MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 12*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
ALKAWARIN ALLAH
"Yaya affan sannu, da gajiyan jirana fa afwan, wallahi mr sherali ne ya bata mana lokaci yau a aji"
Wani murmushi yayi daya sanyata jin tsikar jikinta duk sun miƙe, harda bugun zuciya, sai yau ne taga kyaun nan nasa na fulani, tsaf yake yi mata yanayi ko kama zatace ne da ɗan wasan kwaikwayon nan na hausa yakubu muhammad saide yafishi fari nesa ba kusa ba, affan irin fararen nan ne fat wanda har jaja sukeyi.
Ta sunkuyar da kanta ƙasa dn bata iya jurewa kallon dayake harba mata.
" Wani ya ta ɓa ce miki kinada kyau??
A bazata tambayar ta doketa,
Ta duƙar da kanta ƙasa, tana wani dan murmushi mai kma da yaƙe,
" Yaya affan wasa kakeyi kaima dai ko? Ina kyau ga baƙar mace, gajera?
Fuskarsa a ɗan turɓune yace " kinsan meye asalin kyau?
Ta ɗan ɗago tare da girgiza kanta
" Kwayun zuciya shine asalin kyau, kina kuma dashi, bayan haka ance beauty is in the eyes of the beholder"
Yaci gaba " ni kin min, kuma zakici gaba dayi min har abada, ki dena ɗari ɗari, kema mutum ce, kuma halitta mafi daraja wato mace, believe in your self, ki ɗauka kinada kyau irin naki, kyawun da ba wanda ya isa mallakarsa se ke kaɗai, u are unique in your own way, never ever look down on your self!
Wasu kalmomine na karfafa guiwar duk wanda yakejin bai kai ba, bai isa ba, kuma yayi kaɗan, ko yayakake karka taɓa jin baka kai ba kada ka ƙaskantar da kanka, kowa yanada nasa kyawun halittar yadda Allah yaso ganinsa.
Shiru tayi tanajin wani irin farin ciki na ratsata, ashe har zatayi gamo da irin wanan bawan Allahn, bayan duk irin yadda take jinta wata ƙasƙantacciya kuma hakan ya samo asali ne tuntana yarinta, yanda kabeer yake tsangwamarta yana faɗa mata maganganu kamar " wai zai auri wanan mummanar yar taki umma"
" Ji ta ko kyau batada dashi"
" Baƙa mummuna"
" Da gajarta da ƙanƙanta kamar ruwan aski, ai wanan bazata auru da wuri ba"
Waɗanan kalaman su suka sake nesantata da jin ita watace , ita mutum ce mai daraja, hakan yasa take yawan tsame kanta cikin harkoki na mutane, take jinta a muzance, wataran har tambayar kanta take yi meyasa aka halitto ta haka, idan taga mamanta kyakkyawa, abbanta shima kyakkaywa, taga umman abuja kamar balarabiya, abban ma haka, kabeer kuma duk ya fisu kyawun ma, shida affan suna kunnen doki gurin sura da kyau, hajiyar tofa tasha faɗa mata wai d wata kakarsu hanne take kama, mace mai dattako, da kyawun zuciya, tana sonta fiye da kowa a dangin tofa, tsananin kamarsu da kaka hanne ya sanya hajiyar tofa ƙaunarta fiye da ƙima, tana tuna ranar data yiwa kabeer dukan tsiya da girmansa dn yace mata mummuna baƙa, saida ya kwanta jinya, shiyasa basa shiri sosai, bayason zuwa hutu can, har ya girma abin yabi jikinsa.
Ya katse mata dogon tunanin data faɗa
" Ummkhulsum ina sonki da dukkanin zuciyata, zaki iya son ɗan marayan Allah?
Wat kunya ce ta lulluɓeta, yaya affan na sonta wai ita ita khulsum dai?
Kyakkyawa dashi ga gayu, idan yazo ɗaukarta mata suyi ta kalllonsa, har sai taji wani iri, wasu marasa kunyar har tambayarta sukeyi lambarsa,.
![](https://img.wattpad.com/cover/234330389-288-k196264.jpg)
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...