MACE MUTUM WRITTER's ASSOCIATION✍✍✍.. 🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
*ZABEN TUMU 44*
Via wattpad: @maryamtalba
*Maryam Talba (Mrs abdallah Adam)*
TALBA CE
Biki ne akayi nagarari, anan ta sake ganin idanun sani, wasu matan abokan babanta ne, da sauransu, gwamna da kansa ya sanya aka nemota dn yaji dadin abinda tayi masu ta fiddasu kunya, bai taɓa tunanin wai ashe har a garinsa yanada young enterprenues haka ba, irinsu ai jari ne ga gwamnati, dole ya taimaka a haɓaka musu kasuwancinsu, bayan kudi data samu , sun mata kyautar mota, sun mata kyautar girma, kamar yadda itama ta sayi kayayyakin gimbiya tayiwa amarya kyautarsu, sunji dadin hakan sosai har sun ce ta hadasu da ita. Bayan wanan ta samu contacts dayawa na jiga jigan gwamnati abin kamar a mafarki, nan ta kara fadada iliminta akan harkar abinci, ta ma mance ita doctor ce ta juye dr abinci,
Dama arzikinka ba lallai ya zamo acikin karatun boko bane, wani abin ɗan sanadi yake zamowa arzikinka sekaga Allah yana dafa ma, an wuce guri, itakam zatace wani jinkirin alheri ne, kalubalen rayuwa ya zamo mata alheri, gaba ta kaita gobarar titi a jos!
Tana kan computer ɗinta ne taji ana bugun ƙofa, a gajiye tamiƙe taje buɗe kofar, wa zata gani?
Luba ce, ta rungumeta tana ihun murna kamar zata kayar da ita, da kyar suka shiga ciki.
Murna harda kukansu,
Ta wadata luban da kayan cima iri iri, sana ta zauna hanunsu cikin na juna,
Khulsum tace " the barister, yaushe kika dawo?
Luba ta ɗan bata rai kafin tace " kar kiyi wanan tambayar, ki tambayeni sarkin naci yaya akayi na sameki"
.ta ɗan yi dariya
" Nasan ko a kabari nake zaki lalaboni idan kin dawo , shiyasa. Ban taba yanke tsammani ba akanki"
Luban ta bar komi ta fuskance ta alamun magana mai muhimmanci zasuyi
...Tace " na daɗe da dawowa, naje gidanki naga abin mamaki,naje gidan su mama ba kowa, abin ya dauremin kai, na dai dawo cikin damuwa, me zan gani wai an nada sabo ceo na bks, i was shocked, da ƙyar nasamu kaina, daga nan na soma bincike nagano makarkashiya akayiwa abin, wanda hankalina ya tashi, seda naje har tofa dn neman bayani, ashe haka ne ya faru?
Dan tagumi khulsum tayi tare da taɓe baki tace " wallahi fa luba, komi ya rikice amma alhamdulillah as u can see yanzu kam komi ya dai daita"
Luba tace " ai nayi bincike sosai akan abin, nan naga no RB itace ta shirya komi, da makarabanta"
Mamaki ya kama khulsum dn batasan zancen ba, kb ya ɓoye mata abubuwa da dama game da shari'ar tasu.
Affan ne ya ƙaraso yana gaida luban, sanan yace " anty luba ammyna bataso na fada mata abinda ya faru agidanmu na da, naji anty mai kyau tana cewa zatasa abbana yasa hannu a wani takarda sai komi ya zama nasu, kuma zata kasheshi, dasu ammy damu dukka"
Luba ne ta jawo yaron cikin laluma take masa tambayoyi da ƙwarewar lauyoyi, ta kuma samu amsoshin da hujjoji datake nema masu yawa
Juyowa tayi ta dubi khulsum tace " yoh ke ga maganin matsalarmu ma aketa sha wahala, i am taking over dis case"
Daga nan suka faɗa hirar rayuwa da duniyar da muke cikinta a yanzu.
*************************
************************Bayan wani lokaci...
Jirgin na kamfanin emiraye ne ya dira a da'irar filin jirgi na aminu kano, fasinjojin suka soma saukowa, idanunta saye da gilashi na kamfanin gucci, se abayarta ta baƙa siɗik ƙirar kamfanin lulu fujaj, bawata kwalliya bace afuskarta amma tana cike da annuri, da kuma wani nishaɗi, ta shaki kamshin iskar kasarta na jeriya kuma ta mahaifarta kanon dabo ko da me kazo anfika.
![](https://img.wattpad.com/cover/234330389-288-k196264.jpg)
YOU ARE READING
ZABEN TUMUN DARE
RomanceMafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga...