MACE MUTUM WRITTERs ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 29*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE.
Abubuwa dayawa sunzo sun shuɗe, shuɗewa na har abada, makaddarin Allah mai aukuwane a koda yaushe, duk wani abu da aka rubuta a lauhil mahfuz saiya faru dole saide ko idan maiduka ya sauya hakan.
Ba komi bane agurin Allah mai arziƙi yadawo ƙasƙantacce, talaka kuma ya koma attajiri nagasken gaske.
Haka lamarin Allah ya kasancewa the tofa's wani abin mamakin da kowane ɗan adam yagani dole ya tsorata, an wayi gari the tofa's basuda komi, duk wani gini da sukayi ya rushe, komi ya lalace, basuda komi sai Allah, bisa wani babban dalili wani dalilin da bazasu taba mantawa ba cikin rayuwarsu. Abinda ya tada hankulansu, sanadin daya nuna musu maƙiya da masoyansu na ainihi ƙalilan,inda suka gano tarin maƙiyansu da dama, sukaga sha'ani irin na ɗan adam, irin na mutum, wani sha'ani me wuyar fassara mai kuma ban tsoro, ashe dukiya ake bautawa, ashe dukiya aka fiso fiye da ran ɗan adam, ashe arziƙi shi akewa bautar ma a duniya lallai Allah abin tsoro mutum ma abin tsoro wanan shine kullum abinda hajuyar tofa take cewa.
TOFA
Yana zaune a gaban hajiyar ya natsu yana jinta
" Haƙuri akeyi kabeeru akan dukkanin abinda ya sami bawa, ita rayuwar da kake gani fa duk jarabawa ce, idan ka ɗaga hankalinka matarka da yaranka kuma suyi yaya? Iyayenka mata ma ai duk zasu sare, kana buƙatar jajircewa da jarumta sosai har ka kai ga gaci"
Ya ja wata doguwar ajiyar zuciya, wadu ƙwallah na zubo masa, da zaace masa rayuwa Zata koma haka zai ƙaryata, sai ga hakan ya afku kamar a mafarki, duniya ta zamo masa makaranta, inda ta sanyashi cikin babban aji wani ajin da zaiyi wahala ya ci jarabawarsa balle har ya fita.
Ya share ƙwallarsa yace " zanyi iya ƙoƙarina naga hakan ya yiwu"
Ta dafa kafaɗarsa, tace " karka bar haƙƙinka kacigaba da gwagwarmayar nemansa, ko bama raye"
Ya gyaɗa, kai yace " insha Allahu kuna raye mazan ƙarɓo abuna"
Murmushi kawai tayi tace "yaushene tafiyar taku kanon?
" Zuwa jibi, shi sageer ɗin ne ya nemamin gun zama da kuma wani ɗan aiki haka kafi Allah ya kawo ɗauki"
Ta nisa tace " da ummuu ɗin da yara zaku tafi"??
Ya amsa " ehhh saboda karatunsu ba, zanje nayi aikin da zai taimaka mana"
" Allah ya bada sa'a,Allah ya tsare"
Ya amsa da ameen.
Sashensa ya nufa, ya samu khulsum na koyawa yaran karatun qur'ani, daga bakin ƙofar ya tsaya , yanajin duk yadda sukeyi da mahaifiyarsu, yaro affan ne yake tambayar mamansa da cewa
" Mami meyasa muka dawo nan garin dukkanmu, bama zuwa makaranta kuma motocin abba ma duk babu, abbanmu baya zuwa office?
Batayi mamakin tambayar nan ba dn tasan affan da masifar wayo da ƙwaƙwalwa da kai mai kaifi, iliminsa yasa akeyi masa tsallaken aji tuntuni, yana daga cikin irin yaran nan da ake kiransu da "gifted child" , ƙwanyarsa mai kaifi ce.
Ɗan murmushi tayi tace masa " Allah ne yake mana jarabawa affan yanaso yaga kwatankwacin imaninmu ne gabaki ɗayanmu shiyasa aka ƙwace mana komai, yanzu zamuyi rayuwane irin ta wacce wasu da kuɗi zasuyi, kafin Allah ya yanke mana wahalarmu, kuma fa Allah zai iya barin mu a haka har abada, dama shine me azurtawa kuma shine me talautarwa"
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...