MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 6*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
SABUWAR RAYUWA
A washegarin ta shiga wata sabuwar rayuwa mai cike da ƙaddarori marasa adadi,
A gurguje tayi karin kummallo, ta shirya komi tsaf, cike da fargabar zuwa sabon gurin,
Tazaci Garba direba ne zai kaita, sai ta sameshi a zaune yana karin kummallo,
" Man Garba bada kai zamu tafi bane, nayi latti fa"
Ta k'are maganar tana duba agogon dake daure a tsintsiyar hanunta na kamfanin vincci, kalar fari, wanda ya zauna kan dan madaidaicin hanunta,
Ta tsaya tana dan gyara gilashinta tana dubansa cikin k'agara
Garba direba yace " haj ai inaga oga ne zai kaiki, gashi nan a jar motar can"
Ta dan zaro ido "oga?
Ya gyada kai cikin rashin kulawa bare ya gano rud'unta har yayi mata k'arin bayanin da zata fahimci waye ogan.
Cikin saib'i ta soma takawa ta isa motar, tun fitowar ta yake hangota yanata k'wafa, saib'inta yasa yaji haushi, ya kamashi, gashi dama RAMLAT ta sakashi a kwana, duk akanta, jiya ko barcin kirki baiyi ba saboda fitinar RAMLAT, ga yana sauri zai fita ummansa tace sede ya kaita makarantar sanan ya jirata tayi abinda zatayi sanan ya dawo da ita ya wuce inda zaije, daga karshe ma de umman nasa se tace Affan yaje yayi masa duk abinda zai gabatar ɗin, wanda shi kuma Affan din ma ba haka yaso ba, amman ummah firr taki, yasan tanada nata dalilin wanda bai wuce karfafa zumunci ba, da kuma sanyasu sabon dole, wanda shi bai bukatarsa badon komi ba sai dn sam Khulsum din bata masa ba, ganinta yakeyi a sahun ire iren matan da basu mishi ba a rayuwarsa , shikuma irin mutanen nan ne basu iya b'oye abinda baiyi musu ba, sanan basu iya b'oye abinda suke matukar so ba, saida yasan dole ya sassauta dn ummah bazata kamu ta ba.
Yana irga dakika sunkai 120 kafin ta iso motar, kasancewarta tint baida tagane ko wanene ba, har Saida ta bude mazaunin gaba, tashiga ta zauna, ta juye suka hada idanu, har yanzu dai yana wayar
Tayi kasa da murya cikin fargaba tace " abbana ina kwana muntashi lafiya?
Kwarjinin ta ya sanyashi amsawa har ya mance yana wayar da ake masifa akanta,
" Lafiya mamana alhamdulillah"
Ya amsa mata, sanan ya kunna motar suka fice daga gidan,
Ganin zai raba hankalinsa biyu ya sanyashi katse wayar , yanata tunanin jidalin RAMLAT, abin ya daga masa hankali amma ya birgeshi kuma dn shi mutum ne mai son yaga an damu dashi matuka ana nuna masa so da kulawa, tsananin kishin RAMLAT ya sanyashi jin lallai fa itace zaɓin Allah.....
*********
Wurgar da wayar tayi akan gado tana huci, tayaya za'ayi ma wata tazo ta shiga gonarta , ai ita ba'a mata haka, tanaso idan tanada abu toh ya kasance nata ita kadai, shiyasa ko yawon iskancinta datakeyi ba'a mata kishiya, sede in ta gaji dakai ta Barka ta kama wani, mutum d'ayane yake taka mata burki, wanda ra'ayinsa ya sanya ta fidda rai kan wata aba wai soyayya sai zuwan kabeer ya dawo mata da komi danye har tanajin zata iya aurensa, a bangaren ta auren kabeeru shine zai sadata da cikan wasu burirrikan na rayuwarta burika masu dimbin yawa wanda take kasashensu babu dare babu rana, tana so ta tara abinda ko mai tashen kudin nahiyar Afrika bai tara ba, tanaso taganta cikin daula maras karewa, tana so tayi hanun riga da talauci, ta tsani talauci takance talauci masiface, tasan ita ba kalar gidan talauci bace hutune ya kamaceta.
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...