ZAƁEN TUMU 41

290 62 3
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 41*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

Ulaysha Prison (سجن عليشة)  Riyadh  Saudi Arebiyah.

Daga bakin ƙofar daya turo musu abincin ya juya, ƙasan wani ƙaton biredi habeeb ya ga saƙon abduoulhakeem ɗin wanda har sun cire rayukansu ma daga kan ɗuk wani taimako da zaiyi musu, bazasu san iya adadin watanin daaka ɗauka ba kafin ya amince musu da taimako na ƙarshe.

Rubutu ne na larabci inda abdoulh ɗin ya amice zai taimakawa mutum guda shine habeebu, in yaso idan ya fita sai  shi kuma ya taimaki tsohon dayake faɗa,

Ya bashi sati guda ya rubuta duk wani  abu ko shaidar da yan uwansa na najeriya zasu ganeshi, zaiyyi musu lomi domin Allah , amma ya sanar dasu sai ya nemi hanyar da zai bada saƙon a asirce kada asiri ya tonu, tunda hukumci ne babba, amm shi zuciyarsa ɗin ta addabeshi kan ya taimakawa habeeb ɗin bai san dalili ba.

Haka kuwa akayi bayan kwanaki ɗin habeebu ya rattaba rubutu manya manya yada koma waye zai ganeshi, adireshin kabeeru, da kamfani ya rubuta, sanan wata dabara ta faɗo masa, ya rubuta adireshin sageeru da dukka lambobinsa.

Ya miƙawa abdoul cikin ɗoki da aduoi na samun sa'a.

Wanan kenan.



ABUJA

" Madam dole ke zaki halarci wanan taron fa"

'
Matailda tace da Ramlat,

Wacce yanzu duk tagaji da lamuran kamfanin, saboda tafiye tafiye sun hana mata sakat, ga kullum taro, ita fa batayi zaton haka ma abin yake ba, ta z aci zama zatayi tana yan kan miliyoyi tana hutawa ita da mijinta da yan uwansa da uwarta, tunda yanzu kaf dangin ambursa ta ɗaukosu ta dawo dasu abu 'ja. Ta dan ƙama kowa abinyi, wnaan shine irin kyautayinndatayi.musu dn ƙaunar datakema ɗan uwansu.

Duban matilda tayi kamar cikin harara tace " nagaji gaskiya bazan iya ba, haba kullum mutum kaman ɗan tsuntsu baida aiki sai tashi sama da yawo a kan iska, kisan yadda zakiyi kawai ni bazan iya ba"

Shiru matildan tayi alamun girmamawa a ƙasan zuciyarta kuma murna ne fal!

Bata zaci nasara zatazo mata haka da gaggawa ba, ta zaci wanan ma saita wahala amma ba haka bane abin ramlat zata sauƙaƙa mata komi

Tunda ita kuɗin kawai takeso ba aiki ba, ita kuwa tanason ne taga bk sunnje ƙar! Tayi fata fata da bk saboda wani sirri nata data kudurta, takan ce " i will make u proud father youreffort will never be in vain"

Dan gyara zama tayi ta dubeta tace " hajiya shifa ƙaidar kamfani ba haka yake ba, bazakaci kudin dabakayi aiki tuƙuru kansu ba, wani abu ne wanan sanannne"

Ramlat tace " toh kuwa gaskiya sede asan abinyi ni na gaji"

Ta ɗanja numfashi sanan tace " abinyi guda ne, sede ke ki koma gefe ki zama yar kallo ana kawomiki kuɗin, ki bada muƙaminki na ceo ga wanda kikasan zai iya aikin"

Jim ramlat ɗin tayi, kafin ta dubi matilda tace " wa yakamata na bawa toh?

" Mijinki rankishidade shi yafi cancanta , komi zaizo da sauki shi namiji ne, zaiyi kujiba kujiban tunda ke bazaki iya ba, inyaso duk wani ƙudi sai ya zamo naki ne kina daga zaune zaki cin abinki cikin kwanciyar hankali"

Wanan shawara ta matilda tayi mata daɗi sosai, hakan zatayi kawai ma a huta, tazauna gida ta mike kafafu taci arziki ta barshi a inda yake, yanzu ne zata gyara rayuwarta, ta hayayyafa itama ko dn tsatsonta suci gadonta, saide wanan duk abinda ta shirya ne a matsayinta na yar adam, batasan shirin da ubangijinta ke yi mata ba................shine kuma abunda mafi yawan mutanen duniya basu sani ba.




ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now