MACE MUTUM WRITTERs ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 28*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE.
Yana daga zaune a office gabansa sai dukan uku uku yakeyi kawai, tunaninsa ɗaya kada hajiyar tofa ta watsa masa ƙasa a idanu, dama itace kaɗai MADOGARARSA shin idan ta janye ƙudirinsa yaya zaiyi!
Yadda yakeji a yanzu duk duniya ba wanda ya isa ya hanashi abinda yakeso.
Kiran wayar sageer ne ya katseshi , ya ɗauki wayar
Daga daya bangaren sageer yace " yallaɓai sai bamu ganka ba agurin ɗaurin auren habeeb"
" Wane habeeb yaushe kuka tafi bansani ba"
Segeer yace " ha'a mufa muna TOFA gun daurin aure. Habeeb da ƙan......."
Shu shuu shuuuuuuuuuuuuuu
Wayar ta soma yi na rashin ingantacxen netwrk,
Kb yayi kiran duniya wayar taƙi shiga.
Tuni gumi ya riƙa feso masa!
Hajiyar tofa bata kyauta masa baa, duk da yasan su kawu musa su baffa sule zasu iya hana abinda ya nema ɗin.
Wallahi bazai yarda ba zaijene ya birkice musu har sai sun sa habeeb ya sakar masa mata!( 😳😳😳😳😳😳).
Da gaggawa ya nemi jirgin rana na zuwa kano ɗin. Bai faɗawa kowa ba ya kama hanya, yana isa ya ƙira sageer yazo ya ɗaukeshi.
Ko a mota bai tambayi komi dn baya ma son yaji komi ɗin.
Shima sageer shiru ɗin yayi ganin yadda ogan nasa ya zama kamar wani zaki.
Ya samo ma an wawwatse se tsirarun jama'a,
Fadawa ne suka soma masa ƙirari, ya sa hannu a aljihu ya basu abinda zai basu, yayi gaba , ya gaida sarki, wanda shima ya soma masa nasiha wacce ya kasa gane kanta
" Muhammad kabeer sai ayi hakuri a zauna lafiya ayi adalci tsakanin mata biyu sai kazamo jajirtacce zaka zamo adali, kayi ƙokarin haɗe kan matanka guri guda, dama hajiya tace bazaka zo ɗaurin aure ba se shi ɗaya angon daya nemi ummu ne yazo, akan zakazo da yamma kaima, nina bada sadaki nace a mayar maka da naka daka aiko, Allah muku albarka"
Ya amsa da amin kansa a ɗaure tamau!
Hajiya tajawo masa masifa! Wai wa tasa aka aura masa ma tukunna?
Gumi ne kawai yake feso masa, sashenta ya isa ya samu matan nan kuwa sun masa caaaaa
Ango ango, ga ango ga ango,
A dole yake yaƙe, amma ji yakeyi tamkar zai faɗi, hajiyar tofa ta kanne idanu tace " iye iye kaga angon shaheedah komi dozin!
Wata fargaba ce ta rufeshi, wayaji an ambata shaheeda?
Wai wace shaheedar?
Ɗakin hajiya ya wuce kai tsaye ya faɗa kan gado, wasu kwalla masu zafi suka soma zubo masa, innalillahi kawai yaketa ambata, ko zuciyarsa zatayi sanyi, yau ya shiga ukunsa!
Shaheeda kuma?
Mai zeci da shaheeda ayanzu?
Duk da ta tara duk wani abu da da can yake raayi, shaheedah doguwace zet! Mai kyau da ita, fara tas tas zubin zabarmawa, mutane nace mata ma ta haɗa dangi da larabawa ko yan nijar dn kyau, tanada zafin nama, tanada hankali kuma, kwanan nan tagama makarantar sakandare ɗinta , aka turata nijar karatu ita da shaheed twin broda ɗinta.
![](https://img.wattpad.com/cover/234330389-288-k196264.jpg)
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...