ZAƁEN TUMU 21

294 80 24
                                    

ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 21*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE.

Haka lokuta masu ɗimbin yawa suka shuɗe cikinsu kuwa abubuwa na ban mamaki, da al'ajabi, da kuma hukuncinnubangiji kuwa sun ƙadartu

Ayau kuma wani abin ya kuma kunnu kai ga resu ita dama jarabawar Allah haka nan take idan ya waiwaye ka sai kaga tamkar kai kaɗai ne a duniya wamda ake taɓawa, abin farin ciki na tafe garesu , kuma na baƙin ciki sai ya taho ya mamaye gurbin  farin cikin.

" Oga mun gama duk wani abu dayakamata, mun kunce birkin motar tasa"

Cewar hakuna

Daga ɗaya gefen shikuma ya amsa
" Well done hakuna, aikinka na kyau, wanan karon zaku samu babban rabo"

Wani ihu mai firgitarwa hakunan yayi wanda ya sanya AMBURSA katse wayar gabaki ɗaya, ya juya ya dubeta

" Semu fara shirye shiryen zaman makoki da kuma shagalin zama ceo's na babban kamfanin BK's, tunda mun kauda babban jarinsu"

Ta dubeshi kafin tace "bari de muga yadda zata kaya kada muyi saurin yanke hukunci ko?

Kamota yayi zai soma lalata da ita ta tureshi

Tace " AMBURSA bamuyi wanan alƙawarin ba. Dakai tukunna in wanan kakeso saide  ka sameshi ta hanyar aure kai kuwa kaga baka shirya ba, so muyi abinda zai fishshe mu"

Tamasa sallama ta fita zuciyarta cike da lissafi manya manya tana hango kanta kan karagar BK's COMPANIES nan bada daɗewa ba, wani mafarki datasha ayyanaashi, wani mafarki da ta daɗe da son taga ya zamo gaskiya, wani mafarki da batasan shine sanadin numfashinta ba..............

Bayan fitarta ne ya zauna nazari, tabbas wanan yarinyar tafishi shu'umanci, duk abinda yakeji dashi ta ninkashi, batada imani ko kaɗan! Bai taba ganin mace mai tsayayyan zuciya marar tsoro ba irin ta, kashe mutum da haɗa masa tuggu wani abu ne da ta gwanance akansa, bayan haka tana hulɗa da muggan ƙusoshin najeriya kama daga yan sanda ,sojoji da kuma manyan ƙasa yan siyasa,  shiyasa abubuwa da dama datake aikatasa su suke ɓoyuwa a doron ƙasa, daman hausawa sukace maganin biri karen maguzawa , yau ambursa yayi gammo da  wacce tafi ƙarfinsa... Ya soma tunano duk irin tijararsa ace wai wata tafishi?

WAYE AMBURSA??

Ambursa matashi ne me kimanin shekaru 30 dayake cikin ganiyarsa, ɗan asalin ƙauyen ambursa ne dayake jahar katsina wata nahiya mai tattare da mutane masu karamci ( zainab ɗahiru wowwo, m. Ali, anty rabi) wata nahiya mai ƙunshe da ababen mamaki, nahiyar data azurta nigeria da shuwagabanni har guda biyu.

Tun tasowar ambursa yaro ne mai falli, ga mugunta ko wasa akeyi dashi saiya ci zalin ɗiyan mutane wanan tun yana ɗan ƙanƙaninsa fa kenan, kasancewar sa ɗa tilo yasa yayi tashin sangarci! Sangarci irin wanda yake lalata rayuwar yaro har abada saiko idan taimakon Allah ya zo kansa.

Babu wanda bai sanshi ba saboda hatsabibancinsa, sane, sata, yankan aljihu duk nasa ne, har takai ta kawo ya koma fashi da makami, a sanadiyar haka yayi ajalin mahaifiyarsa wata rana ya shigo gida hanunsa dumu dumu da jini ta nemi yi masa kururuwa ya hamɓareta, daganan ko shurawa batayi ba, shikuma ya tsunduma duniya, bai tsaya kusa ba ya harba legas, inda yayi gwagwarmayar rayuwa ya ƙara gogewa kan harkokin fashi da sauran muggan ayyuka, har ya samu motar kansa, daga nan ya gudo abuja, toh amma a abuja harkar fashi bata ci saboda tsananin tsaro, harka ɗaya ce ya gano tanaci shine KAWALCI!

ZABEN TUMUN DARETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon