ZAƁEN TUMU 11

340 68 8
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 11*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

ALKAWARIN ALLAH

Cukumar gaban rigar sabuwar farar shaddarsa tayi

" Wallahi baka isa yar tawa zaka aurar ba tare da izinina ba? Ni iyatu  nace kayi kaɗan kayi tsararo"

Ta ƙare  maganar ta na huci, kamar kububuwa,

Dubanta yayi yau a malam bellonsa yace " saboda kece uwata ko ubana, ko kuma kece me iko dani? Ko masu wadannan ikon akaina basu isa tuhumar hukuncina ba akan ɗiyar dana haifa, ke da tunaninki na dabbobi ya baki cewar bazan iya ɗaukar wanan hukuncin ba? Ko kinaga akwia wani boka ko malami da zai hanani wanan ƙudirin? Ko kina ganin yar dana haifa har ta kai gandun da zata bijirewa hukuncina akanta a matsayin uba! Sunan UBA mahaifi mairamu inada ikon komi akan gida, saboda haka inaso ki natsu ki sauke duk wata hauka da kikayi dakonta ko karawa duk hukuncin na baya, idan ba haka ba wallahil azeemu wallahil azeemu aurena dake yazo karshe , idan nace ƙarshe ina nufin komi ɗin zaizo ƙarshe"

Ya yakice hannuwanta da sukayi sanyi a jikin kalar rigarsa, zantukan nasa sun girgizata, girgiza irin wacce duk taurin kanta bata taɓa jin irinta ba, Takoma da baya, ta jingina da itacen gwafar data rike barandar ƙofofin dakuna biyu da suke kallon tsakar gidan.

Ya sake katseta

" Kuma sati mai zuwa za'a kaita gidan mijinta, bana bukatar ko wane irin taro"

Bakin iyatu na rawa tace Malam wa ka aurawa ɗiyata"?

Fuskarsa da wani murmushin wanda bata taɓa ganin irinsa ba yace " MAN LADAN"!

Wani abu RAMLAT taji ya sauko daga sama ya rikito kanta, kamar ginin bene na zamani mai hawa 50 ɗinan, da wnaan kaɗai zata iya kwatanta nauyin abinda taji a rikito a tsakar kanta, ruɗun datashi ga n zancen ƙaƙaba mata aure da'akayi, shine ya hanata cewa komi dn wani ɗan suma tayi na wucin gadi, jin sunan angon nata kuwa ya firgigitata matuka, abin kamar a mafarki

Kawia seta kwashe da dariya kamar wata hauka sabon kamu,

Tana dariyar tace " haba baba wanan wane irin wasa ne kuma, kace ka aura min man liman sa'anka, talaka, tsoho, me cin goro , mummuna tsohon banza, naja...................."

A karo na biyu ya zabga mata wani gigitaccen marin dayayi sanadiyyar natsar da ita, ta rarrafa ta riƙe ƙafar mahaifinata tana magiya, magiyar da bata taɓa yiwa wata halitta ba a doron ƙasa

" Baba, baba , dn zatin Allah kayi hakuri, ka aura min kowa banda ladan, inada wanda nakeso yake sona, zaizo zaizo baba ajirashi dn Allah"

Dubanta yayi kamar zuciyarsa zara karye sai kuma yayi yaƙi da hakan, idan ya barta dukkan su a halaka zata tsunduma su,

Ya ɗan sauke murya yace " uwata duk abinda zanmiki zanyishi ne saboda maslahar rayuwarki, maza nawane suka zo nan ɗin basu kuma dawowa ba? Maza nawane sukayi alƙawarin aurenki suka karya? Maza nawa ne suka soki ba domin Allah ba? Ki ciremin kwaya daya kwakkwara naji"

" Baba kabeeru Yana Sona zai aureni"

" Ina kabeerun yake? Yazoshi?

Ta ɗan yi dummm
Dn batada masaniyar halin ma da kabeerun yake ciki, tasan dai akwai matsala, in ba haka ba ba yadda za'ayi tajishi shiru ɗin har ta fara tunanin ma ko wani abu yaji a game da ita marar kyau, ko kuma wnaan Affan ɗinne ya zugashi dn bataga alamar ta karbu ba agurinsa,

ZABEN TUMUN DAREWhere stories live. Discover now