ZAƁEN TUMU 45

283 59 7
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 45*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

"Abba"!!!!!!
Sageer ya daɗa daddagewa ya kirayi sunansa, datijon ya juyo ya dubeshi, cikin mamaki yace " sageer?

Sageer ya karaso yana gyaɗa kai yana ƙwalla, ya rungume abban yana kuka, karfin hali irin na abban baisa yayi kukan ba, sai rarrashin sageer dayakeyi yana bubbaga bayansa kamar ƙaramin yaro, shikam habeeb mikewa yayi ya zuba musu idanu cikin mamaki. Har suka gama, sageer ne ya dubi habeeb yace masa
" Oga habeeb wanan shine Alh kabeeru tofa DG na kanfaninmu"

Idanu habeebu ya gwalo , se yqnzu ya gano kamarshi da shaheedarsa, ashe wai tun tuni yana tare da sirkinsa ne a garƙame a kurkuku bai ma sani ba, ko ace dukkansu basu da masaniya?

Ikon Allah ya wuce wasa!

Takawa yayi a hankali ya zube a kasa yana gaidashi " abba ina wuni?

Abban ya shafa kan habeeb yqna cewa kabeeru wanan yaron dan albarka ne, mutumin kirki ne, a dan zamana danayi dashi na fahimci hakan ban san da mai zan saka masa ba"

Sageer ne yaɗanyi murmushi kafin yace " abba toh ai habeeb shine ya auri shaheedatu"
Abban ya buɗe baki cikin mamaki ya dafa. Sageeru yace
" Wai wace shaheedatun?

Sageer yace " shaheedatu de tamu ta gida, yanzu ma haka ta haihu"

Ciikin murna habeeb ya rungume sageer yana murna, sai daga baya ne ya tuna ashe fa da surukinsa suke tare sanan ya risina.

Sun zauna sun maidawa abban duk abinda ya faru, sageer ya ci gaba da musu ƙarin bayanin abubuwan da suka faru da basu nan.

Ran abba yakai matuƙa gun ɓaci, bakin ciki ya lulluɓeshi, musamman ma da yaji labarin ta sanadin kabeer abin ya faru, kuma wai ya auri yarsa daya wulakanta , wama ya haɗa wanan auren? Koma wanene zai nuna masa bai isa dashi ba akan ɗiyarsa dayafi so.......

Naylah tayi musu shirin tafiya najeriya cikin kwanaki ƙalilan.

Koda suka isa ɗinma agidan abban nata suka sauka, don su gama shirin da tafiya abujan wanda ta nace sai an tafi da ita, abban ya amince mata dn yanada wani shiri akan ta na mussaman.

Abuja

Yadda kotin ta cika maƙil! Babu wani sarari, wani yanayi ne da baa saba ganin hakan ba, sai idan shariar mai girma ce,mafi yawa yawan bayin Allahn dake gun sun zo ne dn ganin yadda gaskiya zatayi halinta bayan shekaru masu yawa.

Duk an hallara, sede yau ita kadai ta iso gurin, kuma kamar tana cikin wata yar damuwa.

Tawagar alkali ta iso, aka mike akayi gaisuwa.

Kafin aka fara gabatar da shaidu dn dama yau ake shirin kare komi.

Man liman ne ya tashi ya shiga gurin da aka keɓe dan masu laifi ko bada shaida.

Barister luba ta soma sanar dashi ya gabatar da kansa, ya gabatar da kansa, sanan ya fadi abinda take so ya sanar da kotun.

Duk wani hali na banza da kuma shaidar dayasan zata karya logon ramlat toh ya faɗeshi. Ya ƙare yana mai cewa "  a matsayina na mahaifin wanda ta kawo wanan ruɗanin inaso kotu tayi watsi da duk abinda ta fada ta mallakawa mai shi dukiyarsa"

Mamakin ƙarfin hali irin na man liman ya kama mutane, kabeer seda yayi ƙwallah dn tausayinsa lallai albasa batayi halin ruwa ba.

Shaidar gaba da zaa gabatar shine sageer tare da  naylah.

Sun shigo sun bada dukkanin jawaban kan yadda suka tserar da rayuwar habeeb wanda ake ta neman sa dn kusan shaidarsa itace karshen zancen.

Mamaki bai kar kb ba saida habeebun ya fito tukkuna, har saida ya mike dn mamaki.

Labarin da habeeb din ya bayar na tughun da aka haɗa masa har akayi sanadin kamashi ya bawa kowa tausayi, kunya da nauyi ya kama kabeer ɗin, komi dai bai tashi fitoowa fili ba har saida  abba ya fito, hakan ya sa kb mutuwar tsaye, kowa tsoro ya far masa.

Jawabin da abban ya bayar kamar haka ya girgiza kowa!

" Tafiya ta sameni zuwa kasar jubail dn tattaunawa kan wani kasuwancin da muka sa hannu, bamsam ya akayi ba naga hodar ibilis acikin kayana, wanan yayi sanadinnda aka garƙameni a kurkun ƙasar, daga baya kuma suka dawondanin babbsr kurkunsu ta ƙasar saudi, duk wani kokarin da nayi dn na fito abu yaci tura, har ma fidda rai sai kuma Allsh ya jefo da wanan yaron habeeeb"

Guri yayi tsit kaman ba halitta

Yaci gaba" abinda kowa bai sani ba shine nida ɗan uwana mun maida wanan dukiya tamu ma ƙarkashin diyata ummukhulsum tun bayan wani ganawa da mukayi akan ɗansa kabeer dn irin matar daya auro, wanan sune takardun da muka sanya hanun"

Ya mikawa kotu shaida...

Shikenan ta faru ta ƙare anyiwa me dami ɗaya sata.

Hargowar matilda ne ya cika gurin inda tayi kukan kura tqyi kan abban ta shakeshi , cikin ƙaraji tace " karya kakeyi, babu wanda ya isa ya kwace bks a hanuna, baka isa hanani wulaƙanta the tofas ba kamar yadda suka kashemin MAHAIFINA"

Ana ɓanbareta daga jikinsa tana cewa " kasan mr NULAMUGA da kuka kashe kaida ɗan uwanka?

Jikin abba a sanyaye ya dubeta, se yanzu ya gano tsananin kamarsu sosai da mr nulamuga, zuciyarsa ta tsinke matuƙar tsinkewa.

Yanaji a karon farko ya cutar da wani a rayuwarsa ko sun cutar zaice"

Wani zufa ya rika keto masa ,

Hukuncin Alkali na karshe shine kamfani ya koma hanun maishi khulsum saboda shaidu da aka gabatar masu ƙarfi.

Da kyar aka kama matilda wacce taketa ihu da zage zage da tonon asiri, da maganganu marasa kan gado. Dama alhaki  kwuikuyone.........


KARSHEN ZANCE

Yau kimanin wasu watanni kenan da yake zarya, gidan abban, sede kullum yakan dawo ne ba tare da abinda yaje neman ba.

Yauma kamar kulum farhana ce kawai take tare dashi suna wasa take ce masa "abba yaishe zamu tafi gida da mama, ni inason gurinka"

Rungumar yarinyar yayi yana rarrashi, baya zaton zata fahimci halin dayake ciki, ta yaya zai sanar da ita KUSKURENSA ne ya jawu musu wanan lamarin......

Fitowar abban ne ya sanya shi dawowa daga dogon tunanin dayakeyi, ya gaiddashi, fuska a murtuke ya amsa

Sanan ya dubeshi yace " banason yawan zarya in don ɗiyarka ne ka ɗauketa maza ku tafi da ita, tawa diyar da kace naje na jiƙatanasha, ban gama jikatan ba balle har na shanye"

Abban ya juya ciki ya barshi anan cikin matsanancin tashin hankali.

Dafatan kuna lafiya, tafiyar tamu tazo ƙarshe, insha Allah gobe zamu ƙaƙare... Sai ayi mani hakuri dn Allah wani uzuri ne ya tasomin wanda bayaninsa bazai yiwu ba, amma kumin adua Allah ya fitarni cikinsa lafiya.






ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now