ZAƁEN TUMU 35

345 60 15
                                    

MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬

*ZABEN TUMU 35*

Via wattpad: @maryamtalba

*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*

TALBA CE

" Yanzu ke wanan yar fililikar yarinyar kika zubawa ido haka, take abinda taso da mijinki?

Cewar hinda wata ƙawar su jammy da suka kawo ziyara da ita gidan kb,

Ɗan taɓe baki jammy tayi kafin tace " kema dai kya faɗa, ni wallahi banga ma abin sakewa har ta zo ta shiga jikin mijinki, ji fa yada yake rawar ƙafa. Yanacin abincinta kuma ran girkinki, lallai kuwa za'ayita "

Hmmmmmmmmmmm

Wani numfashi ramlat tayi, batasan tayaya ma zata fara gaya musu ai yau tayi mugun ji da gani ba, inda taje tayi laɓe ta kashe kunne ta jinsambatun da kb yakeyi akan wanan yarinyar, mamaki ya sanya ta leƙa ta taga ta baya , inda taga abinda bata taɓa gani ba tunda uwarta ta haifeta, tunda take yawon iskanci babu wanda ya taɓa yi.mata haka nan, yanda kb ɗinta ya sururuce ya sakwarkwarce akan yarinyar nan, da wani abu data ga yana yi mata, seda abin ya bata mugun tsoro, da ƙyar ta kai kanta ɗakin kwananta ( karki sake, karki yarda, karki kuskura, kar ki kuskura kina yi ma kishiya laɓe dn zaki sha mugun mamaki, zaki yi kuka, zuciyarki zata buga, ki mutu ki bar mata mijin, laɓe ɗabia ce mummuna wallahi, kazantar da baki gani ba tsafta ce yar uwa, kawai aje ahaka  abinda kikaji ko kika gani ɗin har ki mutu hoton majiginsa ba zai daina tariyo miki ba, kuwwar amon zancen da kikaji bazai taɓa ficewa daga kunnenki ba, mu kiyaye)

Hinda ta ɗan taɓata kafin ta farga

" Inason na shiga culinary school hinda wacce zanshiga ?

Duk suka dubeta

Hinndan ta ce

" Akwai wata ta wani bature daya buɗe kwanan nan se muje ki shiga"

Ramlat tace " ɗaya kenan, se kuma inaso a dubamin wata kafirar me kayan mata, wacce idan nasha sai kb ya mutu a kaina"

Dariya ta kubce musu dn sun gano akwai matsala

Nan jammy ce ta ƙarɓi zancen da cewa

" Akwaisu gasunan birjik su jaruma su matilda, su queen ,se wanda kika zaɓa, kuɗi kawai zaki zubar amiki aiki"

" Kuɗi ba matsala bace jammy aikinnnake buƙatar gani"

Anan dai aka ƙaƙare duk yadda za'a ta basu atm, su ka tafi suna murna dn zasu kwashi rabonsu su ma, tunda bata iya hasala musu komi se izza, wai duk yadda suke da jammy bata iya bata komi sede ta figa cikin dabara ko idan wani abu makamancin hakan ya taso.

Da dare yau girkinta ne, dn haka khulsum tashiga kicin dn nema musu abinda zasu ci,ita da ɗanta wanda bata barinsa yaje ko nan da can dn gudun fitina dn ta lura ramlat bata son shi ko kaɗan.

Fried indomie ce tayi musu da soyayyar kaza,

Tana fita madam ta sauko ta shiga kicin itama, sunci abinci ita da affan suka gama abinda zasuyi suka shige ciki.

Can taji kamar ana buga mata ƙofa cikin kasala ta tashi ta buɗe , maigidan nne rai a ɓace,

Ko gaisuwarta bai amsa ba yace " ki samamin abinda zanci yanzu"

Ya barta gurinn tana tunani, da kamar bazata je ba ɗin ,sai ta tuno huɗubar luba datace

" Karki gajiya gurin yi masa hidima, mussamman ma wanda kika san bazata yi masa ba ki karɓa kiyi, hakan na ƙara darajar mace idanun miji"

ZABEN TUMUN DAREDove le storie prendono vita. Scoprilo ora