Allah ya ɗauki rayuwakansu, cikin yan mintuna, haka Allah ke ƙudurarsa idan lokacinka ya ƙare toh tabbas baza'a taɓa ƙara maka ba, saide faran Allah yasa mu cika da imani.

Asibitin zankli ɗin dai aka kaisu abun babu kyawun gani, dayawansu basa numfashi, wasu sun ƙone, dn faɗowar da motar tayi kan mutane ta kawo kuma ta kama da wuta.

Cikin hukuncin Allah mutum ɗaya ne bai jigata ba, sosai duk da yaji ciwuwwuka amma Allah baisa wnaan shine sanadinsa ba, an basu taimakon gaggaaa wanda suka rasu aka sanyasu cikin akwatin ƙankara kafin a gane yan uwansu.

Suna cikin ɗakin sai murna sukeyi, sun ƙanƙame yaro, khulsum tanata raba idanu kozataga maigidan nata amma shiru, kai tun tana kawaici har
Ta dubi shaheeda ta yafito ta, dai dai kunnuwanta ta raɗa mata " ina ya affan?

Zatayi magana , sageer ya shigo jikinsa yana rawa, umman kano yace ta biyoshi, suka fice tun daga nan jikin kowa yayi sanyi, gaban khulsum ya daɗa tsananta bugu, haka kawai taji bata yadda da zuwan sageerun ba ta kasa natsuwa, itama umman hankalinta ya kasa kwanciya, saita miƙawa mai aikinsu ɗan yaron , ta bi bayansu umman da sageerun,

" Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sageeru meyake faruwa damu ne?

Muryar umman kano ke tashi cikin kuka, da sauri umma ta iso garesu tana dafe da ƙirji, tana cewa " meke faruwa ? Meya faru mamana?

Cikin kuka sageer yace " hajiya oga affan da oga kb ne sukayi hatsari"

Salati ta somayi murya a sama

" Suna ina? Karkace mun sun mutu suma,nashiga ukuna"

Sageer yana matse ruwan kwallah yace muje suna can nima ban sani ba kirana akayi, naga fitansu oga affan yana waya ma yacemin zasu taho nan an samu ƙaruwa, ina tahowa nima kawai naga mummunan haɗari ashe sune, muje ku gansu"

Yawuce gaba suka bishi, suna koke koke, kabeerun suka gani wani ikon Allah raunukan jikinsa da sauki sosai kan na saura, sun gama dubansu ba affan, sunyi cirko cirko sega habeebu ya shigo shima ya iskesu ya isa gurinsu yana cewa " haj yanzu aka kirani fa wai sunyi hatsari"

Ya dubi sageer yace " suna ina,?

Sageer yace " ga oga kb amma bamuga oga affan ba"

Wata nas habeebun ya tsare yana tambayarta a rikice, cikin tausayawa tace "kuje macuwari akwai gawawwaki acan kila yana can ɗin"

Ta kare maganarta cikin jimami da tausayawa, da kuma ƙarfin hali, da gudu gudu suka bazaba, macuwari,

Gawar farko da suka ɓude ta affan ce wanda ya ƙone, takalmansa da zobunan hanunsa ne suka shaida musu wanan affan ɗinsu ne, ai tuni umma tazube agurin tana kurma ihu, se sambatu takeyi tana cewa " Allah muntuba ka yafemu mai mukayi mqka haka Allqh, me muka makaAllah dan Allah me muka maka dazaka mqna hana, na rasa mijina bance mqka komi ba nayi shiru, na rasa kanin mijina ɗan uwana bance komi ba, kuma yanzu ka ɗaukemin ɗan danafi so nafi ƙauna ɗan da yafiye min abinda na haifa, baka gani ba matarsa ta haihu ko ɗan bai gani ba seka daukeshi haba hqba hqba!"

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now