MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 5*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Komi lokaci ne, kuma komi da aka sanya masa lokacin zai zo shi komin dadewa, jarabawar Khulsum ta fito taci komai daya kamata, dn haka sai shirin tafiya Abuja, cikin kwanakin nan har wata 'yar rama tayi dn tsabar tashin hankali da mak'on gida, Allah ya sani batasan ta inda zata fara ba, gata ba mai saurin kuka ba bare tayi kukan ko zataji sanyi, ba komi bane yake sanya ta kuka, mutum ce Mai dauriya sosai.
Kayanta take had'awa jiki duk babu kwari, ummah ta Miko Mata wasu kayayyaki da batasan dasu ba,
" Ungo wadannan sababbine na dinka miki su"
Ta amsa tare da cewa " Nagode ummah"
Yanayin jikin nata yasa mahaifiyar Tata zama kusa da ita ta ruku hannuwanta cikin hikima da kwantar da zuciya ta soma kwantar mata da hankali
" Kin san anyi wani lokaci da muka yanke ahawaran mu bayar da ke a umman Abuja, saboda tashin hankalin da ta shiga na rashin haihuwa, da kuma tsananin k'aunarta gareki, wanda muke ganin ko mu iyayenki bamu nuna Miki ita ba"
Dagowa tayi ta dubi umman Tata, ta d'an sunkuyar da kai.
Taci gaba " don Allah Khulsum kisan ruwan sanyi, gida zakijeki babu wani abinda zai sameki, idan kikaje a haka yaya bazata so ba, zataji wani iri, taga kamar ba don ita ta haifeki bane, kuma Kinga dukkanmu dai abu guda ne, yadda take uwa agurinki haka nake, dn Allah ki saki ranki, ki ajiye wnaan mak'on"
Ba shiri ta kakalo wani murmushin da bai kai zuci ba, tace " umma insha Allahu zan sake, kawai de yanzu.n ma kewarki da zanyi ne ta dameni"
Umman ta ɗora hanunta bisa kanta Tana shafawa tace " babu komi muna nan, muma zamuyi kewarki ki kula mana da kanki , halin da muka sanki dashi karki canza, ki tuna duk inda kike akwai ALLAH yana ganin ki"
Ire iren shawarwarin da dukkanin iyaye nagari suke bawa diyansu idan zasuyi nisa da gida shi ummah tabawa Khulsum, tare da jaddada mata girman Allah da hukuncin saba masa a duk inda kake.
Abbanta ma dai nasihar yayi mata sosai wadda ta dan sanyata kwallah.
Karfe biyu na wayewar safiyar ranar suka kaita filin jirgin sama na Aminu Kano, sukayi sallama cikin kewa.
Har ta shiga jirgin tana ayyana yaya rayuwarta zata kasance, ko yaya su yaya Affan suke, dn rabonta dasu tun da sukaje wani hutu a can London a sheiffield, bata kuma ganinsu ba, sai tarin sab'ani da suke tayi da su din, fuskar kabeer tana nan rad'au a idanunta, mugun kallon dayake mata dinan da yawan gwasaleta dayakeyi duk bata manta dasu ba, kaunar da Affan yake mata da kariyar dayake bata a kullum bazata mance ta ba.
Tashin jirgin yayi dai dai da lumshe idanunta tanaji a ranta lallai wata ƙaddara ce mai girma take kiranta a can din........
Haka kuwa abin yake tayi tunani dai dai da abinda aka rubuta mata cikin kuddin KADDARAR Tata, kaddarori masu dimbin yawa da suke buƙatar jajirtacciyar mace irinta.Karfe biyar dai dai na ranar
Affan wanda yake ta gudu yana yanke motocin gabansa, yazo daf da wani soja ofisa wanda yake shirin dakatar dashi , wani ID card ya nuna masa kadai, sojan ya barshi ya wuce, yana mai daga masu hannu tare da washe musu katoton bakinsa, wanan itace kasarmu fa ayau!
Yanda yaja birkin jikinsa har wani mazari yakeyi, har ya fita zai tafi yaga kabeer ko gezau baiyi ba, ya dawo cikin mamaki ya zagaya ya bude kofar motar
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...