ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 17*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Kamar ance kalli can, idanunsa suka sauka akan wani babban tashin hankali, tashin hankalin da har ya mutu ba zai taɓa mantashi ba,
Da farko ya ɗauka idanunsa ke masa gizo, saida suka matso kuma yaga ray'ayal ayni itace, yanda gayen daya ganshi tare da ita yake latsata yana rungumarta abindai ba kyawun gani, seya firgitarshi, tabbas amaryar dan uwansa ne , bai farga ba har suka bar gurin, da ƙyar ya ja ƙafarsa, ya bude buut ɗin motar ya kwashi kayan abincin da zai kaiwa baƙinsu da suka iso daren jiya suka kwana anan,umma tace ba zaa basu abincin otel ba, wanan shine maƙa sudin zuwan nasa, sai kuma ya tarar da wnaan babban tashin hankalin, matar ɗan uwansa daya ƙwallafa rai fasiƙa ce kuma mazinaciya! Wata zuciyar ta kwaɓeshi da cewa kai affan kaji tsoron Allah shaidar ZINA fa babban abu ne, abind abaka gani ba kada ka idar dashi, wanan shine tsarin islama, wnaan ya ɗan sanya shi jin dama dama duk da zuciyarsa ɗin taki aminta da hakan, saide baijin zai iya barin ramlat ta cutar da su ko da kuwa hakan na nufin karshen numfashinsa zai sadaukar.......
Tafiya takeyi tamkar yar kaciya, zuciyarta baƙiƙkirin ambursa ya wargaza mata lissafinta, jiya yayi mata abinda tunda uwarta ta haifeta bata taba gani ba, duk yawon barikinta, ambursa ya murjeta , ya cinye komi na daga tanadin datayiwa kabeeru dn boye duk wani aibunta, ɗan iskan ya kwashe romon komai, ya rike wuta tun dare har safiya, tana kyautata zaton wani maganin yasha ma dn kawai ya tozartata dn yasan ba yadda ta iya dashi, yanzu ba maganar so akeyi ba, maganace ta yanaso yazo ya ƙarasa ɗaiɗaita mata rayuwa wanda batajin zata lamunta, ai ta bauta masa iya bauta, yanzu kam lokacine na nemarwa kanta yanci!
Banɗaki ta wuce kai tsaye tana ƙwalawa jamila kira, jamila ta taho a sukwane saboda kawarsu gaga tace mata gacan amarya ta shigo kamar bata cikin hayyacinta,
Ta sameta shame shame a bandakin tana maida numfarfashi,
" Lafiya ramlat?
Jamila ta tambayeta
Idanunta jajur ta ɗagosu ta dubii jamila, bakinta har yana rawa tace " AmBURSA jamila, jamila ambursa ne ya dawo?
Wata irin mikewa jamy tayi ta kunduma wata ashariya
" Amma ramlat ke dabbace! Kina nufin kice ambursa ya dawo kin fasa auren kabeerun da aka daura ko kuwa me kike nufi?
Ranta a ɓace tace " nina fada miki haka?
A masife jamila tace " toh meye nufinki? Kina magana da tsoro kamar kinga mala'ikin mutuwa"
" Jiya yayi threatening ɗina ya min barazanar tona duk wani asirina wanda nasani da wanda ban dani bama, dole yasa na miƙa kaina gareshi, yamin kaca kaca ba tausayawa ko kaɗan"
" Kan barauben can! Haka zamuyi da tsinanne! Garin yaya ma yasan hakan"
Jamsy ta kai idanunta gareta dn neman ba'asi , dn bata yarda da mayyatacciyar soyayyar da ita ramlat din takeyiwa ambursa ba
Itama dubanta tayi kafin ta fahimci inda jamilar ta dosa
" Haba jamila kina tunanin zan faɗa masa ne, akan me?
Ramlata da maida mata amsa cikin kwantar da murya.
Jamila tace " waya sani ne kam dn
.........Ta katseta " yanzu meye abinyi jamsy kar mu tsaya ɓata lokacinmu a banza,abinda ya faru ya faru, kinga anjima zaa kaini gidana, idan kb yajini a haka ai kashina ya bushe"
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...